Dakta Jamilu Yusuf Zarewa" />

Hukuncin Wanda Ya Tura Wani Gidan Boka Bai Sani Ba

Tambaya:

Assalamu Alaikum. Dr, nine wani ya faka a motor dinshi sai ya tambaye ne shin na san gidan wani mutumi sai na yi mishi kwatance sai daga baya na tuna gidan boka zai je, meye hukunci wanda ya yi hakan?

Allah ya sakawa malan da gidan aljannah fiddausi

Amsa:

Wa’alaikum assalam, Mutukar ba da saninsa ba ya nuna masa, Allah ba zai kama shi da laifin hakan ba, saboda Allah ya yiwa al’umar Annabi Muhammad (SAW) afuwa cikin abin da suka aikata da kuskure ko mantuwa kamar yadda ayar karshe a suratul Bakara ta tabbatar da hakan.

Allah ne mafi sani.

Zan Iya Yin Magana Lokacin ‘Pre-Khudba’?

Tambaya:

Asalamu Alaikum. Allah ya karawa Dr Fikira da Fasaha. Idan mutum yazo masallacin jumaa ya samu ana pre-khudba shi kuma yana so ya karanta S Kahfi, to zai iya karantawa ya jiyar da kansa sautin karatun koda na kusa dashi suna ji?

Amsa:

Wa’alaikum assalam, zahirin hadisin da ya zo akan hana yin magana lokacin da ake hudubar juma’a bai game har da pre khudba ba, don haka za ka iya yin magana, ko ka karanta alkur’ani a lokacin da ake yinta.

Pre- khudba ta banbanta da huduba, saboda akan yi ta kafin Muktarin Juma’a ya shiga,sannan a lokuta da yawa za ka ga ba liman ne yake yi ba, Hani da umarni a shari’a abu ne da yake hanun Allah da manzonsa, wannan ya sa za’a takaita a inda ya zo a nan.

Hadisi mai lamba ta: 841 a sahihil Bukhari ya tabbatar da cewa: sai liman ya fito zai hau minbari ya fara huduba sannan Mala’iku suke nannade takardun su,su zauna su saurari wa’azi da ambaton Allah, wannan sai ya nuna Pre-khudba ba ta daukar hukuncin hudubar juma’a wajan wajabta yin shiru da sauraro.

Allah ne mafi sani.

Fatawar Rabon Gado (59)

Tambaya:

Assalamu alaikum, Dr Allah ya karawa rayuwa albarka, tambayata itace mace ce ta rasu tabar mujinta da mahaifiyarta da shakikanta su uku abinda tabari an lissafa jimla 800,000 ya rabon zai kasance.

Amsa:

Wa alaikum assalam, Za’a bawa mijinta 400,000, sai a bawa mahafiyarta:  133,333.33333333, ragowar sai a bawa ‘yan’uwa shakikai su raba, duk namiji zai dau rabon mata biyu.                                                                                            Allah ne mafi sani.

Hukuncin Yin  Masallatan Juma’a Guda Biyu A Gari Daya

Tambaya:

Assalamu alaikum malam tambaya : yanzu za ka ga dan karamin gari, amma sai ka ga sama da masallacin juma’a  daya a cikinsa, shin hakan ya halatta ?

Amsa:

Wa’alaiku musalam, To malam babu wani hadisi ingantacce da ya hana hakan, saidai malamai sun yi sabani a cikin mas’alar zuwa maganganu guda uku: wacce ta fi inganci daga ciki, shi ne ya hallata ayi sama da masallacin juma’a guda daya a gari daya, mutukar akwai bukatar hakan, kamar ya zama masallacin farkon ba zai ishi mutane ba, ko kuma za’a samu wata fitina idan aka hadu wuri daya, ko ya zama akwai nisa tsakaninsu, ta yadda mutane za su sha wahala, wajan isowa zuwa gare shi.

Idan babu bukata abin da ya fi shi ne yin masallaci guda daya a gari daya, saboda daga cikin hikimomin shar’anta juma’a akwai samun hadinkan musulmai, da kuma nishadantar da juna, da samun lada mai yawa, hakan kuwa zai fi tabbatuwa idan suka yi sallah a masallaci guda daya, wannan ita ce maganar Ibnu Taimimiyya da Ibnu Bazz da kuma Ibnu Uthaimin, da wasu manyan maluma Allah ya yi musu rahama.

