Idan Ana Maganar Kamfanonin Sin, Ita Kanta Burtaniya Ma Za Ta Ji Radadin
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Idan Ana Maganar Kamfanonin Sin, Ita Kanta Burtaniya Ma Za Ta Ji Radadin

byCGTN Hausa
2 years ago
Sin

A kwanakin nan ne, kafofin watsa labaru na Burtaniya suka ba da labarin cewa, kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Burtaniya, ya cire abubuwan da kamfanonin kasar Sin suka samar, wai saboda batun “tsaro”. Wasu manazarta sun yi nuni da cewa, idan har wannan lamari ya tabbata gaskiya, abin da ake nufi shi ne, bangaren Birtaniyya na cin mutuncin kamfanonin Sin, suna ta yada abin da ake kira wai “barazanar kasar Sin”, bayan Amurka, ta kara neman dakile kamfanonin fasahohi na kasar Sin, wanda ke nuna kawance na musamman tsakanin Burtaniya da Amurka. Ban da wannan kuma, kasar Burtaniya za ta gudanar da babban zabe a shekara mai zuwa, kuma jam’iyya mai mulki na fatan samun karin kuri’u ta hanyar kara daukar matakai masu tsauri kan kasar Sin.

Sai dai kuma, Burtaniya ce za ta dandana kudarta: canjin da kamfanin na Burtaniya ke fatan gani zai dauki lokaci mai tsawo kuma yana da tsada, kuma mutanen Burtaniya na iya shan wahala daga farashin makamashi mai yawa na dogon lokaci. Koma bayan babbar tashar samar da wutar lantarki na baya-bayan nan, jan hankali ne kan canjin makamashi, kuma yana da wahala a cimma burin rage fitar da hayaki. Siyasantar da batutuwan kasuwanci da fasaha ta kowane hali, zai iya dakushe kwarin gwiwar manyan kamfanoni na kasa da kasa wajen saka hannun jari a Burtaniya.

Ya kamata mutane masu hankali a Burtaniya su fahimci cewa, kasar Sin abokiyar hulda ce kuma wata dama ce ta samun ci gaba. Hanyar da ta dace da kasashen Sin da Birtaniya su bi wajen yin sulhu, ita ce ta hanyar yin hadin gwiwa a aikace da kuma samun moriyar juna, ta yadda za a sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kawo moriya ga duniya baki daya. (Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7
Daga Birnin Sin

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Next Post
Sin Ta Tsara Kyawawan Sharuddan Janyo Jarin Waje

Sin Ta Tsara Kyawawan Sharuddan Janyo Jarin Waje

LABARAI MASU NASABA

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version