Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home ADABI

Idan Waka Na Cin Zabe, Mamman Usman Zai Lashe Zaben Kasar Nijer – Kosan Waka

by Muhammad
February 9, 2021
in ADABI
5 min read
Waka
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

MUHAMMADU BUHARI shine da aka fi sani da KOSAN WAKA ko kuma KOSAN MASARI, wanda ya kware wajen yin wakar zambo, wanda kuma ko a shekarar da ta gabata sai da Gwamnatin Jihar Kano ta sa aka kama shi har zuwa gidan maza, saboda wakar da ake zargin ya ci mutuncin mai dakin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Shi dai Kosan Waka an dade ana ganin akwai abinda ya taka, inda ya kasance mawakin jam’iyyar APC a jihar Katsina amma kuma mawakin jam’iyyar PDP a jihar Kano da ma wasu jihohi, to sai dai ya ce shi yana ganin ba wata matsala ba ce hakan. Kwatsam kwanan nan sai aka ji shi ya bulla kasar Nijer, inda yanzu ake kakar siyasa. A can din ya yi wasu wakoki da suke tafasa a wannan lokacin musamman wakar nan da ya yi mai taken ‘‘Yan Nijar Mun Bi Canji’. Wannan waka ana tunanin za ta iya jawo masa matsala kamar yadda ya taba fuskanta a nan Najeriya musamman saboda yadda ya tara mawaka a wakar kuma an yi zambo iya zambo sai dai ya ce wannan ba wata damuwa ba ce, siyasa ce kawai, kuma duk dan siyasa ya san haka.

samndaads

Ga dai tattaunawar da Muhammadu Buhari ya yi da Wakilin LEADERSHIP A YAU, EL-ZAHARADEEN UMAR, domin jin yadda suka tattauna game da wannan waka da ma wasu sauran batutuwa:

 

Wannan lakani ya samo asali ne daga kosai da nake yawan ci tun ina dan karami, tun muna yara saboda yawan cin kosai da wani abu da ya shafi kosan na samu wannan suna.

 

To, ya sa aka juya wannan suna ya koma Kosan Waka?

Abinda yasa na koma kosan waka, shi kosai shine sunan, kosan waka kuma wakar na ke tasa ake ce mani kosan waka, amma sunan shi ne kosai.

 

Tun yaushe ka samu kanka a cikin wannan harka ko sana’a ta waka?

Gaskiya shekaru suna da yawa, saboda tun muna almajiranci, amma ban fara wannan harka gadan-gadan ba sai shekaru bakwai zuwa takwas da suka gabata.

Da wane irin wakoki ka fara, tun farkon fara wakarka?

Na fara ne da wakokin irin na turawa nan da ake kira H hip hop, sai kuma wakokin Yabo daga baya kuma na koma wakokin siyasa.

 

Sunanka ba boyayye bane a harkar waka a arewancin Najeriya, amma sai gashi kuma ka juya akalar wakarka zuwa kasar Nijar inda yanzu kakar siyasa ke kadawa, me ya jawo haka?

A a ban canza akala ba, ba kuma na bar wakoki a Najeriya ba, ina Najeriya kuma ina Nijar saboda kasan shi mawaki kamar dan kasuwa ne, ko ina zaka iya ganinshi, saboda haka ina Najeriya kuma ina kasar Nijar.

 

Shin siyasar kasar ce ta burgeka ko ko uwayen gida ke gareka acan Nijar din da suka bukaci bada gudunmawarka a can?

Eh! Ina da uwayan gida, ina da masoya acan, kuma ba a raina masoya kuma ba a raina ubangida, shi Mamman Usman ubangida na ne, sannan wasu mayan manyan na tare da shi uwayan gidana ne, kuma da na shiga siyasar shi sai na fahimci shi mutumin kirki ne, kuma mutun ne wanda talakawan kasa basa kuka da shi, sannan idan muka yi kira ga jama’a suka zabi wanda ba shi ake so ba, idan muka yi wasa sai mun yi da kyar zamu tsira.

 

A Najeriya ana jinka kana yi wa ‘yan Jam’iyyar PDP waka kuma sai a jika kana yi wa jam’iyyar APC, amma a kasar Nijar sai aka ji ka fadawa ‘yan adawa, menene sirrin wannan?

Shi ne yasa na yi maka bayanin cewa iyayan gidana ne, ko a Najeriyar ma, idan ka lura a sama wadanda nake yi wa waka ba su da yawa, jihata ce dai na rike gwamna na wato Aminu Bello Masari, shi ne babu yadda za a yi a wannan iska mai kadawa na daina yi mashi waka, sannan Nijar da nake adawa, saboda su iyayan gidana ne, kuma mutanen kirki ne.

Ya ka tsinci kanka a lokacin da kake yi wa Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso waka da kuma gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari saboda suna da banbanci siyasa?

Eh! Gaskiya ne, kuma akwai kalubale so sai, amma dai dole hakuri za ayi da mu, akwai masu cewa in bar wancan, wasu sun ce in bar wannan, kasan kowa da ra’ayinsa, don ina wancan ina wannan, ina ganin ba wata matsala ba ce, ta yi wo wata rana ka ga ‘yan siyasar sun hade waje daya, ko na sama ya bi na kasa ko na kasa ya bi na sama su tafi jam’iyya daya.

 

Idan muka koma kasar Nijar ka yi wata waka da ke tafasa a wannan lokaci, mai take “Yan Nijar Mun bi Chanji” wane sako ne ke cikin wannan waka da aka ce ita ce kawai wakar ‘yan siyasa ke saurare a kasar Nijar?

 

Wane fata kake da shi akan wannan waka mai taken “‘Yan Nijar Mun bi Chanji”

To ni dai na san cewa inda waka tana sa a ci zabe, to wannan waka mai taken ‘‘Yan Nijar Mun bi Canji’ ni Muhammadu Buhari Kosai na tabbatar sai Mamman Usman ya ci zaben shugaban kasar Nijar wannan ka rubuta ka ajiye, Insha’Allahu sai haka ta faru nan kusa ba wai sai nesa ba.

 

To mun gode.

Ni ma na gode kwarai da gaske.

SendShareTweetShare
Previous Post

Amfanin Wasu Tsirrai 13 A Jikin Mutum

Next Post

Mai Kula Da Gidan Haya Ya Kashe Dalibi Kan Takaddamar Biyan Kudi

RelatedPosts

Littafin

SHARHIN LITTAFI: Littafin Koyon Salatin Annabi Cikin Sauki

by Muhammad
7 days ago
0

Daga Ibrahim Sheme, SUNA: Salatin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa...

An Karrama Marubuciya Umma Sulaiman Saboda Ayyukan Jinkai

An Karrama Marubuciya Umma Sulaiman Saboda Ayyukan Jinkai

by Sulaiman Ibrahim
3 weeks ago
0

Jajirtacciyar 'yar gwagwarmayar kare mata da kananun yara kuma shugabar...

Fitattun Littattafan Hausa A 2020 (2)

by Muhammad
1 month ago
0

Daga Adamu Yusuf Indabo, Kamar yadda muka faro bayani a...

Next Post

Mai Kula Da Gidan Haya Ya Kashe Dalibi Kan Takaddamar Biyan Kudi

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version