Allah ne mafi Sani.

Hukuncin Kari Ko Ragi A Cikin Al’ada

Tambaya:

Assalamu Alaikum, da fatan mallam yana cikin koshi lfy,. dan Allah malam ina da tambaya, ni ce nake jinin haila kwana 5 na saba yi to amma wannan karan kwana 9 yayi min, bayan na yi wanka da kwana 3 sai kuma wani brown din abu tare da jini kadan yake fito min wanda har yanzu bai dena ba shi ne nake tambaya akan hukukncin wannan rikitaccen lamarin nawa. Nagode

Amsa:

To malama ana iya samun ragi ko kari a jinin haila, don haka karin ba zai cutar ba, saboda shi ma haila ne, mutukar bai wuce iyaka ba, ta yadda zai zama jinin istihala, amma brown din da kike gani to mutukar bayan kin kammala haila ya zo, to ba ya cikinta, ba zai hana azumi ba da sallah, domin shi ne ake kira kudra, ita kuma kudra, idan ta zo bayan jinin haila, to ba ta cikinsa, kamar yadda hadisin Ummu Addiyya ya yi nuni, inda take cewa : “Mun kasance ba ma kirga kudra da sufra bayan tsarki a cikin haila. Bukhari 1\426.

Fatawar Rabon Gado (60)

Tambaya:

Assalamu akaikum. Malam mutum ne ya mutu ya bar mahaifiyarsa da ‘yar’uwarsa shakikiya da kuma ‘yan’ uwansa li’ummai ?

Amsa:

Wa alaikumus salam za’a raba abinda ya bari 12, abawa mahaifiyarsa kashi biyu, ‘yan’uwarsa kashi:6, ‘yan’uwansa li’ ummai a ba su kashi: 4

Allah ne mafi sani.

Ina So Na Yi Bakance, Ko Ya Halatta?

Tambaya:

Malam dan Allah ya hallata ayi bakance kuma dan Allah ya akeyi, ?

Amsa:

To ‘yar’uwa abin da ake nufi da bakance shi ne mutum ya yi alkawari cewa : idan Allah ya biya masa wata bukata zai yi wani abu na biyayya ga Allah.

Barin yin bakance shi ne ya fi, har wasu malaman ma sun tafi akan haramcinsa, saboda fadin Annabi s.a.w. ” Bakance ba ya zuwa da alkairi, saidai ana fitarwa daga marowaci ta hanyarsa” Muslim a hadisi mai lamba ta : 1639, ma’ana marowaci ne ba ya iya yin biyayya ga Allah sai ta hanyar bakance.

Duk lokacin da mutum ya yi bakance ya wajaba ya cika shi, saboda fadin Annabi s.a.w ” Duk wanda ya yi bakance zai yi biyayya ga Allah to ya yi masa biyayyar” kamar yadda Bukahari ya rawaito a hadisi mai  lamba ta  : 6322, Allah ya yabi masu yin bakance su cika,  kamar yadda aya ta :7 a suratul-insan take nuni zuwa hakan.

Saidai duk da haka abin da ya fi shi ne mutum ya yi niyyar aikin alkairi ba tare da ya danganta shi da samun wani abu da Allah zai bashi ba.

Idan mutum ya yi bakancen aikata wani zunubi bai halatta ya aikata ba, saboda fadin Annabi s.a.w. “Duk wanda ya yi bakance zai sabawa Allah to kar ya saba masa” kamar yadda Bukahari ya rawaito a hadisi mai  lamba ta  : 6322 .

Allah ne mafi sani.

Hukuncin Kallon Wasan Kwaikwayon Annabawa

Tambaya:

Assalamu Alaikum. Malam Don Allah Tambaya Na ke da shi Da Fatan Za’a  Fahimtar da ni. -wai Shin Kaset din da akeyi na Tarihin Annabawa Ya Halatta A Kalle shi ? Allah Ya Saka Da Alkhairi.

