Ibo Sun Fara Gangamin Neman Tsayar Da Dan Takarar Shugaban Kasa A 2023

Rahotanni na cewa, al’ummomin Kudu maso Gabas sun fara harin mulkin Nijeriya a shekara ta 2023, inda yanzu haka su ke ta shirya tarurruka domin su kai labari.

Manyan ‘yan boko da ‘yan siyasa da Attajirai da ‘yan kasuwa da Sarakunan gargajiya na yankin, su na halartar tarurrukan da ake yi a gidan wani tsohon gwamna kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Yunkurin da ake yi dai shi ne, a yi watsi da duk wani bambancin siyasa a ba Inyamurai tikitin takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2023, kamar yadda jam’iyyun PDP da AD su ka tsaida Yarabawa a shekara ta 1999.

Wani ‘dan majalisar yankin Benjamin Kalu ya bayyana cewa, da gaske su na harin kujerar shugaban kasa a shekara ta 2023, ya na mai cewa, ya kamata a ba kowace kabila damar mulki.

Ya ce sun fi karfi idan su ka hada kai, matukar su na so su karbi kujerar farko a Nijeriya, kuma za a fi samun zaman lafiya idan kowane yanki ya yi mulki Nijeriya, a cewar shi.

Exit mobile version