Idan Har Matasa Ba Su Daina Shan Kwayoyi Ba Karshensu Mutuwar Wulakanci – Maitama

Maitama

Kowa dai ya san yadda matasa suka zama kashin bayan al’umma da ma duniyar bakidaya dole sai da matasa ake komai na rayuwa. Sa’annan duk muna da sanin yadda suke fadi-tashi domin ganin su ma sun zama abin alfahari a rayuwarsu da ma ta wadanda suke kewaye da su. Sai dai kash! Ana samun bata-gari da ke dora wmatasanmu a turbar shaye-shaye da sace-sace. Da yawan wadanda ake lalatawa marayu ne wanda ba su da mataimaka sai Allah babu gaba babu baya, haka babu tudun dafawa domin cinma kudurin su a rayuwa, marayu da yawa na shiga halin ‘lahaula’ hade da daura hannu a ka idan suka rasa madafa, wasu da yawa na fadawa garari, kalilan ne ke iya tsallakewa. Kan wannan matsala ce wakiliyarmu BASIRA SABO NADABO ta tattauna da wani matashi da ake wa akabi da MAITAMA, wanda ya kasance abin koyi ga sauran matasa bisa irin gwagwarmayar da ya yi a rayuwa. Ku karanta ku ji yadda zantawar tasu ta kasance:

 

 

Assalamu alaikum, masu karatu za su so jin dan takaitaccen tarihin ka…

 

Wa alaikumus salamu warahmatullahi wabarakatuhu. Kafin na ce komai zan mika yabo da jinjina ga Ubangijin Al’Arshi da ya kak’i sammai bakwai ba tare da neman taimako a gurin kowa ba, kuma saboda isa da ikonSa ya shinfida kassai bakwai ba tare da neman shawarar kowa ba. Ba zan iya bude bakina ba har sai na mika salati mara iyaka ga Annabin da babu wani bayan shi, Manzon da ya zo mana da hasken da ke haskaka mana hanyar da muke bi har zuwa ranar da kiyama zai tsaya, salati da yabo su kara tabbata ga ahalin gidansa da sahabbai da tabi’un tabi’una.

 

To da farko dai ni Sunana Yusuf Sabo Nadabo wanda aka fi sani da Maitama. An  haife ni a cikin garin kaduna, na yi Primary da Secondary school dina a Sheikh Abubakar Gumi Collage Kaduna. Na yi Diploma a Abubakar Tatari Ali polytechnic Bauchi, sai kuma na yi HND na anan Kaduna polytechnic. Na je Camp ina a NYSC Permanent Orientation Camp a Former Girls Model Secondary School Eziama Obaire, Nkerre Local Gobernment Area, Imo State, daga nan sai na yi relocating zuwa Kano, inda na yi PPA na a Bebeji cikin jihar ta Kano.

 

Mun ji tarihin rayuwa da kuma inda ka yi karatu. Yaya kalubale da kuma gwagwarmayar rayuwanka ta kasance, duba ga wannan zamanin da muke ciki da komai na rayuwa ya zama sai addu’a ce kawai mafita?

 

Amin. Alhamdulillah kawai zan ce domin duk inda muka tsinta kanmu sai dai mu gode wa Allah. Duk tsanani duk wuya sai  Shi din dai Rabbi samawati wal Ard nake godewa, kullum addu’a nake yi Allah ya fitar damu a wannan halin da muke ciki. Su kuma wanda suke da hannu cikin halin da muka shiga, Allah yashirye su in ba masu shiryuwan ba ne Allah Ya san yadda zai yi da su. Mu Kuma Allah Ya bamu ikon cin wannan jarabawan, Allah ya bamu yanda zamu iya har mu taimaka wa wanda basu da shi.

 

 

Ma sha Allah! Wace rana ce a rayuwarka da ba za ka taba mantawa da ita ba kuma mene ne dalili?

 