Amsa:

Wa’alaykumussalam, To dan’uwa  malamai da yawa sun haramta yin wasan kwaikwayon annabawa saboda dalilai kamar haka:

 1. Hakan zai iya bude kofar da wasu masu kallon za su yi isgilanci ko ba’a ga annabawan Allah, isgilanci ga annabawa kuma yana iya fitar da mutum daga musulunci, kamar yadda aya ta: 65 a suratu Atttauba ta yi nuni zuwa hakan.
 2. Wasu daga cikin masu shirya film din suna wuce gona-da-iri, kamar masu nuna annabi Isa a matsayin Allah, addinin musulunci kuma ya haramta duk abin da zai kai a riki wani annabi ko managarci a matsayin Allah.
 3. Irin wadannan wasannin na kwaikwayo, suna ragewa annabawa matsayi, saboda masu film din suna cakuduwa da matan da ba muharramansu ba, wanda hakan kuma ragewa annabawa kima ne.
 4. Kasancewar hakan ya sabawa hikimar Allah ta sanya shaidanu ba sa iya kama da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda ya zo a hadisi.
 5. Kasancewar hakan zai jawo aki girmama annabawa, a kuma yi musu karya, domin wasu masu yin wadannan fina-finan mutanen banza ne, ka ga sai a dinga kallon annabawan da siffar wadannan.

Allah ne mafi sani.

Fatwar Rabon Gado (61)

Tambaya:

Assalamu Alaiykum Allaah Yagafarta Malam, Ina Neman Fatawa akan Rabon Gado. Dan’Uwa Na Wanda Muke Uwa Daya Uba Daya YaraSu Yabar ; Mahaifin Mu, Mahaifiyar Mu, MatarSa Daya Da YaranSa Guda 9(Maza 5 Da Mata 4). Shin Iyayen Mu Sunada Gadon? Kuma Yaya Rabon Gadon Zai KasanCe??? Allah Yakara Maka Ilimi Mai Albarka.

Amsa:

Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ya bari gida:24, a bawa mahaifiyar kashi:4, mahaifiinku kashi: 4,

matarsa: kashi:3, ragowar kashi:13 sai a bawa yaransa, duk namiji zai dau rabon mata biyu.

Allah ne mafi sani

Nawa Ne Kason Zakkar Miliyan Daya?

Tambaya:

Assalamu Alaikum Tambaya daga jahar Taraba Suna so Dr. ya amsa musu a wannan zaure mai albarka.  Wata ce take da Miliyan daya tana so tafir da zakka nawa ne ya kamata ta fitar dashi?

Allah ya tsare mana Dr. ya yi mashi sakamako da gidan aljannah fiddaus.

Amsa:

Wa’alaikum assalam, Idan ta mallaki miliyan daya (1,00000), kuma su ka yi shekara daya a wajanta, to za ta fitar da dubu ashirin da biyar (25,000), wato daya cikin arba’in din abin da ya mallaka.

Allah ne mafi sani.

Yadda Ake Zakkar Gidan Haya Da Motar Haya

Tambaya:

Assalamu alaikum Malam Shin ko akwai zakka akan Gona, Fili ,Gidan haya da Motar Haya?

Amsa:

Waalaikumussalam, To dan’uwa duk gonar da aka rika don ayi amfani da ita, to babu zakka a cikinta, haka nan fili, amma idan kasuwanci ake yi da su, kamar a siya a sayar to za’a fitar musu da zakka, idan sun cika nisabi kuma shekara ta zagayo musu, ko kuma ya zama sun cika sharudan zakka idan ya hada su da abin da ke hannunsa.

Haka nan babu zakka a cikin gidan haya saidai idan aka tara kudin kuma shekara ta zagayo akan su, sun cika nisabi, to anan ne za’a fitar musu da zakka, ko kuma ya zama sun cika sharudan zakka idan ya hada su da abin da ke hannunsa.

Allah ne mafi sani.

Fatawar Rabon Gado (56)

Tambaya:

Assalamu alaykum. Malam inada tambaya? Allah gafarta malam, shin idan mace ta rasu batada miji da iyaye sai ” ya’ya uku mata batada namiji, shin ” yan uwanta da suke uba daya sunada gadonta?

Amsa:

Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ta bari kashi uku, sai a bawa ‘ya’yanta kashi biyu, ragowar kashi dayan sai a bawa ‘yan’uwanta da suka hada uba daya in har babu shakikai.

Allah ne mafi sani.

Mene Ne Hukuncin Matar Da Ta Yi Aure A Cikin Aure?

