Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Inyamurai mazauna Jihar Bauchi sun bayyana cewar a rayuwarsu da suke yi da mutanen Bauchi babu abin da za su ce sai godiya da hamdala, domin gwamnati da al’umman jihar sun rikesu da gaskiya da kuma zaman lafiya ba tare da nuna musu wariya ba. ‘yan kabilar Ibo mazauna Bauchi wadanda suka bayyana hakan a makon jiya a sa’ilin da suka kawo zo ofishin ‘yan jarida.
Shugaban ‘yan Kabilar Ibo mazauna Bauchi Reverend Dominic Nkwocha ya shaida hakan inda ya ci gaba da cewa “Mu Ibo mazauna Bauchi aka zamanmu a Bauchi babu abun da zamu ce sai mun gode, muna ji dadi zamanmu a wannan jihar. gwamnan jihar nan sai mu ce masa mun gode a bisa tabbatarwar da yake yi ya ga an samu zaman lafiya. Haka kuma muna jinjina wa mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu muna jin dadin yanda yake bamu goyon baya a kowanne lokaci da kuma bamu kulawa ta musamman”. In ji shugaban na Inyamurai
Shugaban na Ibo wanda ya samu rakiyar Sakataren Kungiyar da wasu jiga-jigai sun ce Nijeriya kasa ce ta kowa ba wai na wani jinsi ba “Mun yarda Nijeriya kasarmu ce wacce Allah ya ajiye mu domin mu yi rayuwa baki daya. Kuma shi Allah da ya hada mu waje guda bai yi kuskure ba. don haka mu mun amincen da dokokin kasar Nijeriya kuma bamu da ja a kai, duk wasu matakan zaman lafiya muna na’am da su”. In ji su
Reverend Dominic Nkwocha ya ce suna bayan matakin da gwamnonin arewa suke dauka dari bisa dari “Gwamnonin arewa maso gabas muna goyon bayansu dadi bisa dari a kan matakin da suke dauka kan zaman lafiya”. In ji shi
Ya ce sun barranta da masu fafatukar kafa Biyafara, ya kuma yi kira da babbar murya a duk inda Inyamuri yake ya kasance mai da’a da biyayya wa dokokin kasa, “Muna fada wa duk wani Ibo a duk inda ya ke da zama, ya yi abin da ya kamata, kada ya aikata wani kuskure. Wasu mutane da suke IPOB mu bamu sansu ba; kuma bamu goyon bayansu kan abin da suke aikatawa. Don haka muka shaidawa duniya mun barranta da su”. A cewarsa
Sai ya nuna kansu a matsayin masu bin umurni da kuma dokokin zaman lafiya na Jihar Bauchi da kuma na kasa baki daya.