Connect with us

Uncategorized

Idan Saboda Allah Ake Yi To Sai A Kame Baki

Published

on

Ba wani sabon bakon abu bane saboda ai wasu daga cikinmu ko ma nace zai yi wuya ace kowa ya tsallake irin wannan tarkon, a halin rayuwar tamu ta yau da kullun , sai dai wani ya fi wani, ko wasu su fi wasu. Wasu sun daina tare da wani, wasu kuwa jiya ma suka fara wani ma ci gaba ne suka samu, al’amari na aikata riya domin kuwa abin ya kasance ma wasu tamkar wata al’ada ce ta rayuwa wadda idan basu yi ta ba, tana iya kasance masu ko ma shi, tamkar idan ba a aikata ba hankali bai kwantawa. Abar ko nace al’adar ta kasance kamar wata masifa ce wadda sai dai mu ce Allah ya kiyaye amin. Amma kuma akwai wani abu wanda wasu sun san babu kyau aikata shi maimakon  ma a samu lada sai a kasance da samun zunubbai, saboda sun bi son zuciyarsu ne wadda dama ita ce jagaba wajen taimakawa ga zuwa halaka. Kada mutane su yi tsammanin ita halakar sai  ance  wani mutum ko  kuma  wasu mutane sun kai ga mutuwa ba, azo ayi shiri na kai su zuwa ga, sababbin gidajen da kowa sai ya shige su, saboda wanda ko wadanda suna  ganin  suna aikata aiki ko ayyuka, kuma masu kyau ne, suna ganin lada  ce suke samu, amma ina zunubi ne saboda ladar tuni sun bar ta wani wuri. A ce kuma kuma kusan a kullun ana samun irin haka kuma maimakon a rika samun da kyau kwarai da gaske, dakyau kwarai, dakyau, zuwa da dama,  sai  dai ta kasance a kuma shiga babi na babu kyau ko kadan, ai wannan an ci baya ke nan, maimakon a doshi zuwa gaba.

Haba ai wannan ba dadi ko kuma ai dai ba dacewa yayi ba, kai ke nan ko kuma ke, ke nan, ba zaku tashi nuna kun yi ko kayi ma wani ko kuma wasu abin kirki ba, ko dai ku bari sai,  kun hadu wani wuri, a can ne kuma, a gaban jama’a sai  kawai kuma a  fara ‘’Kun samu  ko kuma ka  samu sakona , am! Ina nufin wadannan kayan sawar da na aikoma, an kawo maka kuwa? ko kuma kayan abinci, haba na ma tuna shin maganar Masara dana ce a baka da kuma Gero, ina fatan sun  baka’’. Don Allah da Annabinsa minene wannan sai kuma an bari an zo fadar wurin da jama’a suke taruwa, ace nan ne kuma da za a rika  tozarta mutum wato a tona ma shi asiri da kuma nuna shi ba wata tsiya bane, kamar yadda wasu ke cewa, nuna shi ba komai ke gare shi ba, yana daga cikin alfakara’u, a kuma tuna fa wanda ya halicce shi ba fa  ya manta da shi bane, yana  kuma son shi, shi yasa ya halicce shi, watakila ma yafi son shi , fiye da kai, ko ku, har da kuke ganin ku kamar kun fi shi ne, shi yasa Allah ya baka, ko y aba shi,  ku kuna ganin tamkar shafaffu da mai ne, ya fi son ku shi yasa ya baku, shi kuma ko su kuma ya hana masu. Sai kuma Riyar ta biyu wadda a gaban jama’a  ake yi  saboda su gani, nan ne za a kira wanda ko wadanda za a ba, ace su zo wurin, anan ne kuma za a rika mikawa ko wanne daga cikinsu, ana badawa a gaban jama’a saboda dama  ai sune ake son su gani, sun kuma ganin, domin kuwa saboda dasu ne aka yi. Don haka ita ma ladar kada ayi tsammanin za a same ta, idan dai ba a bar wannan mummunan hali na riya ba. Ga kuma wani  abu , wanda sam bai kamata ba, dalili kuwa wani ma  sai ya bari wanda yai ma alkhairin ya wuce sai ya ce,

kaga waccan rigar da wancan mutumin ya sanya, ai nine na bashi ita wallahi, ai kaga tana  da kyaun ko, amma ai ya dace saboda ita rigar bai dade da dinka ta ba.