Amsa:

Assalamu Alaikum, Game da tambayarka da ka yi akan matar da ta yi sabon-aure, ba tare da mijinta ya sake ta ba. Bayan bincike da tambayar malamai, na isa izuwa ga hukunci kamar haka:

 1. Abin da ta yi mummuna ne a shari’ar musulunci saboda ta yi aure cikin aure.
 2. Zaman da su ka yi da mijinta na biyu, a matsayin mazinaciya take, saboda haka duk kwanciyar da suka yi da wannan mijin na ta zina ne.
 3. Yaran da su ka Haifa da mijnta na biyu, ‘ya’yansa ne, tun da bai san abin da ya faru ba a baya.
 4. Har yanzu igiyar aurenta ba ta warware ba tsakaninta da mijinta na farko, saboda haka har yanzu ita matarsa ce saidai idan ya sake ta.
 5. Mijinta na farko, zai iya dawowa da ita, ba tare da sake daura aure ba, saidai dole sai bayan ta tuba, domin ita a matsayin mazinaciyya take, kuma Allah ya hana auren mazinaciya.
 6. Ya wajaba a gare ta ta yawaita istigfari saboda girman zunubun da ta aikata.
 7. Zai yi kyau su je wajan Alkali wanda ya san shari’a, domin ya yi musu hukunci.

Allah Ya Kiyaye Mu Daga Irin Wannan Aika-Aikar.

Ina Son Karin Bayani A Kan Sallar Walha?

Tambaya:

Asalamu Alaikum malam ya aiki malam, don Allah ya ka’idar sallar walaha take? Allah ya saka da Alheri.

Amsa:

Wa’alaykumussalam, To ‘yar’uwa sallar walaha ba ta da wani adadin raka’o’i na musamman, Za ki iya yın raka’a biyu ko hudu ko shida da sallama uku, mafi yawan abin da aka rawaito daga Annabi s.a.w. a sallar walaha shi ne raka’a takwas, kamar yadda ya yi ranar bude Makka, Bukhari ya ambaci kissar a hadisi mai lamba ta: 5806. Lokacin sallar walaha yana farawa daga sanda rana ta fara zafi, kamar yadda hadisin Muslim mai lamba ta: 748 ya tabbatar da hakan, har zuwa dab da karkatar rana daga tsakiyar sama.

Allah ne mafi sani.

Ta Yi Aure Da Cikin-Shege, Yaya Hukuncin Auren?

Tambaya:

Assalamu alaikum. Malam Wata tayi cikin shege da wani mutum,sai ta nemi wani daban ya rufa mata asiri ya aureta.Yanzu sun yi Auren,yaya hukuncin Auren a Shari’a yake?

 Amsa:

Wa’alaykum assalamu Zina sabon Allah ne da kuma yada fasadi a bayan kasa.

Aure kuwa sunnar Manzon Allah ne, da samar da zuriya mai albarka. Kuma an kwadaitar da mu yin sa. Amma Mazhabar Malikiyya suna ganin matar da aka yi zinar da ita sai ta yi jini wanda ake kira Istibra’i, kafin a daura mata aure domin a raba maniyyin zinar da na aure.

Kuma idan har an daura aure ba ta yi wannan jinin ba, to, za’a raba wannan auren ko da sun haifi ‘ya’ya, domin suna ganin an daura auren ne a cikin idda, kuma Allah Ya hana daura aure a cikin idda.

Saboda haka, a wurinsu, wannan auren batacce ne kuma rusasshe.

Amma Mazhabar Abu Hanifa da Imam Shafi’i suna ganin macen da ta yi zina, an so ta yi istibra’i kafin ta yi aure, amma idan har an daura auren ba ta yi istibra’i ba, auren yana nan daram, ba za a raba su ba. Kuma suka kara da cewa ko da tana da cikin zinar ne aka daura mata aure, to, auren yana nan. Sai dai Imam Abu Hanifa ya ce: mijin da ta aura, ba zai sadu da ita ba, har sai bayan ta haihu, ko da kuwa cikin zinar nasa ne ko na waninsa.

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa” Abu- dawud: 1847.

Don neman karin bayani duba: Al-Mudawwannah Al-Kubrah 2\173 da Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 8/79.