Ranar da ba zan taba mantawa ba, shine ranar da mahaifina ya Rasu wato 11/08/2002 sai kuma ranar 6/04/2004 a wannan ranar da mahaifiya ta tarasu, sai kuma ranar jaji barin babban sallah na 2011. A wannan ranar ne sallah ya kamani a makaranta kuma gashi bani da kosisi, kuma dai kowa yasan in sallah ya zo zai so yaci abu mai dadi kuma ni ban iya roko ba, Ballantana na kira gida a turomin da kudi! Akwai abokindakina mai suna Sadik Bala. Shi iyayen shi sun tura mai da kudi yaje yin sallah a gida, sai na kira shi yaranta min kudi tunda shi yana gida sai ya ce min bashi da kudi amma zai turomin da 1000 ta banki, ni kuma bani da ATM da ya turomin da 1000, sai na je gurin mai shagon da muke siyan kayan abinci a gurinsa, na ce mai ya ban aron 300 zanje gari na ciro kudi, domin daga inda muke zuwa bank road kusan 150 ne kudin mashin, kuma lokacin ba ayin POS, sai dai kaje banki ko kuma Atm machine ka cire kudi, bayan ya bani kudin na wuce banki, na shiga banki na cika teller zan cire 1000, wallahi mutane dake gabana sunfi 50 kowa yana son ya cire kudi yayi bikin sallah, sai da layi yazo gareni, na ba da teller sai naga an dawo min da teller na, wai bazan iya cire 1000 ba saboda akwai bank charges inda ake cirewa sai dai na cire 500 haka nan na amsa, na mai da shi zuwa 500 tare da yin signing na bata, ko da cashiered ta bani kudin, kusan fusgan kudin na yi kar wanda suke baya na suga abin da na amsa. Tun daga wannan lokacin ne na fara tunanin ni maraya ne, a wannan lokacin nasan cewa bani da uwa ba  uba wallahi ina kan mashin amma hawaye suna zuba a idona! Na yi kuka kaman dan shekara 1 wanda yake jin yunwa ba bashi abinci ba, karfa ku manta naci bashin 300 kuma acikin 500 in zan biya bashi. Tun daga wannan lokacin nake son taimakawa duk mutumin da akace maraya ne shi. Allah Ka ji kan iyayenmu da musulmai bakidaya.

 

 

Bayan ranakun bakin ciki. Wacce rana ce kuma ta farin cikin rayuwarka?

 

Ranar farin ciki a rayuwata ta ita ce ranar da na kammal karatuna, har na ganni a Camp na zo bautan kasa wanda yanzu haka Ina shirye shirye yin masters. Sai kuma ranar da wani mai gidana ya min albishir in cewa in na gama Diplomana nazo zai bani aiki. Wanda kuma ya cika alkawarinshi, kafin gwamnatin Goodluck su tsayar da company din. Sunan wannan bawan Allahn wato mai gidana na farko Shine Barrister Muhammed Sani Suleiman Allah Ya saka mai da alkhairi, Allah Ya mai albarka. Sai kuma ranar da na hadu da wata halitta mai kama da yan Aljanna.

 

 

Wani kira za ka yi ga matasa masu dabi’ar shaye-shaye?

 

Kiran da zanyi ga matasa yan’uwana akan shaye-shaye shine. Idan kana son ka zama Gaye ba lallai bane sai ka hada da shaye-shaye, babban Gaye shine wanda zai rike addininsa da kuma mutuncin sa. Shaye-shaye bata da amafani sai dai ta lalata ma rayuwanka ban san dadinta ba,  to amma nasan illanta tunda ina ganin tana haukatar da matasa masu yinta. Ka yi kokari ka dinga ibada kan lokaci, dan ko wannan zai hanaka yin abinda bai dace ba a rayuwarka.  Babban illarta shine za’a daina ganin ka da mutunci, kaninka zai zama yayanka, yayyinka zasu mai daka mahaukaci. Duk abinda ya faru a gida na rashin gaskiya to ko ba kai bane za’ayi zargin ka. Allah ya shirye mu gabadaya kuma ya hanemu aikata aikin da-na-sani. Amin

 

 

Me kake gani zai iya janyo musu in har ba su bar shan miyagun kwayoyi ba?

 

Tabbas inhar basu daina shan muyagun kwayoyi ba to karshen su hauka ce tare da mutuwar wulakanci saboda hatta jana’izarka sai dai ‘yan’uwanka a gurin shaye-shaye ne zasu maka to ina amfanin hakan? Kawai abinda nake ganin ya dace shine su yi hakuri kuma subar wannan dabi’ar domin ba-za-ta haifar musu da d’a mai ido ba.

 

 

Mun ji tarihin maitama amma ba mu ji ka yi maganar iyali ba. A kasuwa kake ko kuma an kusa kiran LEADERSHIP A Yau wurin daurin auren ka?

