Daga Rabiu Ali Indabawa.
Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP, Mohammed Adamu, ya ba da umarnin kame Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, kan umarnin korar wasu Fulani da ke Jihar Oyo. Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da sashen na BBC.
Ya shaida wa BBC Hausa cewa IGP ya ba da umarni ga Kwamishinan ’Yan sanda a Jihar Oyo, Ngozi Onadeko, da ya kamo Mista Igboho ba tare da bata lokaci ba kuma a kawo shi zuwa Abuja. Idan za ku iya tunawa dan gwagwarmayar Yarbawan ya ba da sanarwar kora ga dukkan Fulani saboda zargin satar mutane da yin fashi a Igangan, Karamar Hukumar Ibarapa ta Gabas dake Jihar Oyo.
Bayan sanarwar ta kare a ranar Juma’a, Mista Igboho ya afka wa matsugunan Fulani a garin don korar Sarkin Fulanin, Salihu Abdukadir, da wasu makiyaya da ake zargi da rura wutar tsaro. Matakin na Mista Igboho ya haifar da maganganu daban-daban daga ‘yan Nijeriya, musamman a kafofin sada zumunta.