A fahimtata, fatawar Malikiyya ta fi inganci kafin ayi auren, saboda fita daga sabanin malamai abin só ne, sannan kuma za’a kaucewa fadawa hadari, amma idan an riga an yi auren to fatawar Hanafiyya abar lura ce, saboda akwai bambanci tsakanin zina da aure, saidai ya wajaba şu nisanci saduwa, kafin ta haihu Saboda hadisin da ya gabata.

Allah ne mafi sani.

Fatawar Rabon Gado (57)

Tambaya:

Assalamu alaikum Malam ina da tambaya, idan mace ta mutu ta bar ‘ya mace guda daya, da dan”uwa shakiki daya, da jikokinta na da namiji 24 maza 14 mata, dan Allah mlm yaya rabon gadon zai kasance?, Allah ya saka da”alkhairi.

Amsa:

Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ta bari gida biyu, a bawa ‘Yarta kashi daya, ragowar sai a bawa jikokinta, duk namiji ya dau Rabon mata biyu.

Allah ne mafi sani.

Hukuncin Ba Da Gidan Haya Ga Masu Bautar Coci!

Tambaya:

Assalamu Alaikum. Malam dan Allah miye matsayin Musulmi da ya gina hotel kuma yana baiwa kafirai haya suyi choci?

Amsa:

Wa alaikum assalam, Bai halatta ba, saboda Allah madaukakin sarki ya hana taimakawa mai aikin sabo.                                                                               Aya ta biyu a cikin suratul Ma’ida tana cewa: “Kuma ku dinga tamakekeniya wajan aikata alkairi, Amma kada ku yi tamakekeniya wajan aikata sabo”.

Ibadar Coci shirka ce kamar yadda ayoyi da yawa a suratul Ma’ida suka siffanta Wanda yake bautawa annabi Isa da kafiri.

Allah Ne mafi Sani.

Fatawar Rabon Gado (58)

Tambaya:

Assalamu Alaikum. malam Allah saka da gidan Aljannah. malam inatambaya mahaifiyata ce Allah ya amshi rayuwarta ta bar mahaifiyarta da maigidanta da ni namiji 1 sai mata su 6. ya gadon zai kasanche. Allah yakara wa Malam lafiya amin

Amsa:

Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ta bari gida:12, Sai a bawa mijinta kashi:3, mahaifiyarta kashi: 2, ragowar sai a bawa ‘ya’yanta su raba duk namiji ya dau rabon Mata biyu.

Aĺlah ne mafi sani.

Page 27

Hukuncin Wanda Ya Tura Wani Gidan Boka Bai Sani Ba

Tambaya:

Assalamu Alaikum. Dr, nine wani ya faka a motor dinshi sai ya tambaye ne shin na san gidan wani mutumi sai na yi mishi kwatance sai daga baya na tuna gidan boka zai je, meye hukunci wanda ya yi hakan?

Allah ya sakawa malan da gidan aljannah fiddausi

Amsa:

Wa’alaikum assalam, Mutukar ba da saninsa ba ya nuna masa, Allah ba zai kama shi da laifin hakan ba, saboda Allah ya yiwa al’umar Annabi Muhammad (SAW) afuwa cikin abin da suka aikata da kuskure ko mantuwa kamar yadda ayar karshe a suratul Bakara ta tabbatar da hakan.

Allah ne mafi sani.

Zan Iya Yin Magana Lokacin ‘Pre-Khudba’?

Tambaya:

Asalamu Alaikum. Allah ya karawa Dr Fikira da Fasaha. Idan mutum yazo masallacin jumaa ya samu ana pre-khudba shi kuma yana so ya karanta S Kahfi, to zai iya karantawa ya jiyar da kansa sautin karatun koda na kusa dashi suna ji?

Amsa:

Wa’alaikum assalam, zahirin hadisin da ya zo akan hana yin magana lokacin da ake hudubar juma’a bai game har da pre khudba ba, don haka za ka iya yin magana, ko ka karanta alkur’ani a lokacin da ake yinta.

Pre- khudba ta banbanta da huduba, saboda akan yi ta kafin Muktarin Juma’a ya shiga,sannan a lokuta da yawa za ka ga ba liman ne yake yi ba, Hani da umarni a shari’a abu ne da yake hanun Allah da manzonsa, wannan ya sa za’a takaita a inda ya zo a nan.

