S.P Imam Ahmad Adam Kutubi" />

Hukuncin Sallar Idi Da Layya (II): Ranakun Yanka Dabbar Layya

Ana yanka dabbar layya a ranar goma ga Zulhajji, bayan hantsin farin ya yi; kuma bayan Liman ya yanka dabbarsa a Masallacin Idi. Wanda duk ya yanka gabanin Liman, babu layyarsa. Ranakun da aka bayar don yin layya uku ne. Watau ran 10, 11, da 12 ga Zulhajji. Ana yanka dabba a ko wace rana a cikin wadannan ranaku da rana kawai. Watau lokacin yanka shi ne daga fitowar rana har zuwa faduwarta. Bai halatta a yi yanka a cikn dare ba idan kuwa an yi, layya bata yi ba.
Yadda Za a Yi da Naman Layya
Abu uku ake yi da naman layya. Su ne mai layya ya ci, ya yi sadaka, ya yi kyauta. Yin sadaka ga matalauta shi ne wajibi. Kuma ba a iyakance yawan abin da mutum zai bayar sadaka ba. Amma ci da yin kyauta sai idan ya ga dama. A wajen yin kyauta ana iya ba har kafiri idan a wuri daya ku ke zaune, ko kuwa ya ziyarceku. Sai dai abin ki ne a aika masa da shi har gidansa.
Bai halatta a sayar da naman layya ba. Haka kuma bai halatta a sayar da fatarta ba bisa ga kauli mashhuri.
Hada Karfi
Bai halatta ba mutum biyu ko fiye da haka, su hada kudi su sayi dabba daya don su yi layya. Dalilin wannan hanin, domin an ce ita layya sunna ce ga mai iko kawai. Amma ya halatta ayi tarayya ga lada. Kamar mutum daya ya sayi dabba da kudinsa shi kadai. Sa’an nan ya yanka ta domin kansa da kuma wadansu mutane daban. Ko kuwa wani mutum guda ya ba wadansu mutane dabba daya don su yi layya da ita. Wannan kam ya halatta. Tarayya ce a wajen kudi ko mulki kadai aka hana.
Ba a ba mahauci ladan aikin fida daga cikin naman layya. Za ka biya shi ladan fidarsa dabam, sa’an nan k aba shi nama sadaka ko kyauta idan ka ga dama. Maganar da wadansu su kan ce, wai kafin ka fara yi wa kanka layya sai ka fara da yi wa iyayenka tukunna, wannan ba haka ba ne. Iyayenka dai idan matalauta ne, kai kuma mawadaci ne, ya zama har ciyad da su ya wajaba a kanka, to, sun shiga cikin tsarin sauran iyalanka, kamar ‘ya’yanka da matanka, wadanda an so ka yi wa ko wannensu layya ko ka gwamaya su.
SIFFAR YANKA
Akwai abubuwan da suka wajaba ko suka zama mustahabbi game da yanka dabba ko tsuntsu:
1. Idan za a yanka dabbobi da dama, an so kada a yanka daya a gaban idon wata.
2. An so a ba dabbar ruwa ta sha kafin a yanka ta.
3. An so a wasa wuka ta yi kaifi kwarai, don kada yanka ya dauki lokaci mai tsawo. An so kuma kada a wasa wukan nan a gaban idon dabbar.
4.Idan za a yankata, an so a ka da ita da sauki a akan barin jikinta na hagu. Idan rakumi ne kuwa, an so a soke shi daga tsaye, bayan an dabaibaye shi.
5.An so a fuskantad da dabban nan wajen alkibla.
6.Wajibi ne mai yanka ya yi niyyar yin yanka a cikin zuciyarsa. Watau niyyar halatta cin namanta. Idan mutum ya manta bai yi niyya ba, ya halatta a ci naman.
7.Sa’an nan bayan ya yi niyya sai ya ce: (Bismillahi wal lahu akbar), sa’an nan ya fara yanka. Fadar “Bismillahi” wajibi ne. Idan mutum ya manta fadarta, ya halatta aci naman. karawa da fadar “Allahu Akbar” mustahabi ne, watau abin so ne. Haka kuma idan dabbar da za a yanka ta saadaka ce. Kamar layya da suna da hadaya, an so a kara fadar: ( R a b b a n a t a k a b b a l m i n n a ) , . Wa t a u “Ubangijimmu ka karban mana”.
8.Sa’an nan mai yanke ya sa wukarsa a kan wuyan dabba r daga gaba , ya yanke makogaronta da wadansu jijiyoyi biyu na rabe da shi ta ko wane gefensa. Ana kiran jijiyoyin nan jannaye. Idan mutum bai yanke dayan wadannan abubuwa uku ba, yanka bai yi ba, ya baci. Haka kuma idan ya fara yanka, ba zai dauke hannunsa ba sai ya gama yanka sarai. Don haka idan mutum ya daga hunnunsa bayan ya yanke sashen makogaro ko jijiyar jannaye, sa’an nan kuma ya sake maido hannusa, ya karasa yankan, yanka ya baci ba za a ci ba. Amma an yafe laifin daga hannu dan lokaci kankane kwarai, kamar kubcewar wuka a tsakiyar yanka; ko wanna ma yana da hilafa don wadansu maluma sun ce ba za a ci ba.
