Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home WASANNI

Iheanacho Yana Son Cigaba Da Taka Leda A Leceister City

by Muhammad
April 1, 2021
in WASANNI
2 min read
Iheanacho
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Dan wasan gaba na Super Eagles ta Nigeriya, Kilechi Iheanacho, ya bayyana cewa babban burinsa shine ci gaba da bugawa kungiyar ta Leceister City wasa har yayi ritaya idan har kungiyar zata bashi dama.

A satin daya gabata ne wasu rahotanni suka bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Leicester City na shirin tsawaita kwantiragin dan wasan tawagar Nigeriya, Kelechi Iheanacho bayan ruwan kwallayen da ya yi mata a wannan kaka ciki har da wadanda ya zura a ragar Manchester United ya yin wasan gab da na kusa da karshen gasar cin kofin FA na bana.

Dan wasan gaban na Najeriya mai shekaru 24 a duniya na shirin shiga watanni sha biyun karshe ne a kwantiragin shekaru 5 da ya kulla da kungiyar ta King Power a shekarar 2017 bayan raba garinsa da kungiyar kwallon kafa ta Manchester city.

A wasanni 12 cikin 15 ne Leicester ta yi amfani da Iheanacho wanda ya zura kwallaye 7 a wasanni 4 na baya-bayan nan da ya doka kuma hakan ne yasa shugabannin kungiyar suke ganin yakamata su kara masa sabuwar yarjejeniya domin ya ci gaba da zama da kungiyar.

Jaridun wasanni a Ingila dai sun ruwaito Brendan Rodgers mai horar da kungiyar kwallon kafar ta Leicester City na bayyana bukatar tsawaita kwantiragin dan wasan wanda ya bayyana a matsayin mai cike da bajinta.

A bangare guda shi kansa Iheanacho ya bayyana cewa a shirye ya ke ya tsawaita kwantiraginsa da tawagar matukar bukatar hakan ta taso sannan  kuma indai kungiyar taga ya cancanta ta ci gaba da zama dashi

“Leceister City babbar kungiya ce wadda take cike da manyan ‘yan wasa da kuma babban mai koyarwa saboda haka ina fatan ci gaba da buga wasa a wannan kungiyar har lokacin da zanyi ritaya daga buga kwallo”

Matukar dai Iheanacho ya amince da sabon kwantiragin kenan zai fara albashim fan dubu 90 kowanne mako banda alawus alawus wanda zai sa ya zama daya daga cikin ‘yan Nigeria masu karbar albashi mai ywa.

Kelechi Iheanacho wanda ya taimaka wa kungiyaar kwallon kafa ta Leicester City samun gurbi a matakin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin FA bayan ya ci mata kwallaye biyu a fafatawar da ta doke Manchester United da ci 3-1 a satin daya gabata ya dai bayyana cewa  zai ci gaba da nuna bajinta har a wasannin da zai wakilci Nigeriya a nan gaba.

Iheanacho ya jefa kwallaye biyu a mintina na 24 da 78, sannan kuma ya taimaka wa Youri Tielemans jefa wata kwallon a minti na 52 hakan yasa jumullar kwallaye tara kenan da dan wasan na Najeriya ya jefa a raga a wasanni tara da ya buga kuma ko a makon da ya gabata sai da ya zura kwallaye uku a ragar Sheffield United.

“Ina fatan ci gaba da nuna hazaka a wasannin da zan wakilci Nigeriya saboda haka dole ne ragowar ‘yan wasa su bayar da hadin kai domin tabbatar da ganin mun samu irin sakamakon da muke bukata” in ji Iheanacho

Karon farko kenan tun shekarar 1982, wato shekaru 39 da Leicester City ke samun gurbi a matakin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin FA kuma yanzu haka Leicester City za ta hadu da Southampton a wasan na dab da na karshe a  filin wasa na Wembley a cikin watan Afrilu mai zuwa, inda ita ma Chelsea za ta hadu da Manchester City.

SendShareTweetShare
Previous Post

NIS Ta Yi Wa Hukumomin Gwamnati Fintikau A Fasahar Sadarwar Zamani –Babandede

Next Post

Messi Yana Son Barcelona Ta Sayo Aguero

RelatedPosts

Ibrahimovic

Za A Iya Dakatar Da Ibrahimovic Shekaru Uku

by Muhammad
17 hours ago
0

Tauraron kungiyar kwallon kafa ta AC Milan, dan asalin kasar...

Europa

Za Mu Iya Lashe Kofin Europa – Arteta

by Muhammad
17 hours ago
0

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya bayyana...

Pillars

Zan Taimakawa Kano Pillars Ta Koma Ta Farko A Gasar Firimiya – Ahmad Musa

by Muhammad
17 hours ago
0

Sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Ahmad...

Next Post
Aguero

Messi Yana Son Barcelona Ta Sayo Aguero

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version