Idan Kana Da Sha’awar Fara Kasuwancin Wayoyin Hannu A Nijeriya, Ga Yadda Za Ka Yi…

 

Kasuwancin sayar da waya shine tsarin sayen wayoyin hannu daga kanfanoni, masu rarrabawa, ko dillalai masu izini, don sayarwa don samun riba. Wannan kasuwancin yana da riba sosai a Nijeriya saboda ba kowa ke sayen sabbin wayoyi ba, musamman tsakanin matasan Nijeriya. Damar wannan kasuwancin shine, yawancin ‘yan Nijeriya basa rike waya daya. A kowace shekara, idan sabbin nau’ikan wayoyi suka fito, ‘yan Nijeriya sukan zama a gaba a duniya wajen saye.

Zan yi bayanin yadda ake fara kasuwancin, inda ake sayen wayoyin don sake sayarwa, da kuma yadda ake sayar da wayoyin. Bari mu fara da yadda ake fara kasuwancin sayar da waya a Nijeriya yanzunnan.

Yadda ake fara kasuwancin sayar da waya a Nijeriya (iPhone da Android)

Bi wadannan matakan don fara kasuwancin sayar da waya a Nijeriya:

  1. Gudanar da bincike sosai:

Shiga gari ka yi binciken yiwuwar wannan kasuwancin. Ba ka bukatar biyan kudi don wannan. Shiga wuraren da suka fi hada-hadar kasuwanci ka gano irin kasuwancin da ke bunkasa a can.

Mayar da hankali kan yankunan da ke ma’amala da wayoyi da kayansa, tunda wannan shine babban layin kasuwancinka.

Shiga shago zuwa shago don sanin kudin wayoyi, duba wayoyi masu tasowa ka lura da farashin su sannan ka rubuta abubuwan da ka ke bukatar tanadar wa shagon ka.

Yi hira da masu wadannan shagunan kuma ka kimanta farashin wayoyin, farashin haya, biyan kudi don masarufi, yawan ma’aikatan da ka ke bukata, inda suke sayen haja kuma suna yin kididdigar yiwuwar aiki a duk wurin da ka zaba.

Samun jagoranci game da kasuwanci: Kafin ka fara kasuwanci, gana da mutumin da yake irin wannan kasuwancin da zaka fara.

Koyi abubuwa kamar sarrafa kaya, rarrabawa, talla, yadda ake gano wayoyi masu kasuwa, da kuma yadda zaka san farashin da ya dace don cajin samfuran waya daban-daban.

Haka zalika, dole ne ka san fasalin wadannan wayoyin da kake shirin fara sayarwa, yadda karfin kowane iri yake, kuma ka kasance a shirye don tambayoyi daga kwastomomi masu zuwa.

  1. Zabi wurin da ya dace don kasuwancin:

Zabin wurin da ya dace shine babbar muhimmiyar shawara da zaka yanke kafin ka fara kasuwancin sayar da waya a Nijeriya.

Gano kasuwancin ka kusa da masu saye kamar, inda yake da samari da yawa. Yi tunani game da masu irin kasuwancinka kuma ka san yadda banbanta kasuwancinka.

Kana iya la’akari da zaman shagonka kusa da kantin kasuwa, kusa da makarantu, manyan makarantu, da kusa da sauran kamfanoni masu zaman kansu.

Kana iya sanya shagonka kusa da shagon masu sana’a na waya da kuma a cikin cibiyar kasuwancin garinka inda yawan tafiya da kafa.

Ya kamata ka yiwa kanka wannan tambayar, idan kana cinikin wayoyi ne, da iphone, da tablets, da sauran na’urori kamar su iPad da iPods, shin mutanen da ke rayuwa a cikin muhallin da ka ke zasu iya sayen su?

Idan haka ne, to sanya wasu abubuwa kamar kudin haya, tsaro da aminci, filin ajiye motoci, da saukin samun damar zirga-zirgar ababen hawa zuwa yankin da kuma kasafin ka.

  1. Rubuta tsarin kasuwanci:

Dayan matakai mafi kima idan kayi la’akari da yadda zaka fara kasuwancin sayar da waya a Nijeriya shine rubuta tsarin kasuwanci.

Misali, kamar fara ginin gida, kana bukatar samun tsarin gini. Fara sabon kamfani yana bukatar tsari. Idan kana da tsari, zai tafiyar da kasuwancinka cikin sauki.

