Daga Khalid Idris Doya
Tun bayan darewarta kan karagar mulki, Gwamnatin APC karkashin Shugaba Muhammadu Buhari, ta himmatun wajen tabbatar da ganin an samu tsaro ta kowane bangaren a Nijeriya. Saboda haka ne ta bada karfi sosai don ganin an kawo karshen masu tayar da kayar baya a yankin Arewa Maso Gabashin kasar, wanda ya hada jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Taraba, Gombe, da kuma Bauchi. Wadannan yankuna suna fuskantar tashin hankali na kashe-kashe, zubda jini da kuma asarar dukiya ta bilyoyin naira. Matsalolin tsaron wadanda suka hada da Bokoharam, masu garkuwa da mutane, manyan ‘yan fashi da makami, barayi da dai sauransu.
Baya ga wannan matsalar, akwai batun satar mutane da kuma ayyukan fashi da makami wadanda suke faruwa a manyan hanyoyin kasar nan, musamman Abuja zuwa Kaduna, har ila yau, balahirar satar shanu da farwa rugogin Fulani da hari, a sace matansu, shi ma na cikin manyan abubuwan da Gwamnatin ta sako a gaba domin ganin ta magance su.
A irin wannan tafiya ne, ake samu jaruman maza ‘yan sa-kai, wadanda suka sadaukar da kansu, lokacinsu da kuma rayuwarsu domin ganin sun taimaka wajen samar da zaman lafiya mai ma’ana. Sai dai kwana biyu ya tsagaita saboda matsalolin da yake fuskanta na idan ya kama mutum, sai a dauki lauya a fito da shi, daga bisani a dawo ana farautarsu.
A wata zantawa ta musamman da ya yi da LEADERSHIP A Yau Asabar, Shehu Aljan ya bayyana cewar a shirye suke su bada gudunmawarsu don shawo kan matsalar tsaro a kasar nan “Matsalar satar shanu tana daya daga cikin matsalolin da suke addabar al’amarin tsaro da kuma tattalin arzikin kasar nan. Tun lokacin da na sa kaina wajen ganin an shawo kan matsalar na rika jan hankalin gwamnati ta taimaka mana mu ’yan Banga don mu fatattaki barayin shanu, abin akwai daure kai a ce Fulani a junansu suna yi wa juna fashin shanu”. In ji sa
Da yake bayyana takaicinsa kan yanda suke farautar miyagu da kamo su amma abun takaici sai ‘yan sanda su bada belinsu a maimakon kai su gban kuliya.
Haka zalika Shehu Aljan ya taba kama wani dan Boko Haram, kuma bai yi kasa a gwiwa ya mika shi a hannun ‘yan sanda, inda su kuma suka bayyana cewar su ne suka kamo shi, alhali Shehu Aljan da mutanensa ne suka yi nasarar kamo dan Boko Haram din.
“Bai kamata a yi min haka ba, na kama mutum, ya dace a jinjina min kuma a yaba min. Sai kawai gani na yi a jaridu ‘yan sanda suna fadin su suka kama shi. Irin wannan yana sanyaya gwiwar mutum wajen sadaukar da ransa, dukiyarsa, lokacinsa da dukkanin kwakwalwarsa wajen ganin Nijeriya ta samu fita daga matsalar tsaro.” A cewarsa.
Sanin kowane wannan lokacin da garkuwa da mutane ya zama ruwan dare, kuma abun rainin wayo da ke faruwa a kasar nan. “Tabbas jami’an tsaro suna kokari wajen shawo kan matsalar satar shanu, garkuwa da mutane amma fa gaskiya suna bukatar agajin ‘yan Banga sosai, domin ‘yan banga suna da rawar da suke takawa wajen kamo miyagun a cikin daji da kuma birni”. In ji Shehu Aljan
Abun takaici da kasar Nijeriya irin wadannan mutanen bayin Allah da suke sadaukar da ransu don a samu kwanciyar hankali a maimakon shugabanni a matakai daban-daban su jawo su a jika wajen taimaka musu da abubuwan da suke bukata don a samu nasara sosai amma ina. A bisa haka ne ma Shehu Aljan ya taba bayyana damuwarsa kan irin wannan halayen, inda ya ce “Ya kamata gwamnati ta zauna da mu, mu kuma sai mu sanar da ita yadda matsalar ta fara da kuma yadda za a magance ta. Mutanen Jihar Zamfara sukan kira mu su bukaci taimakonmu saboda yawaitar sace-sacen shanu a jihar.
