A matakin da ake kai yanzu cutar Coronabirus ta riga ta zama ruwan dare a kasar nan, domin manyan jihohin Kasar nan sune gaba gaba wajen masu ɗauke da wannan cutar, wanda hakan ke nufin baki daga wasu sassan zasu iya ɗaukan wannan cutar su shafawa wanda bai da ita. Wannan kusan shine dalilin daya sanya aka kulle iyakokin wasu jihohin domin hana masu ɗauke da cutar shiga wata jihar, ko kuma wanda yake zaune a jihar da masu ɗauke da cutar suka kai wani adadi. To amma abin damuwa anan shine yadda wasu har yanzu suke maida hannun agogo baya, har yanzu mutane na shigowa daga wata jihar zuwa wata jihar, duk da cewa an ayyana hakan a matsayin cin zarafin dokar da jihohi da dama suka sanya.
Mu bar ta maganar hana shigowa jihohi ma, yadda aka hana zirga-zirga a wasu jihohin, kamar Jihar Naija, Filato, Kaduna da Jihar Kano har yanzu wasu mutane basu ɗauki hakan a matsayin wani matakin dakile wannan cutar ba. Misali jihar Kano, har yanzu manyan tituna kaɗai zakace ba’a yawatawa yadda yake a baya, amma cikin lunguna da layuka har yanzu ana dabalbala, ana buɗe kantuna, ana kwallon kafa, ana majalisa, ana sallolin jam’i da sauran su. Duk wata hanya da akeso a dena cakuɗuwa, to ana nan ana cakuɗeɗeniyar, babu maganar tazara, wanke hannaye ballantana kuma sanya takunkumin fuska. Duk da cewa dole akwai masu uzurai da dama da dole se anyi musu uziri, amma dai ya kamata mu girmama doka. Ni kaina da nike wannan rubutu, na shafe kimanin sati guda banda lafiya, wanda hakan har ya janyo aka fara azumi babu ni, tabbas akwai masu irin uzura-uzuran mu da suke bukatar suje can zuwa can domin neman lafiyar su, to amma banda waɗanda kai tsaye dokar suke aibantawa.
Ya kamata Gwamnatocin jihohi su ɗauki tsaruka domin kyautatawa mutane, kuma su tabbatar da cewa mutane sunbi duk wata doka da aka sanya, domin wannan cutar gaskiya ce, kuma tana kashe mutane. Misali, jihar Kano na ɗaya daga cikin jihohin da suke ɗaukar wannan cuta ba gaskiya ba, kuma suke wasa da wannan kullen da aka yiwa jihar. Taimakawa mabukata na ɗaya daga cikin abinda zai sanya mutane subi doka, domin da yawan marasa karfi suna gararamba ne layi da lunguna gidajen masu kuɗi suna neman tallafin abinda zasu ciyar da iyalansu. Taimaka musu Musamman da kayan abinci zai sanya asamu su zauna guri ɗaya, musamman a cikin wannan wata da kowa yake bukatar abinci bayan an sha ruwa. Gwamnatin Jihohi ya kamata suyi amfani da masu unguwanni domin gano waɗanda sukafi bukata, domin kowa yasan wanda yake cikin tsananin taimakon da yake bukatar taimakon, hakan kuma tabbas zaiyi maganin ƴan siyasar da zasuyi amfani da wannan kayan suyi awon gaba dasu.
Cutar corona tana ta kashe al’umma, amma mutane sunayin duk wani shakulatin bangaro da hakan, mutane da dama sun dogara da cewar idan har da gaske akwai wannan cutar, to ance ba maganin ta, maiyasa mutane suke warkewa? Mutane har yanzu basu ilmantu da kalaman likitoci da sukace garkuwar jikin ɗan adam itace take kashe kwayoyin wannan cutar ba, wanda kuma da yawan masu shekaru da masu wasu cututtukan garkuwan jikinsu baya iya kare kwayar tasiri a jikinsu, wannan ya sanya cutar tafi kashe masu shekaru da kuma masu cututtuka. Abin damuwar anan shine, da yawan mutane zasu ɗauki wannan cutar, amma kuma su yadawa iyayensu ko ahalin su masu yawan shekaru wanda hakan yake janyo salwantar rayukan su, kaga kenan anan killace kan shine abu mafi tasiri da zai rage yaɗuwar wannan cutar.
Ya kamata muyiwa kanmu faɗa, muyi duba zuwa manyan kasashen duniya irinsu Amurka, Faransa, Sifaniya da Italy yadda dubunnan mutane suke mutuwa sakamakon wannan cutar, mu duba yadda kasa mai tsarki Saudiyya ta soke umrah, sallar asham da sauran ibadoji saboda wannan cutar, shin hakan ba zai zame mana izina mu yarda cewar akwai wannan cutar ba?
Tabbas muna cikin wani hali na ha’ula’i da muke neman ɗaukin Ubangijinmu, muyi amfani da wannan wata mai daraja muyi roko agareshi ya yaye mana wannan cutar. Sannan kuma mubi duk wata doka da aka sanya domin lafiyar mu, yau idan wanin mu ya kamu, mune zamu wahala, hakan bazai shafi Ƴar gidan Ganduje ko ɗan gidan Elrufa’i ba, idan ma mutuwar ne, to mune dai zamu mutu ba abinda wani jami’in Gwamnati zai iya yi mana, don haka hakan ya rage garemu, walau mubi doka mu zauna lafiya, ko kuma mu taka doka mu wahala.