Connect with us

LABARAI

Idan Na Ci Zabe Zan Habaka Harkar Ilimi Da Noma – Aliyu Dandagazau

Published

on

Wani matashin dan siyasa a jihar Gombe mai Neman jam’iyyar Social Democratic Party SDP ta tsayar da shi takarar majalisar wakilai ta tarayya daga yankin Gombe da Kwami da Funakaye Aliyu Inuwa Dan Dagazau yace idan aka zabe shi zai habaka harkar ilimi da Noma.

Aliyu Inuwa Dandagazau ya bayyana hakan ne Jim kadan bayan ya mika fom din sa na takara a sakatariyar jam’iyyar su ta kasa dake Abuja.

Ya kuma yi alkawarin cewa zai ciyar da yankin mazabar sa gaba wajen kawo musu ayyukan raya kasa muddin suka zabe shi.

Sannan sai ya tabbatar da cewa abu na farko da zai fara bai wa kulawa shi ne harkar Noma dan wadata kasa da abinci sannan ilimi dan yakar jahilci, kuma yace zai hada kai da gwamnatin tarayya wajen kara kawo ayyukan ci gaban yankin sa.

Aliyu Inuwa Dandagazau, yace shi dan siyasa ne da bai son ganin matasa suna zaman banza dan haka suma zai samar da shiri na musamman domin su mata kuma za’a fara da tallafa musu da jarin da za su fara jari dan dogaro da Kansu.

Da yake karbar dan takarar shugaban jam’iyyar ta SDP na kasa Mista Olu Falaye, ya bayyana dan takarar da cewa ya cancanta kuma zai iya kawo canjin da al’umma suke bukata a yankin su.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: