Connect with us

TATTAUNAWA

Idan Gwamnati Ta Tallafa Wa Sana’ar kwara Za A Samar Da Ayyuka – Hon. Ibrahim

Published

on

HON. GARBA IBRAHIM jigo ne a kungiyar masu safarar kwara a Jihar Neja. A tattaunawarsa da Wakilin LEAERSHIP A YAU, MUHAMMAD AWWAL UMAR, ya ce, sana’ar kwara ta na samar da kudaden shiga ga gwamnati, sannan ta na bai wa dimbin jama’a damar samun ayyukan yi. Ga hirar kamar haka:

Gwamnati nata yunkurin samar da ayyukan yi ga jama’a kuma ta na neman hanyoyin samun kudin shiga. Wadanne hanyoyi ne ya kamata gwamnati ta shigo, don amfana da wannan sana’ar?
Haka ne, da farko da gwamnati za ta inganta wannan sana’ar da hanyoyin kudadenta sun karu kuma an samar da ayyuka ga jama’a. Domin ita wannan sana’ar ba wai kawai a saye kwara ayi man kade ba ne kawai, yanzu zamani ya zo da ta ke kokarin maye gurbin sana’ar koko. Yanzu maganar da na ke yi da kai a duniya kwarar da ake samarwa a Neja kusan itace kasuwar duniya ta kwara ke bukata saboda kyau da ingancinsa.
Amma idan ka duba mu ne kuma baya a wannan harkar kusan yanzu jihar Kogi tana yunkurin mamaye kasuwar, duk da cewar kwarar da ake samarwa ta yi kasa sosai saboda matsalar masu yanke itace kuma an kasa maye gurbin wadanda aka illatar, yasa ba a iya samar da adadin kwarar da ake samarwa a shekarun baya.

Amma ba ka tsammanin cewar, kila saboda ku masu harkar ba ku nunawa gwamnati muhimmancinta ne ba ya sa ba ta mayar da hankali a kai ba?
Gaskiya ne, a waccan gwamnatin da ta gabata, ta Dakta Mu’azu Babangida Aliyu an kirkiro shirin inganta itatuwa wanda wannan shirin ya kawo sauki kona daji da yankan itace wanda yasa kusan dukkanin itatuwa masu albarka sun rayu, amma bayan zuwan wannan gwamnatin duk da cewar matsaloli sun yawa tana kokarinta amma ba kamar gwamnatin da ta shude ba.
Maganar sanar da gwamnati muhimmancin harkar kwara, mun samu zama da maigirma gwamna sau biyu, amma dai har zuwa yanzu da muke hira da kai ba mu ga wani yunkurin da aka yi akai ba.

Wane alfanu ke cikin sana’ar?
Ta na da alfanu da dama, bari in fara da bangaren kudin shiga, yanzu kowace mota da za ta tashi daga jihar Kogi sai mun biya mata haraji, ka ga ke nan idan mota biyar zuwa goma za su tashi a yini wani abu ya shiga aljihun gwamnati, na farko ke nan. Bayan nan a ton daya kawai da ake sayar da shi daga dubu arba’in da biyar zuwa dubu talatin a kallan sai ka samu sama da mutum biyar da suka anfana, daga kan masu tsintowa, zuwa fasa ta da dafawa har kan direban da zai dauka zuwa inda ake bukata idan ka duba ita kadai a kallan za ta iya baiwa dubban mutane aikin yi.

A baya ka bayyana cewar ita kanta kwarar ta na da alfanu da dama. Yi ma na karin haske.
A shekarar da ta gabata mun zauna da wasu mutanen China kan cewar zasu rika sayen bawan da aka fitar da ainihin diyan kwarar, ka ga akwai wani mai muhimmanci ke nen da bawan zai iya bayarwa.
Sannan ana yin man gashi da ita, ana sanadarin man cin burodi da ita, sannan ana man shafawa da ita, akwai abubuwa da dama masu alfanu ga jikin dan Adam ke bukata da man kwara zai iya bayarwa.

