Idan Ta Bi Daga-daga Na Kurya Ne Ka Sha Kashi

Buhari

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Haka ne ita wannan maganar take saboda kuwa idan ka ki ka tashi sai a tashe ka, idan kuma ka nuna kai mai yawan jin kasala ne, sai tara maka ita, watakila ma idan baka yi sa’a ba, wani lokacin sai a barka da tsamin jiki, wanda har ya kai ga sawa ma sai an yi maka Tuwon kasa, ana ta yi maka gashi ka kasance tamkar wata  sabuwar Tukunyar da aka yi da Yunbu. Saboda haka ne wanda ya bari har aka bar shi cikin sakon daki wanda idan zai fito sai ya rika cewar don Allah ina son fa na fito, wanda a shi wannan lokacin sai ya gani da kuma jin, ko sauraren abubuwan da hankali ma ba zai yadda da hakan ba, idan mutum ya sake tun farkon fari ya fara nuna cewar shi fa wawa ne ko kuma gaula da sakarai, to hakan ne za a rika kallon shi, ko wanne lokaci koda kuwa ace ya canza daga yadda aka san shi a  kwanakin ko kuma shekaraun baya.

Hakika mun yi sake kwarai da gaske matuka kusan ma wasu daga cikin wadanda muke kallon cewar sune za su iya kare mana hakkin mu, ashe ma sune suke nuna ashe mufa bamu ma isa su kalle mu ba. Ballantana ma wasu daga cikin matsalolin da muke fuskanta har ma wasu lokutta, su kan kasance mana “gawa da maka” wato yadda mutum yake shan zuma a cikin rashin sani ashe ma har da akwai ‘ya’ya a ciki, sune kuma  za su iya cutar da shi gaba. Haka muke yau tamkar yadda wasu suke neman mayar da mu tamkar agololi bayan kuwa mu mun san cewar ai muma, muna da Uwa wadda ta haife mu ‘yan gidan ne bambancin kawai da ake da shi, shi ne Uba daya amma kuma Uwa kowa da ta shi, wadda take kokarin yi mana tarbiyya wadda kuma ko shakka babu tayi iyakar kokarin ta, na matsayin Uwa ta bayar da tarbiyya ta kwarai abar yin koyi koda- wanne lokaci.

A wancan lokacin irin tarbiyyar da aka yi wato yadda shi Maigidan yake yi abin kowa sai ya burge shi, duk kuwa da yake tun ma su ‘ya’yan da aka fara haihuwa basu kai ga yin wayo sosai ba, har su kai ga sanin makama al’amura, sai aka dora su akan tafarki wanda muddin aka bi shi, to daga karshe babu wata maganar yin dana-sani wadda kowa ya san keya ce domin a can baya take. Sannu a hankali har dai shi Maigidan ya kara samun haihuwar wasu ‘ya’yan biyu wato suka koma hudu ke nan, suka kuma kasance cikin hadin kai na ganin sai sun ciyar da shi gidan nasu ya kasance babu wanda ya yi kamar sa, amma kuma kuma fa ba wanda ya manta da dakin su, inda kuma ya san cewar da akwai mahaifiyar sa, duk kokarin da zai yi shi ne sai ya ga kullun rana ta Allah yana faranta mata rai.

Haka ta rika kasancewa har dai su ‘ya’yan suka fara yin wayo suna cewar ashe fa ita tarbiyyar nan da ake koya masu, ba wai saboda ba a son su bane, ana basu dauri ne da kuma tsimi ne saboda a gaba kada su kamu da wasu cututtukan da za su iya yi masu illa. Illar da kuma zata iya yi masu wani babban tabon da zai rika tashi lokaci- zuwa lokaci, mutum ma ya ce kamar cutar sikarin daba a tarbe ta da wuri bace, ko kuma kansa wadda take da wuyar magani. Ko shakka  babu su wadannan ‘ya’yan mutum dayan babu wanda zai ce basu samu tarbiyya ba, ko kadan ba haka bane saboda kuwa masu iya magana sun ce “Ba baiwa Biri ruwa ke da wuya ba, amma dauko shi kwanon bayan an san cewar ya sha ya kuma koshi”, wannan shine babban kuskuren da wasu  daga cikin manyan wani bangaren suka yi inda suka bar mazubin ruwan da suka kai ma shi birin, har dai ga shi yanzu ya ma kasance ko kuma kidimewa ya kasance wani katon Bika wanda ya kan  iya dukan mutum komai karfin sa. Wani abu kuma daban shi ne su wadancan basu bar shi mazubin da suka kai ma nasu Birin ruwan da zai sha tare da shi ba, tsaya suka yi, bayan ya  gama sha suka dauke shi mazubin. Manufa anan  ita ce sai ga shi  wasu daga cikin wadanda muke ganin Shugabannin mu ne, kuma sune din, suna nuna basu  damu ba, amma su wadancan ‘yanuwan  nasu da suke zaman ‘yan Uba, basu manta da irin tarbiyyar da aka basu ba. Rungumar nasu suke yi suna kasancewa tamkar Harshe da kuma Hakori.