  1. Tushen jari:

Yawancin mutane sun daina yin kasuwanci saboda rashin jari. Kana iya samun duk adadin da kake so idan kana son nuna wa masu ba da bashi cewa za ka iya biya idan sun ba ka rance.

Jari shine rayuwar kowane kasuwanci, duk sauran abubuwan daidai suke, ba shi fifiko lokacin da kake son fara kasuwancin sayar da waya a Nijeriya.

  1. Yi rijistar kasuwancin:

Wani muhimmin abu yayin fara kasuwancin sayar da waya a Nijeriya shine yin rijistar sunan kasuwancin. Samun suna don kasuwancinka ta hanyar hada sunan Wayar da sunaka don kirkirar suna na musamman wanda za a samu a hukumar kula da harkokin kasuwanci (CAC).

  1. Rajistar haraji:

Koyi yadda zaka biya haraji kuma ka sami Lambar tabbatar da haraji (TIN) don kasuwancinka daga ‘Federal Inland Rebenue Serbice’ (FIRS), kuma ka shirya don bayar da wani abu kowace shekara a matsayin ingantaccen dan kasa.

  1. Bude asusun banki na kasuwanci:

Ka zagaya yankinka ka gano bankunan da suke shirye don ba da rance don farawa ba tare da tantama ba kuma bude asusu a can.

  1. Sayen wayoyin:

Gano yadda zaka sami wadataccen kayan da kake son sayarwa. Don samun damar sayarwa a farashi masu kayatarwa, dole ne ka samo samfuranka daga masana’antun ko kuma kai tsaye ta hanyoyin yanar gizo.

Wanda ya kirkiro kuma ya kera Techno da Infinid dan Nijeriya ne, sannan kuma shi ne mamallakin SLOT, wani sarkar sayar da waya a kauyen Ikeja Lagos, kuma ya bazu ko ina cikin kasar. Lura cewa Techno da Infinid suna aiki akan Android.

  1. Hada da kayan wayoyi:

Shawara ta gaba da za a yanke shine sayar da abubuwa wadanda suke tafiya tare da wayoyi. Lokacin da ke shirin fara kasuwancin, dole ne ka sayar da kayan hade-hade na waya wadanda suka dace da irin wayoyin da kake sayarwa.

  1. Tsara kasuwancinka:

Yayin da kake shirin fara kasuwancin sayar da waya a Nijeriya, ka lura cewa ba tare da sayarwa ba, ba ka da wata harka. Dole ne ka yi kokarin sayar da wayarka. Tallata kasuwancinka yana da matukar muhimmanci.

Zama mai sayarwa mai izini ta wayar salula:

Wata shawarar da zaka iya yankewa akan kasuwancin tallan waya a Nijeriya,shine zama mai sayarwa mai izini. A Nijeriya, manyan masu bada sabis na wayoyin hannu sun hada da Glo Mobile, 9 mobile, Airtel, da MTN.

Bincika tsare-tsaren tallan su, ka fahimci yadda suke aiki, sannan zabi daya sannan ka nemi zama mai sayar da wayar salula mai izini.

Damuwa da tsaro:

Wayoyi abune mai jan hankali kuma babban makami ga barayi, don haka, kare kasuwancinka kuma ka guji sayen tsofaffin wayoyin hannun. Sayi Inshora don samfuranka, da kayan aikinka don kasuwancin.

Fadada kasuwancinka:

Kowane babban kasuwanci ya fara ne da karami, don haka lokacin da kake kimanta zabin ka kan yadda zaka fara kasuwancin sayar da waya a Nijeriya, kar ka manta da tunanin hanyar fadada sabuwar kasuwancin wayarka a nan gaba.

A wannan rubutun, jaridar LEADERSHIP A YAU ta yi bayanin yadda ake fara kasuwancin sayar da waya a Nijeriya. Kun koyi yadda ake fara kasuwancin, inda zaku sayi wayoyin don sake sayarwa, da kuma yadda ake sayar da wayoyin ga kwastomomi. Wadannan abubuwa guda uku sun shafi dukkan kasuwancin sayar da komai a duniya. Ka san matakan da zaka dauka, domin idan ka yi hakan, kana iya fara kasuwancin yanzu.

Exit mobile version