Hadisi mai lamba ta: 841 a sahihil Bukhari ya tabbatar da cewa: sai liman ya fito zai hau minbari ya fara huduba sannan Mala’iku suke nannade takardun su,su zauna su saurari wa’azi da ambaton Allah, wannan sai ya nuna Pre-khudba ba ta daukar hukuncin hudubar juma’a wajan wajabta yin shiru da sauraro.

Allah ne mafi sani.

Fatawar Rabon Gado (59)

Tambaya:

Assalamu alaikum, Dr Allah ya karawa rayuwa albarka, tambayata itace mace ce ta rasu tabar mujinta da mahaifiyarta da shakikanta su uku abinda tabari an lissafa jimla 800,000 ya rabon zai kasance.

Amsa:

Wa alaikum assalam, Za’a bawa mijinta 400,000, sai a bawa mahafiyarta:  133,333.33333333, ragowar sai a bawa ‘yan’uwa shakikai su raba, duk namiji zai dau rabon mata biyu.                                                                                            Allah ne mafi sani.

Hukuncin Yin  Masallatan Juma’a Guda Biyu A Gari Daya

Tambaya:

Assalamu alaikum malam tambaya : yanzu za ka ga dan karamin gari, amma sai ka ga sama da masallacin juma’a  daya a cikinsa, shin hakan ya halatta ?

Amsa:

Wa’alaiku musalam, To malam babu wani hadisi ingantacce da ya hana hakan, saidai malamai sun yi sabani a cikin mas’alar zuwa maganganu guda uku: wacce ta fi inganci daga ciki, shi ne ya hallata ayi sama da masallacin juma’a guda daya a gari daya, mutukar akwai bukatar hakan, kamar ya zama masallacin farkon ba zai ishi mutane ba, ko kuma za’a samu wata fitina idan aka hadu wuri daya, ko ya zama akwai nisa tsakaninsu, ta yadda mutane za su sha wahala, wajan isowa zuwa gare shi.

Idan babu bukata abin da ya fi shi ne yin masallaci guda daya a gari daya, saboda daga cikin hikimomin shar’anta juma’a akwai samun hadinkan musulmai, da kuma nishadantar da juna, da samun lada mai yawa, hakan kuwa zai fi tabbatuwa idan suka yi sallah a masallaci guda daya, wannan ita ce maganar Ibnu Taimimiyya da Ibnu Bazz da kuma Ibnu Uthaimin, da wasu manyan maluma Allah ya yi musu rahama.

Allah ne mafi Sani.

Hukuncin Kari Ko Ragi A Cikin Al’ada

Tambaya:

Assalamu Alaikum, da fatan mallam yana cikin koshi lfy,. dan Allah malam ina da tambaya, ni ce nake jinin haila kwana 5 na saba yi to amma wannan karan kwana 9 yayi min, bayan na yi wanka da kwana 3 sai kuma wani brown din abu tare da jini kadan yake fito min wanda har yanzu bai dena ba shi ne nake tambaya akan hukukncin wannan rikitaccen lamarin nawa. Nagode

Amsa:

To malama ana iya samun ragi ko kari a jinin haila, don haka karin ba zai cutar ba, saboda shi ma haila ne, mutukar bai wuce iyaka ba, ta yadda zai zama jinin istihala, amma brown din da kike gani to mutukar bayan kin kammala haila ya zo, to ba ya cikinta, ba zai hana azumi ba da sallah, domin shi ne ake kira kudra, ita kuma kudra, idan ta zo bayan jinin haila, to ba ta cikinsa, kamar yadda hadisin Ummu Addiyya ya yi nuni, inda take cewa : “Mun kasance ba ma kirga kudra da sufra bayan tsarki a cikin haila. Bukhari 1\426.

Fatawar Rabon Gado (60)

Tambaya:

Assalamu akaikum. Malam mutum ne ya mutu ya bar mahaifiyarsa da ‘yar’uwarsa shakikiya da kuma ‘yan’ uwansa li’ummai ?

Amsa:

Wa alaikumus salam za’a raba abinda ya bari 12, abawa mahaifiyarsa kashi biyu, ‘yan’uwarsa kashi:6, ‘yan’uwansa li’ ummai a ba su kashi: 4

Allah ne mafi sani.

Ina So Na Yi Bakance, Ko Ya Halatta?