Me yasa ne suka rushe babban ginshikin tubalin da ya kasance na hakika ne, suka canza mana gini wanda suka yi da Tubalin Toka, kowa dai ya san yadda take tamkar mutum ya yi tsammanin cewar Tusa tana iya hura wuta ne. Irin ginin da suka yi mana ke nan wanda ga shi yanzu, ma har ya kai ga ya fadi ana ta kallon mu a waje, su kuwa wadancan din basu canza ba daga alkiblar da aka dora su ba, kara gyara ta ma suka yi ta kasance kamar kwangiri karfen jirgi wanda katse shi sai dai makeran asali ko su kuwa sai sun tsafa, kamar dai yadda marigayi Alhaji Mammam Shata Katsina ya fada a wata wakarsa ta Bakandamiya.

Tafa riga ta kare an yi wa mai dami daya sata, tura kuma ta riga ita ma ta kai bango, in ta kuma bi ta daga- daga kamar dai yadda kowa yake ganin yadda shi al’amarin yake tafiya mun san cewar na kurya din shine kan sha duka, mun kuma dade da barin kanmu a can kurya wadda take da nisa, mun kasa fitowa mu nuna muma fa’ya’ya ne ba kuma na Bora ba, ‘ya’yan Mowa ne. Amma sai muka mayar da kan mu wasu agololin da aka auro mahaifiyarsu ta zo gidan mijin da su, saboda dangin mahaifin su daya mutu sun kasa amsa su rike su. Shi yasa yanzu dole ne su yi hakuri da duk irin wulakancin da za ayi masu, wannan al’amari bai dace ace yana tafiya kamar yadda yake tafiya ba cikin halin da ake ciki, ba matukar sake muka yi ba domin mun bari an kwantala ko kuma tsunkula mu sun  kuma  cewar  ashe da akwai jini. Dole ne fa sai an nuna wa kowa iyakar sa, amma kuma mu sai ga shi har  mun bari inda bango ya kai ga tsagewa wasu kadangaru kuma bama kadangare daya ba suka samu wurin shiga, har ginin gidan namu ma nema yake yi ya rugurguje muna kuma ji muna kallo. Idan muka yi tunani tsan da ran mu ai duk sai da yarda wasu daga bangaren namu ko dai Musulmi ko kuma Kirista idan ba, a samu daya daga cikin mu ya kasance Shugaba ba, to ya iya kasancewa matsayin mataimaki, a duk wasu muhimman wurare na harkokin yau da kullun.

Sai dai kuma wani al’amari wanda zan iya cewar kash! har yanzu bamu gane muhimmancin mu ba, wannan ma ga kuma Shugaban kasa daga Arewa, majalisar dattawa dan Arewa shine mai jagoranci, mataimakin kakakin majalisar tarayya, rundunar sojoji ta kasa, rundunar sojoji ta sama, Ministan tsaro, babban mai shari’a na kasa, shugaban Hukumar shige da fici ta kasa, ga kuma na Hukumar kwastan ko kuma ta hana fasa kwauri da dai sauran wasu muhimman wurare ai duk dai ‘yan Arewa ne suke jagorancin wuraren. Amma wani abu shi ne har yanzu bamu iya wani hobbasan da muka yi wanda za mu taimakawa kan mu ba.

Ya dai kamata ace zuwa yanzu mun  kai ga farga mu gane cewar shirin da muke yi ana ta dungurin mu ba zai kai mu ko ina ba, yanzu ne lokacin da zamu dinke mu kasance tsintsiya daya, mu manta da duk wasu bambance- bambance ko mu ceton shi bangaren namu daga rugujewa gaba daya ba. Su kuma shuwagabannin ku kara tunawa idan kun manta ina kara tuna maku cewar Talakawa fa amana ce Allah ya baku idan kuma kuka kai ga yin sakaci da watsi da su za ku sha ta da daci.

Exit mobile version