Idan Har Ka Dogara Da Kanka, To Ka Huta Da Gori Wajen Mutane – Fa’iza Kawule

Abin koyi ne ga matasa masu aure da marasa aure,maza da mata su tashi su nemi na kansu domin taimakawa kansu da abokan zaman takewar su, har ma da iyayen su. Hakan zai bawa sauran marasa aikin yi kwarin gwiwa wajen neman na kansu dan dakile yawan bani-bani, da zaman banza, da kace nace  a zamantakewa. Shafin Adon gari ya zanta da daya daga cikin masu neman na kansu inda ta bayyana mana yadda take gudanar da sana’o’inta ga kuma yadda hirar ta kasance.

 

 

Da farko masu karatu za su so jin sunan ki da kuma dan takaitaccen tarihin ki…

Sunana Faiza Danlami Kawule, an haife ni a garin azare nayi makarantar firamare a azare, Sakandare a alkaleri na fara N.C.E ban gama ba na bari nayi aure na hayayyafa, ina zaune lafiya a gidan miji na.

 

Yanzu a bangaren aiki ko karatu, sana’a, wanne mataki kike, ko zaman gida kike?

Ina sana’ar kaji a gida na da dambun kaji da zannuwa.

 

Masu karatu za su so jin meya taba faruwa dake a rayuwa na farin ciki ko akasin sa wanda  ba zaki taba mantawa da shi ba?

Da aka bani kujerar Makkah lokacin da naje madina naji dadi sosai da naje ka’aba ma sai naji wani sanyi a zuciya ta, har da farin cikin na ganni a kasa me tsarki.

 

Wacce shawara zaki bawa mutane game da sha’anin rayuwa ta yau da kullum wanda idan suka yi koyi ko amfani da shi rayuwa zata inganta?

Mutum yayi hakuri da rayuwa a yadda ta zo mishi, ya kuma dogara da Allah ya guji fadawa a halaka, mutum ya kiyaye bin abokai ko kawayen da bana gari ba.

 

Masu karatu za su so jin ko kina da aure?

Eh ina da aure har da yara bakwai.

 

Masha Allah! Kamar yanzu wanan sana’a taki ta sayar da kayayyaki idan mutum yana son farawa, zai sari kaya ne kawai ya fara siyarwa ko sai yayi bincike?

Eh sai kayi bincike kafin ka fara saye da sayarwar saboda babu yadda za’a yi ka fara sayar da kaya ba kayi bincike ba.

 

Me ya jawo hankalin ki kan wadannan sana’oi?

Saboda dogaro da Kai, kuma ba za ka dogara da mutane ba, kuma za ka iya biyan bukatun ka ba sai ka jira mai gidan ka ba.

 

Shi wannan sana’o’in naki a gida kike ko kina da shago? Misali mutum zai koya saye da siyarwa kamar yadda mukai magana a baya shin sai yazo inda kike ne ko a waya mutum zai iya koya ?

A gida ake zuwa ake saya ba sai nakai shago ba yanzu dai ina neman shago saboda ina samun ciniki da yawa sai na fadada kasuwa, eh zan iya koya musu inda masu so sosai ma.

 

A baya kin sanar da masu karatu kina karatu koya kike hada wadannan abubuwa biyu ga karatu ga sana’oi?

Eh haka ne kam, amma yanzu bana karatu saboda na gama tun da jimawa, yanzu kawai sana’a nake yi shi kadai babu komai.

 

Wace shawara zaki bawa matasa mata ‘yan uwan ki kan yanayin rayuwa?

Ya kamata su daina zaman banza su tashi su koya sana’ar yi saboda shi ne zai taimake su ya kuma rufa musu asiri.

 

Duba da yadda rayuwa ta koma yanzu, mai zaki cewa iyaye musamman mu mata da ma mazan duka akan abinda ya shafi tarbiyya?

Tarbiyya tana da matukar amfani a rayuwar al’umma musulmi baki daya, ya kamata iyaye su rinka koyar da yaran su tarbiyya da kuma sanin ya kamata, yara suji tsoron, Allah su kuma iyaye su rinka yin nasiha wa yaran su, yara ba abun duka da zagi bane iyaye ya kamata su  kiyaye yin duka da zagi wa yaran su saboda duka da zagi baya gyara.

 

Ferants shul safot deya cildiren in eni fosibil we de kan so dat deya cildiren shul not  fel into eni bad habits or bihebiyos.

 

Wane kira zaki yi ga mata akan dogaro da kansu?

Mata da ma maza ya kamata kowa ya dogara da kansa ya kama sana’ar yi, saboda zaman banza bai yi ba ya  kamata ko wani dan Adam ya kama sana’ar yi saboda ya taimaki kansa da ‘yan uwan sa har ma da iyayen sa, Sana’a tana da matukar amfani a rayuwar dan adam, saboda baka tsaya dogaro da kowa ba kuma baka tsaya jiran albashi ba, ba kuma ka tsaya jiran taimako a wajen kowa ba (kawa ko aboki) idan har ka dogara da kanka to ka huta da gori a wajen mutane.

Exit mobile version