 

(Dariya) hakika kin tabo mun inda yake mun kaikayi. A gaskiya dai Maitama ba a kasuwa yake ba, tunda Maman Adeela ta kusa yin wuff da ni. Maman Adeela wata baiwar Allah ce mai kama da matayen Aljanna har na kan kirata da hutun ayn ta duniyata, saboda ta san darajan iyayenta, yan’uwanta da kuma duk wani musulmin da ke zaune tare da ita ta san mahimmancinsu kuma tana ba kowa hakkinsa. Babban abinda ke kara birgeni da ita shine Iyayen ta sun dauke ni kamar yaron da suka tsuguna suka haifa a cikin su, ba ni da bakin godiya a gare su sai dai na ce Allah ya saka musu da alkhairi saboda sun san darajan bayin Allah kuma ‘yar su ta yi gado na kwarai. A yanzu haka ma kusan kullum sai iyayenta sun min addu’a tare da sanya min albarka. Ina son Mama sosai, ina jinta a zuciyata kamar ita ce ta haifeni.

 

Sannan wani abu da ya kamata LEADERSHIP A Yau ta sani game da matata Maman Adeela. Gimbiya ce wanda take rike da kambun sauratar zuciyata. Ita ce mace ta farko da duk dangina suke son ta zama sirrikarsu. Maman Adeela mace ce da kodayaushe take tausayina tare da bani shawarwari masu kyau akan Rayuwar duniya. Yanzu duk wani tunanina naga na yi wuff da ita ne wanda a wannan ranar nasan duk wani halitta a duniya sai na fishi jindadi. Saboda duk wani bawa burinsa shine ya samar ma yaransa uwa tagari shi yasa nake wa Adeela sha’wan ta kasance mahaifiyarta in shaa Allah.

Zuwa gare ki matata. Allah Ya ja zamanin Gimbiyata mata a gidan Maitama Yusuf, ji nake ko rashin lafiya nake yi kuma ana neman jinin da za a samin cikin jikina to babu jinin da zai yi daidai dani sai jininta. Ina son ki

 

 

Shin Maitama yana da wani burin da yake son cike wa a rayuwarsa?

 

Sosai kam ina da buri a rayuwata. Babban burina shine na mutu a cikin musullunci sannan kuma na ga ranar da za’a daura min aure na Maman Adeela, sai kuma na koma makaranta domin yin masters. Ina burin na taimakawa yan’uwana da duk wani hallitta dake bukatar taimako domin a gaskiya ina son na ga nima ina taimakon mabukata ko dan rayuwar da na yi a makaranta.

 

 

Idan ka samu damar haduwa da shugaban kasan Nijeriya wani irin kira za ka yi gare shi domin ka nusar da shi abinda ya dade yana yi maka kaikayi a zuciya?

 

A yanzu idan na hadu da shugaban kasata mai adalci da gaskiya zan masa magana ne cikin ladabi da biyayya akan matsalar da talakawa ke ciki musamman ta gefen tsaro da kuma yunwan da ake fama da shi a rayuwa. A karshe kuma zan mai albishir da na samu matar aure mai kyawun zuciya irin na mahaifiyarmu Hajiya Aisha Buhari (First lady) wato Maman Adeela.

 

 

Allah ya kara arziki kuma ya cika maka wannan babban burin. Wani kira za ka yi ga matasa?

 

Kiran da zan yi wa matasa yan’uwa shine su tashi su nema na kansu karsu bari su zama yan bangan siyasa kuma karsu yarda a juyar musu da tunanin akan abinda bai dace ba, kuma ina kira gare su da su koma makaranta domin muna lokacin da karatunka shine gatanka, don haka a tashi a yi karatu kuma a hada da sana’a.

 

Wani abin ci da abin sha, da kalar kaya ka fi so, sannan wane abu ne mai saurin bata maka rai da kuma abin da ka fi so a yi maka kyauta da shi?

 

White rice da stews da cream salad duk yawan shi zanci tare edoctic ko Coca Cola. Sannan a sutura kuma na fi son kananan kaya amma yanzu Maman Adeela ta canza ni zuwa manyan kaya dan shi ta mun kwanaki.

 

A duk duniya in an cire iyaye da Maman Adeela Waye ka fi so?

 

Toh fa, ai abin a bayyane yake duk duniyata babu wanda nake so sama da ‘yan’uwana ba ina matukar son su sosai, sannan sai kuma abokaina.

 

Maitama, LEADERSHIP A Yau Na Yi Maka Fatan Alkhairi.

 

Na gode sosai. Allah ya kara taimakon ku da duk wani ma’aikacinta ina addu’ar  Allah Ya sa kufi haka. A karshe kuma in Allah Ya yarda ranar aurena zan kawo muku katin gayyata.

 

Ma Shaa Allahu.

A nan nima nake cewa daku da mu hadu a wanin satin, taku ce Basira Sabo Nadabo.

 

Exit mobile version