Idan Jinin Mutum Ya Yi Kasa Yana Iya Samun Matsalar Kwakwalwa –Masana

Dokta Nnenna Okafor wata babbar jami’a ce, a sashen maganin iyali ta ta asibitin kasa na Abuja, ta ja kunnen mutane cewar yadda jini yake ja kasa, yana iya kai wa ga lalacewar kwakwalwa, da kuma maganar rashin tsayar da hankali, ga kuma maganar rashin gani sosai.

Okafor ta furta haka ne lokacin da kamfanin dillancin labarai na  Nijeriya yake hira da ita, a Abuja ranar Talata.

Ta kara bayyana cewar matsalolin da za a iya shiga dangne darashin isasshen jini, sun hada da matsalar da kwakwalwa ka iya shiga, rashin tsayar da hankali akan al’amuran da suka kamata ayi su, jin kasala kasala, suma, rasa hankali, da kuma rashin gani sosai. Ta kara bayanin sai kuma matsalar zuciya, habo mai yawa, shan kwayoyin magani da yawa saboda maganin hawan jini, yana iya sa wa jini ya yi kasa.

Sai kuma lokacin da ake da juna biyu, amai, cututtuka masu yawa na iya samar da raguar jin ya yi kasa.

Ta ce jini na yin kasa ne lokacin da yake kasa da 90/60’’. Ta ba marasa lafiya shawara da su rage shan giya wato barasa, shan kayayyaki masu zaki, ta ba marasa lafiya shawarar su rika sa safa.

Ta bayyana cewar a rika sa kayan da ba zasu bada matsala ba, suna kuma bada dama yadda jin zai rika zuwa duk wuraren da suka kamata, ba kuma hana shi tafiya zuwa cikin sassan jiki.

Hakanan maganar sa kayan da suka dace suna kara samar da taimakawa wajen tafiyar jini, da kuma maganar allurer da za ayi ta jijiya, zai taimaka sosai ga marasa lafiya, wajen taimaka masu dangane da jinin su wanda ya yi kasa.

‘’Shan kayayyaki masu ruwa, cin abinci mai kyau, kayayyakin marmari, ganyaye, kaza mara kiba sosai, da kuma kifi, zai taimaka wajen habaka samun ci gaba daga jinin da ya yi kasa.

Okafor ta ba marasa lafiya shawarar cewar su rika zuwa asibiti ana duba lafiyarsu wanda ma’aikata ne zasu yi masu.

Exit mobile version