9. Bayan an gama yanka, an ce kada a fara fida ko figa sai bayan dabbar ta daina shure-shuren daukar rai.
10. Wanda ya fara yanka daga keyar wuya, har ya kawo ga makogaro da jijiyoyin jannaye biyu ya yanke su, yanka ya baci ba za a ci ba. Don dabbar ta rigaya ta mutu ta hanya farawa da yanke lakar kashin wuyanta.
11. Wanda ya darzaza wuka ya yanke wuya baki daya har ya debe kai, za a ci naman ko da kuwa da gangan ne ya yi haka. Sai dai yanke kai da gangan mukruhi ne, watau abin ki.
12. Tumaki da awaki yankawa da wuka shine sunnarsu. Rakumi kuwa sokewa shi ne sunnarsa. Shanu kuwa da yankawa da sokewa duk daidai su ke a gare su. Yadda a ke a soke dabba shi ne a sa wuka ko mashi a huda makogaronta daga nan karshen wuya daga kasa, gun da ya hadu da dakoki. Dabbar da aka ce sunnarta yankawa ne, ko sokewa ne, idan an saba, ya halatta a ci naman game da hilafa.
13. Idan an yanke dabba mai ciki, yankan uwar ya wadatarwa yanka tayinta.
14. Dabbar ruwa ba ta bukatar yanka ko da ta kan fito tudu ta shakata.
15. Idan mutum yana farauta ne, to kafin ya harba kibiyarsa ko bindigarsa, ko kafin ya jefa mashinsa ko sanda, ko kafin ya shishita karensa, sai ya yi niyyar yanka, ya kuma ce: Bismillahi wal lahu akbar. Idan ya tarad da makaminsa ya kasha dabbar, sai a ci. Idan kuwa ya tarad da ita da sauran rai to, sai ya yanke ta.
16. Ko wane Musulmi, mace ko namiji, yaro ko babba, yana iya yanka dabba. Amma an shardanta yaro ko yarinya su zama sun yi wayo, sun fahimci ma’anar yanka. A wajen layya, mustahabbi ne kowa ya yanka dabbarsa da hannunsa don koyi da Annabi.
Bai halatta a ci dabba mushe ba wadda ba a samu yankata ba. Idan wani lahani ya sami dabba har ta yi kusa mutuwa dominsa, idan lahanin nan yana daga dayan abubuwan nan biyar:
Shakakkiya da igiya;
2. B u g a g g i y a d a s a n d a k o d u ts e k o makamantansu;
Wadda ta gangaro daga sama ta fado;
Tunkiyayyiya da kaho;
Wadda naman daji ya kama ya cije ta; to sai a duba a gani cewa, idan abin a bar dabban nan ne za ta rayu? Idan za ta iya rayuwa, to, ya halatta a yanka a ci. Idan kuwa koda an kyale ta bas hi yiwuwa ta rayu, to, ko an yanka ba za a cita ba. Ga alamomin da dabba ba za ta rayu ba idan sun same ta;
Katsewar lakar kashin wuya da na baya.
Yankewa jijiyar jannaye.
Hujewar hanji.
Cakudewar kayan ciki
Idan ba dayan wadannan aibobi hudu ya faru ba, to, sai a yankta a ci ; ko da kuwa ba a tsammanin ta rayu bisa ga kauli mafi karfi.
Ya halatta ga mutum matsattse, wanda ya ji tsoron halakar ransa don yunwa, ya ci mushe, kuma ya dauka guzuri har zuwa inda zai iya samun halattaccen abinci. Ana gabatad da cin mushe a kan cin alade.
Ya halatta a yi amfani da fatar mushe ga ko wane abu idan an jeme ta, amma ban da aikin ibada.
Fatar dabbobin da aka karhanta cinsu, kamar giwa da zaki da kura da yanyawa da kyamwa, idan an yankasu, tsarki gare ta, ana iya yin salla akan buzunta.
Ya halatta a yi amfani, har a cikin ibada, da ulu da gashi wanda aka yanko daga dabba mushe ko kuma mai rai.
An karhanta yin amfani da hakorin giwa. A wani kauli an ce babu karhanci.
An ciro wannan hukunce-hukunce ne daga littafin IBADA DA HUKUNCI ADDININ MUSULUNCI Na Alhaji Halliru Binji Alkalin Alkalai, na Jihar Arewa. Allah ya jikansa da Rahama da mu ma Amin.

Exit mobile version