Daga cikin kokarin da Aljan ya yi wa Nijeriya akwai kama barayin shanu ba adadi a garuruwa daban-daban, sannan ya kwato shanu marasa adadi daga hanun barayin a lokuta mabambanta.
“Wadannan mutane sun samu horo na musamman, idan har suka ga shanun sata nan da nan za su gane su, inda ba tare da bata lokaci ba za su sanar da mu, mu kuma sai mu kai samame wurin. Babu wanda ya san mutanen namu, ko shi ne sarkin wayo ba zai gane su ba.” In ji Shehu Aljan.
Alhaji Shehu Musa Aljan ya ce galibin rikicin da ake yi a jihohin Bauchi da Kaduna da Filato barayin shanu da ’yan fashi ke haddasawa, “yawanci rigingimun da ake yi a jihohin Bauchi da Kaduna da Filato wasu marasa kaunar zaman lafiya ke haddasa su don sace dukiyar jama’a da kuma haifar da fadan kabilanci da na addini.”
Musa Aljan ya ce babbar matsalar da suke fuskanta shi ne matsalar da ‘yan sanda ke haiharwa inda zasu kamo mai laifi kirikiri ga shaida amma sai a sake shi, “Mukan fuskanci matsala sosai daga wasu ’yan sanda da idan muka kama wadanda ake zargi da laifi muka mika musu da cikakkun shaidu sai su sake su, su dawo suna yi mana barazana. Misali a Jihar Filato na kama wasu da shanun sata da makamansu, amma sai aka juya maganar aka kama ni aka tsare, sai da aka yi bincike aka gano gaskiyata aka sake ni”. inji shi.
Haka a Jihar Kaduna ma ya taba kama mutane ya mika ga ’yan sanda amma aka sake su, kuma aka dawo aka sake tsare shi aka kamo su aka hada shi da masu laifin aka tura Abuja daga baya aka sake shi, “irin wannan ba komai ke jawosa bai sai wasu ‘yan sanda da basu da kishin kasar nan da suke cikin aikin, muna kira da ci gaba da tantance ‘yan sanda domin tsaftace aikin”.
Shehu Musa Aljan ya sha samun lambar yabo da jinjinawa a wajen jami’an tsaro a duk lokacin da ya kawo musu masu laifi amma abun takaici sai a sake masu laifin da kuma neman daura wa irinsa laifi, matukar gwamnati ba ta sanya ido kan irin wannan matsalar ba, nan gaba matsalar sata da garkuwa da mutane za ta fi karfin jami’an ‘yan sanda domin masu garkuwar sukan yi shiri ne na musamman.
A kwanan nan rundunar ‘yan sandn jihar Bauchi ta gabatar wa manema labaru da wasu masu miyagun laifuka ciki har da masu garkuwa da mutane, daya daga cikin masu garkuwar da kansa yake shaida wa manema labaru cewar shi bindiga ba ta kama shi kwata-kwata koda an harbe shi to ba za ta shige sa ba.
“Na kawo kaina nan wajen ne domin na tuba daga satar shanu a dajin Falgore sai na dawo jihar Bauchi da yin sana’ar garkuwa da mutane amma yanzu na kawo kaina domin na tuba ne ba kamo ni aka yi ba, ni na kawo kai na domin na tuba.”
Idan gwamnati na barin irin wadannan suna yin karfi da sanin dabarun kariyar kai to tabbas za a wayi gari ‘yan sanda ba za su yi fuskantar masu garkuwar ba. Amma su irin wadannan ‘yan bangan da masu sa-kai sukan san irin hanyoyin da miyagun ke bi su ma su nema don kariyar kan, kenan akwai bukatar a jawosu a jika domin magance matsalolin tsaro a fadin kasar nan.