Da yake yanzu sukuwa ta fara karewa an fara zuwa a gangara ne manufa Azumin watan Ramadan, yanzun ne ake kara kaimi, saboda an ma fara yin Sallar Tu’hajjid, wadda akan fara tane tun ana Azumi na 19, ko kuma 20 saboda kwadayin saduwa da rahamar daren ‘’Lailatul Kadri’’ wanda za a ci gaba da yin hakan har a kai ga zuwa dare na 29 Allah yasa dai mu dace da mafificin al’amari

a rayuwarmu. Idan har saboda Allah ake yi ai sai a samu kame baki, saboda ai shi yana ganin abubuwan ciki dana kuma na waje, babu wani abinda ya gagare shi, ya san zuciyar kowa, don haka kuma wanne irin ilinbo da kuma kinibibi za ayi wanda bai  kai ga sanin su ba.

Ana tasowa daga masallaci kuma sai wasu su manta ma ai daga fa masallaci suke, a kuma shiga yin hirar da bata dace ba, ana yi ana ta yin shewa, musamman ma ace ‘yan mata ne.  Sun manta da cewar bafa su dade da kammala aikin ibada ba, amma kuma gas hi sun shiga wani babi, maganar da ba kamace su ba, a ce an tashi, maimakon a  zarce gida sai kuma a tsaya ana ta gutsiri tsoma da kuma tsugunni tashi. Ba ma a tunawa da cewar daga fa wajen ibada aka taso ana kuma sa ran cikin ikon Allah lada ce za  a samu wadda Allah  kadai ya san ko yaya take, amma kuma kafin a koma gida kuma an tsaya kuma ana neman a samu zunubi, saboda ai duk tatsuniyar gizo zai yi wuya ta wuce ta koki. Ba ama son hannun hagu ya san abinda na dama ya dauka, idan zai yi alkhairi.

‘’Kai ! ya naga ne kana ta hamma ne yau mike faruwa ne? jikani da magana mana, amma bada miyau bafa. Ai baka san wani abu bama. Kallamu ai tuni nake son na baka ka sha, ai jiya nine  na biyu a sahun farko na sallar Tuhajjid na biyu ne, a masallacin kofar Kudu, dana koma gida kuma sai da na yi nafilfili ni ban ma  san iyakarsu ba, kamar ma ba zan iya sake yin barci ba. Namuduka ai ni a sahun baya na zauna barci ya rika dauka ta , saboda nima din shekaranjiya wallahi nayi nafilfili nima , ban san iyakarsu ba’’. Shi kuwa makwabcin naka ai naga shi ko ganin shi ma ba a yi, ya wani boye kan shi, sai kace yana ma jin warin mutane, kyale shi dai shi ai dama haka yake,  tunda wannan watan ya kama bai san  ma ko shigowa cikin mutane ya rika yin sallar jam’i. To Malam Kallamu sai da safe ke nan saboda ni ina so na kara dan runtsawa, haba Namuduka ai sai dai kuma ayi shirin yin sahur, koda yake dai ai sunnah ce a gaggauta buda baki , a kuma jinkirta yin shi sahur din, don haka ni, ina son na samu wannan ladar ta koyi da manzon Allah Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihis Wasallam.To Kallamu sai kuma Allah ya sake hada ni ma watakila zan dan bi shawarar taka ka san ya dace ayi rige -rigen yin ayyukan lada, ba wanda ya san ko mi gobe zata iya haifarwa.

Allah dai ya kiyashemu da nisantar damu da aikata ire iren wadannan munanan ayyuka na cin nama da ma sauran da basu dace ba, saboda idan kayi maganar mutum ba ya nan ai tamkar kaci naman shi ne, sai kuma ace cikin wannan wata mai alfarma har wasu zasu samu lokaci na yin haka. Kuma ya dai kamata mu kara tunawa koda yaushe dukkan aiki yana tare da niyya ne, shi yasa akwai hadisi manzon tsira (SAW) wanda yace ‘’Innamal aamanu bil niyyata wa’innamani’il……..’’. Saboda haka mahaliccinmu  Allah  Sarki ya san komai tun ma kafin a furta shi, zahiri da kuma badini.

 
Advertisement

labarai