Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

IGP Adamu Zai Garzaya Kotu Bisa Zargin Bada Rashawa Don Tsawaita Wa’adinsa

by Muhammad
February 10, 2021
in LABARAI
1 min read
Rashawa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Rabiu Ali Indabawa,

Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta karyata rahoton da wata kafar yada labarai ta yada a kan IGP Adamu, babban Sufeto Janar na rundunar ‘yan sanda. Jaridar SaharaReporters ta wallafa cewa IGP Adamu ya bayar da cin hancin Naira biliyan 2 domin a kara masa wa’adi.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, Frank Mba, shi ya karyata rahoton tare da sanar da cewa IGP Adamu zai nemi hakkinsa a kotu. “Mohammed Adamu, Sufeto Janar na rundunar ‘yan sanda (IGP), bai biya Naira biliyan 2 domin a tsawaita wa’adin mukaminsa na IGP ba”, a cewar mai magana da yawun rundunar yan sanda na kasa, Frank Mba.

Mba ya bayyana cewa shugaban kasa ne kawai ya ke da alhakin kara wa’adin mukamin IGP, kuma shi din ne ya ga dama ya kara ba wai cin hanci ne aka bayar ba, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Sai dai, IGP Adamu ya damu sahalewar shugaban kasa Muhammadu Buhari na ya ci gaba da aiki na tsawon watanni uku nan gaba, inda kuma daga bisani ne rahotanni suka ci gaba da yawo a kafofin sada zumunta na cewar Adamu ya biya cin hanci ne domin a kara wa’adin mukaminsa.

“Batun cewa wai IGP bai yi bikin kara wa’adin mukamin na sa ba, wannan wani al’amari ne na dama, amma dai muhimmancin kara wa’adin ya rataya ne kan aiki tukuru domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.”

Sifeto Janar na rundunar ya ce rundunar ‘yan sanda a karkashin shugabancinsa ta jajirce wajen inganta tsaron dukiya da rayukan al’umma.

SendShareTweetShare
Previous Post

Ku Shirya Jin Radadin Karin Farashin Fetur –Ministan Mai Ga ’Yan Nijeriya

Next Post

Shugaban NAF Ya Zaburar Da Jami’ansa Kan Fatattakar ’Yan Ta’addan Nijeriya

RelatedPosts

Alkalin Kotun Koli, Ngwuta, Ya Rasu A Abuja

Alkalin Kotun Koli, Ngwuta, Ya Rasu A Abuja

by Sulaiman Ibrahim
17 hours ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim Mai Shari’a Sylvester Ngwuta, alkalin kotun koli...

Tinubu Ya Bukaci Matasa Su Nisanci Bangar Siyasa

by Muhammad
23 hours ago
0

Daga Bello Hamza, Jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya...

E Call

Shirin Kula Da Zirga-zirgar Manyan Motoci Na ‘E-Call’ Zai Kawo Karshen Cunkoso A Tashar Jiragen Ruwan Nijeriya -Hadiza Bala Usman

by Muhammad
24 hours ago
0

By Bello Hamza, An tabbatar wa masu hulda da tashoshin...

Next Post
Shugaban NAF

Shugaban NAF Ya Zaburar Da Jami'ansa Kan Fatattakar ’Yan Ta’addan Nijeriya

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version