Idan mun duba kusan kasashen duniya na gwaggoriyon sayenta kuma gaya ba itaciya ba ce da za a iya anfana da ita lokaci daya. Wadanne hanyoyin ya kamata a bi wajen inganta ta?
Gaskiya, kwarar da muke da ita yanzu, kafin a fara cin moriyarta sai ta dauki adadin shekaru hudu da shukawa ko tsirowa, amma bayan wasu tafiye tafiyen da muka yi akan harkar a kasashen duniya kamar Ghana, Tanzaniya da wasu kasashen nahiyar turai, mun fahimci irin cigaban da aka samu domin yanzu akwai tsirran da aka samu za ka fara cin moriyar itaciyar kadanya da ke samar da kwara cikin shekaru biyu.
Kuma idan ka duba tana da anfani domin tana kare kasa daga zaizayewa, kuma wani abu da zai baka mamaki da za ka samar da gonar kadanya za ka iya daukar adadin shekaru hamsin zuwa sittin da biyar kana anfanarta, kadanya ita kadai ke da irin wannan martaban.

Ka bayyana cewar kusan kasashen duniya sun fi sha’awar kwarar da a ke samarwa a jihar nan.
kwarai kuwa, mu dauki misali kasar Amurka, man kwarar da ake samar a kasar nan yafi tasiri a kasuwar duniya da kasar Amurka ke bukata, domin da za ka samu damar fitar da kwara ko man kwarar da ya fito daga jihar nan a kasuwar duniya sai ka ga kwarar da ta fito daga jihar nan tafi tasiri da sauran shigewa, amma samun tallafin gwamnati yasa yanzu mu ne baya wajen fitar da kwarar duk da irin darajar da ta mu ke da shi.

Zuwa yanzu ko akwai wani yunkurin da ku ke yi na ganin kun kara wadatar da kwarar a kasuwar duniya?
Da farko dai muna tafiya ne a kungiyance, amma da gwamnati za ta shigo mu samu tallafi daga gare ta koda ta hanyar zuba jarin gwamnati ne lallai da harkar kwara ya kara inganta a jihar nan. Matsalar da muke samu yanzu manoma ba su san muhimmancinta sosai ba, amma da za a rungumi noman kwara da harkar noma ya kara inganta a jihar nan, ita itaciya ne mai tattare da albarkatu da dama, domin ko a gonar ka za ka shuka za ta taimaka wajen samun kayan marmari kuma ka samu kudin shiga a cikin harkokinta wanda wannan dole sai ta shigo wajen fadakar da kan manoma muhimmancin ta.

Wane karin haske ko kira za ka yi wa manoma?
Da farko karin hasken da zan yiwa manoma shi ne, yana da kyau su fara neman tsirran kadanya a kallan ashirin ko sama da hakan, domin zai kare gonar ka daga zaizayar kasa, zai taimaka maka wajen abin biyan bukatar yau da kullun, domin mai noman kwara a kowani lokaci bai rasa aikin yi, idan ka cire anfani gona sai ka dauki adadin watanni hudu kana cin kasuwarta.

Gwamnati fa?
Ita kan gwamnati da ta san alheran da ke ciki da ta muhimmantar da shirin noman kadanya ga ma’aikatar aikin gona kamar yadda ta ke karfafa sauran bangarori. Yanzu kimiyya ya kara fadada shirin ta hanyar samar tsirran kadanya wadanda za a anfana a cikin shekaru, to kafin wani adadin shekaru da ta san abinda ta yi domin irin hanyoyin da za ta bude samun ayyuka ga jama’a da samun abin biyan bukatun yau da kullun da kudaden shiga daga gwamnati da ba ta yi sa ke ba.

Su matasa fa, musamman masu korafin rashin aiki?
Ai matasa su ne kashin bayan cigaban kowace al’umma, maganar rashin aikin yi babu shi, domin wannan dama ce musamman ga mai zuciya. A baya na fada ma daga kan direba da yaronsa su da ke dakon daukarta a mota, ka ga an rufe wannan gurbin, sannan ka dawo akan masu tsinta, da masu dafawa da shanyawa har kan zuwa ‘yan dako da lodinta a mota da mu masu safararta da masaya ka ga ita kadai za ta iya baiwa dubban matasa aikin yi.

A karshe, wane kira gare ka?
Yakamata gwamnati ta shigo, masu hannu da shuni su shigo domin kowa na da rawar takawa. Ai yanzu a na maganar hasarar da ake yi na anfanin gona ta hanyar hare haren da mahara masu dauke da bindiga ke kai masu yasa da damar manoma yin hasarar anfanin gona, amma da za ka rungumi harkar noman kadanya, ba bu wata hasara a cikin ta domin indai ba yanke itaciyar ba, ta nan za ka cigaba da jan zaren ka, domin ba a iya cire ta a tafi da ita. Koda mahara sun shigo ba wani illar da za su yiwa itaciyar.

Hon, mu na godiya da ba mu takaitaccen lokaci.
Madallah.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: