Alhussain Suleiman" />

ICAN Ta Gudanar Da Taronta Karo Na Sha Biyar A Kano

ICAN

Kungiyar kwararrun akantoci ta kasa ta gudanar a taron ta karo na shabiyar na kwanaki Uku, a jihar Kano, inda ya samu halartar dinbin yayan kungiyar maza da mata da suka fito daga jihohin kasar nan .

Da yake zantawa da manema labarai shugaban kungiyar ta Institute of Chatered Accauntant  of Nigeria  ICAN na jihohin Kano da Jigawa, Dakta Abubakar Umar Farouk PHD, FCA, ya nuna farin cikin shi da aka gudanar da taron karo na shabiyar a jihar Kano , ya kara da cewa duk wadanda ake zaton su halarci taron sun halarta an kuma gabatar da makaloli masu muhimmanci da za su ciyar da kungiyar gaba .

Alhaji Abubakar Umar Farouk fca, y ace dama makasudin taron shi ne ahadu a tattauna tare da wasa kwakwalwa akan matsalolin tsaron dake addabar kasar nan musamman arewacin ta , tare da yadda za’a farfado da tattalin arzikin yankin.

Kungiyar su inji sugaban na ICAN na jihohin biyu, y ace kungiyar su tana da matukar karfin gaske domin ita take wakiltar kasar nan da nahiyar Afirka dama Duniya baki daya matukar ya shafi kididdiga , ilimin zam akanta a hannun kungiyar take , sune suke karantar da duk wani mai son kwarewa , sannan kuma doka ta amince masu kungiyar su akullun tana bakin kokarin ta wajen wayar da kan al’umma musamman yankasuwa ta yadda za su samu cigaban kasuwancin su da zai rika tafiya dai dai da zamani idan Allah ya yarda.

Malam Abubakar Umar Farouk, ya ce a karshen taron aan son a fitar da hanyoyi da za su habaka tattalin arziki da kuma yadda al’umma za su dogara da akan su mai makon su jira sai gwamnati tab a su aiki.Alhaji Abubakar fca , ya kuma tabbatar wad a manema labaran cewa yanzu haka kungiyar ta su na ICAN tan a da fiyali ajihohin Kano da Jigawa wanda gwamnatocin suka mallaka masu kyauta wanda da yardar Allah a farkon shekara mai kamawa za’a kaddamar da fara ginin su da izinin Allah.

Daga nan sai shugaban kungiyar na ICAN na jihohin Kano da Jigawa, ya yi amfani da wannan dama da kira ga masu hali da su taimaka su shigo domin biyawa yara kudaden jarabawa na zama akanta , su nasu amatsayin sun a kungiya shi ne su ba da ilimi kyauta kamar yadda suka saba yi , babban burin ga al’umma shi ne su wayar masu da kai akan  za su tafiyar da harkokin kasuwancin su azamanan ce da samar da aikin yi ga al’aumma musamman matasa maza da mata

 

Exit mobile version