Idan Fadi Wa Mahukunta Gaskiya Ya Zama Abin Tuhuma, Akwai Ranar Kin Dillanci

Daga Ado Umar Lalu/Shamsu Muhammed

Aikata laifukka na tarzoma suna zama babbar barazana ga zamantakewar jama’a. Duk inda ayyukan tarzoma suka sami gindin zama a cikin mutane suna haifar da tsoro, asarar rayuka, dukiyoyi gami da raba mutane da matsuguncin su ya tilasta masu gudun hijira.
Jihar Katsina ta kasance daya daga cikin jihohin da ayyukan tarzoma suka tagayyara sakamakon maharan daji, barayin shanu da kuma garkuwa da jama’a wayanda sukayi sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyin Katsinawa ta hanyar maida mata zawarawa, yaya suka zama marayu da salwantar dukiya mai dimbin yawa.
Ta’azzarar da wayannan ayyukan tarzoma sukayi ya haifar da koke-koke daga cikin jihar Katsina da sauran bangarori domin daukar matakan kawo karshen lamarin wanda kawo yanzu akwai wasu kananan hukumomi da suka zama masu matukar hadari sakamakon yadda maharan daji ke cin karen su babu babbaka.
Tabbas hakki ne akan gwamnati ta dauki dukkan matakai domin kare rayuka, dukiyoyi da kuma mutuncin talakawan da take mulka. Yanayin da al’ummar jihar Katsina suka sami kan su na firgici da jikkata su da maharan daji ke haddasawa ya sanya rayukan su sun zama tamkar na kiyashi kuma kawo yau, wannan matsala ba’a shawo kanta ba.
Gwamnati ta yi yunkurin sasantawa da yin tayin afuwa ga maharan dajin amma kawo yanzu kwalliya bata biya kudin sabulu ba domin ana ci gaba da kashe Katsinawa da sace su a wasu sassan jihar.
Ana cikin wannan yanayi ne sai ga shi gwamnati jihar Katsina ta sanar da shirin ta na sake tsugunar da maharan daji ta hanyar sama masu matsugunni na dindindin da ababen more rayuwa.
Sanar da wannan kudiri ya sha suka daga ciki da wajen jihar Katsina wanda yazo ne a lokacin da al’ummar da maharan daji suka jikkata suke cikin halin tausayi na tagayyara amma maimakon a basu kulawa ta musamman sai gashi hankalin gwamnati ya karkata wajen yiwa maharan daji gata.
Daya daga cikin mashahuran mata a jihar Katsina Hajia Bilki Kaikai tayi korafi ta koka akan wannan shiri na gwamnati a hirar ta da Yusuf Jargaba wakilin gidan radion Jamus na sashen hausa ya yi ganin yadda yanayin yangudun hijira suke cikin mawuyacin hali da wadanda suka jikkata da tagayyara maimakon a basu kulawa ta musamman sai ga shi an mayar da hankali akan maharan daji.
Shi ma fitaccen Lauyan nan Bulama Bukarti mai fafutuka shi ma dai ya yi shakku akan wannan mataki domin tantance wayanda suka tuba tuba na hakika ba tuban muzuru ba.
Sai gashi maimakon a dubi kokawar da Hajia Bilki Kaikai tayi da idon basira ayi gyara sai gashi an gurfanar da ita a gaban sharia saboda ta fadawa gwamnati gaskiya.
Wannan shigar da kara ya baiwa mutane da dama mamaki ganin cewar Mahadi ya sako wannan gwamnati gaba maici yana mata tonon silili amma yana watayawa abunsa. Daga kin gaskiya dai sai bata.

Ado Umar Lalu Da Shamsu Muhammed sun rubuta ne daga Jihar Katsina

Exit mobile version