Tambaya:

Malam dan Allah ya hallata ayi bakance kuma dan Allah ya akeyi, ?

Amsa:

To ‘yar’uwa abin da ake nufi da bakance shi ne mutum ya yi alkawari cewa : idan Allah ya biya masa wata bukata zai yi wani abu na biyayya ga Allah.

Barin yin bakance shi ne ya fi, har wasu malaman ma sun tafi akan haramcinsa, saboda fadin Annabi s.a.w. ” Bakance ba ya zuwa da alkairi, saidai ana fitarwa daga marowaci ta hanyarsa” Muslim a hadisi mai lamba ta : 1639, ma’ana marowaci ne ba ya iya yin biyayya ga Allah sai ta hanyar bakance.

Duk lokacin da mutum ya yi bakance ya wajaba ya cika shi, saboda fadin Annabi s.a.w ” Duk wanda ya yi bakance zai yi biyayya ga Allah to ya yi masa biyayyar” kamar yadda Bukahari ya rawaito a hadisi mai  lamba ta  : 6322, Allah ya yabi masu yin bakance su cika,  kamar yadda aya ta :7 a suratul-insan take nuni zuwa hakan.

Saidai duk da haka abin da ya fi shi ne mutum ya yi niyyar aikin alkairi ba tare da ya danganta shi da samun wani abu da Allah zai bashi ba.

Idan mutum ya yi bakancen aikata wani zunubi bai halatta ya aikata ba, saboda fadin Annabi s.a.w. “Duk wanda ya yi bakance zai sabawa Allah to kar ya saba masa” kamar yadda Bukahari ya rawaito a hadisi mai  lamba ta  : 6322 .

Allah ne mafi sani.

Hukuncin Kallon Wasan Kwaikwayon Annabawa

Tambaya:

Assalamu Alaikum. Malam Don Allah Tambaya Na ke da shi Da Fatan Za’a  Fahimtar da ni. -wai Shin Kaset din da akeyi na Tarihin Annabawa Ya Halatta A Kalle shi ? Allah Ya Saka Da Alkhairi.

Amsa:

Wa’alaykumussalam, To dan’uwa  malamai da yawa sun haramta yin wasan kwaikwayon annabawa saboda dalilai kamar haka:

 1. Hakan zai iya bude kofar da wasu masu kallon za su yi isgilanci ko ba’a ga annabawan Allah, isgilanci ga annabawa kuma yana iya fitar da mutum daga musulunci, kamar yadda aya ta: 65 a suratu Atttauba ta yi nuni zuwa hakan.
 2. Wasu daga cikin masu shirya film din suna wuce gona-da-iri, kamar masu nuna annabi Isa a matsayin Allah, addinin musulunci kuma ya haramta duk abin da zai kai a riki wani annabi ko managarci a matsayin Allah.
 3. Irin wadannan wasannin na kwaikwayo, suna ragewa annabawa matsayi, saboda masu film din suna cakuduwa da matan da ba muharramansu ba, wanda hakan kuma ragewa annabawa kima ne.
 4. Kasancewar hakan ya sabawa hikimar Allah ta sanya shaidanu ba sa iya kama da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda ya zo a hadisi.
 5. Kasancewar hakan zai jawo aki girmama annabawa, a kuma yi musu karya, domin wasu masu yin wadannan fina-finan mutanen banza ne, ka ga sai a dinga kallon annabawan da siffar wadannan.

Allah ne mafi sani.

Fatwar Rabon Gado (61)

Tambaya:

Assalamu Alaiykum Allaah Yagafarta Malam, Ina Neman Fatawa akan Rabon Gado. Dan’Uwa Na Wanda Muke Uwa Daya Uba Daya YaraSu Yabar ; Mahaifin Mu, Mahaifiyar Mu, MatarSa Daya Da YaranSa Guda 9(Maza 5 Da Mata 4). Shin Iyayen Mu Sunada Gadon? Kuma Yaya Rabon Gadon Zai KasanCe??? Allah Yakara Maka Ilimi Mai Albarka.

Amsa:

Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ya bari gida:24, a bawa mahaifiyar kashi:4, mahaifiinku kashi: 4,

matarsa: kashi:3, ragowar kashi:13 sai a bawa yaransa, duk namiji zai dau rabon mata biyu.

Allah ne mafi sani

Exit mobile version