Hunkuncin Sauke Wa Mamaci Alkur'ani Bayan Ya Mutu
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hunkuncin Sauke Wa Mamaci Alkur’ani Bayan Ya Mutu

byDakta Jamil Zarewa
3 years ago
Mamaci

Assalamu alaikum. Wai Malam Meye Hukuncin Sauke wa Mamaci Al-kur’ani?

Wa’alaikum assalam. To malamai sun yi sabani akan wannan mas’ala zuwa maganganu guda uku:

  • Me Ya Sa Erik Ten Hag Yake Goyon Bayan Harry Maguire? 
  • Wakilin Sin Ya Yi Cikakken Bayani Kan Sakamakon Da Jihar Xinjiang Ta Samu Wajen Kare Hakkin Bil Adam

1. Bai halatta ba, saboda ba’a samu wani nassi da yake nuni zuwa haka ba, kuma ita ibada ba’a yinta sai da nassi na musamman, sannan kuma mutum ba shi da wani abu sai aikinsa, kamar yadda aya ta 39 da take cikin suratu Najm, take nuni zuwa haka, tun da ba’a samu ba, yin hakan zai zama bidi’a, wannan ita ce maganar farko ta Shafi’i.

2. Ya halatta ayi, saboda hadisan da suke nuna cewa mamacin yana iya amfana da abin da mai rai zai masa, kamar hadisan da suka yi umarni da yi masa sallah da nema masa gafara bayan ya mutu, da yi masa sadaka, wannan shi ne maganar mafi yawan malamai, har wasu marubuta ma sun hakaito ijma’i akan haka, saboda mutane sun jima suna yi kuma malamai ba su yi musu inkari ba.

3. Akwai wadanda suka tafi akan cewa: idan dansa na cikinsa ya yi masa, to ladan zai same shi, amma wanda ba dansa ba, ba zai yi masa ba, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi “Dan mutum yana daga cikin aikinsa” Abudawud ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi a sahihu sunani-abi-dawud hadisi mai lamba ta: 2528.

Saidai wasu malaman, suna rinjayar da magana ta uku, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: “Idan dan’adam ya rasu ayyukansa sukan yanke sai dayan abubuwa guda uku: sadaka mai gudana, ko ilimin da ake amfana da shi, ko da nagari da yake masa addu’a” kamar yadda Tirmizi ya rawaito shi kuma ya inganta shi a hadisi mai lamba ta: 1376.

Wadancan hadisan kuwa da masu Magana ta biyu suka kafa hujja da su, to za’a yi amfani da su ne a iya inda suka zo, amma ba za’a yi kiyasin karatun kur’ani akan su ba.

Don neman Karin bayani: duba majmu’ul fataawa: 24\366 da Nailul Audaar 4\112 da Ahakamul jana’iz shafi na: 171.

Allah shine mafi sani.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi
Dausayin Musulunci

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

October 3, 2025
Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)
Dausayin Musulunci

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

September 26, 2025
Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Muna Murna Da Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (1)

September 5, 2025
Next Post
NUJ Kebbi Ta Yi Alhini Rasuwar Tsohon dan Jarida Ibrahim Argungu

NUJ Kebbi Ta Yi Alhini Rasuwar Tsohon dan Jarida Ibrahim Argungu

LABARAI MASU NASABA

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version