Abba Ibrahim Wada" />

Iker Casillas Ya Yi Ritaya Daga Buga Kwallo

Tsohon mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Iker Casillas, mai shekara 39 ya yi ritaya daga wasan kwallon kafa bayan ya shafe shekara da shekaru yana buga wasa a matakin kungiyoyi dana kasar Sipaniya.

Casillas ya buga wa Real Madrid wasanni 725 a kakar wasa 16 da ya yi a Santiago Bernabeu, inda ya lashe kofin zakarun turai na Champions League guda uku da kofin La Liga na kasar Sipaniya guda biyar.

Ya kuma bayar da gudunmawar da ta kai tawagar kwallon kafar Spaniya ta ci kofin duniya a 2010 da kofin Nahiyar Turai biyu; a 2008 da kuma 2012 duka a lokacin da yake kan ganiyarsa ta babban mai tsraon raga.

Casillas ya koma FC Porto da buga wasa a shekarar 2015, sai dai bai shiga wasan kungiyar ba tun da ya kamu da ciwon bugun zuciya a lokacin atisaye a watan Afirilun shekara ta 2019 inda kuma yasha jinya.

A lokacin da yake jinya an ba shi aikin koci da zai yi tare da masu horas da kungiyar a Yulin 2019 kuma mai tsraon ragar ya buga wasann sau 256 a kungiyar Porto, ya kuma lashe kofin Premier na kasar ta Portugal.

Casillas ya buga wa tawagar Spaniya wasanni 167 tsakanin shekarun 2000 zuwa 2016, kuma Sergio Ramos ne kadai ke da yawan buga wa Spaniya wasa fiye da shi kuma shima sai bayan yayi ritaya daga buga wa kasar wasa.

Real Madrid ta ce Casillas, wanda ya koma Bernabeu da tsare raga a lokacin yana da shekara tara da haihuwa, babu mai tsaron ragar da ya kai shi kwazo a tarihin kungiyar na tsawon shekara 118 da kafuwa.

Cikin watan Fabarairu, Casillas ya bayyana shirinsa na takarar shugaban hukumar kwallon kafar Spaniya, daga baya ya janye sakamakon matsanancin yanayi da kasar ta shiga saboda bullar cutar korona.

An haifi Iker Casillas Fernandez ranar 21 ga watan Mayun 1981 a Mostoles, Spaniya kuma tsohon mai tsaron ragar Real Madrid da Porto ya lashe kyautar mai tsaron raga da babu kamarsa ta IFFHS karo biyar tsakanin 2008 zuwa 2012.

Casillas ya fara kwallo tun yana dan karami kuma a kungiyar da yake kauna Real Madrid tun daga 1990 sannan tun daga nan ya mayar da hankali kan yadda zai zama kwararren mai tsara raga ya dunga sa kwazo, hakan ya sa tawagar Spaniya ta matasa ‘yan shekara 15 ta gayyace shi a 1996, wasa daya kacal ya kama daga nan ya koma ta matasa ‘yan shekara 16.

A nan ne ya nuna kansa da ya sa Real Madrid ta fara amfani da shi a karamar kungiyar wato Real Madrid C sannan a shekarar 1999 ya shiga jerin fitattun ‘yan kwallon Turai 11 na Champions League, kuma ya zama matashin da ya tsare raga mai shekara 18 da wata shida a ranar 15 ga watan Satumba a fafatawa da Olympiakos.

Iker Casillas ya fara buga wa tawagar kwallon kafar Spaniya wasa a watanYunin shekara ta 2000 a karawa da Sweden a wasan da suka tashi 1-1 haka kuma ya fara tsaron ragar Real Madrid a gasar La Liga ranar 18 ga watan Satumbar 1999 a wasan da suka tashi 2-2 da Athletic Bilbao.

Nasarorin Da Ya Samu:

A Real Madrid ya ci kofi 16.

Ya lashe European Cup guda uku da  Kofin Zakarun nahiyoyin duniya, Club World Cups guda uku da  European Super Cup guda biyu da  Spanish La Liga sau biyar da gasar kofin kalubale na  Copa del Rey guda biyu sai kuma  Spanish Super Cup guda hudu sannan a kungiyar Porto dake kasar Portugal ya lashe  Kofin gasar Portugal guda biyu da kuma  Supercup shima na kasar guda daya.

A tawagar kwallon kafar Sipaniya kuwa Casillas ya buga mata wasanni  167 inda ya lashe  kofin duniya daya da Kofin nahiyar Turai biyu sannan sai Kofin duniya na matasa ‘yan kasa da shekara 20

Exit mobile version