Connect with us

LABARAI

Iklisiyyar CAC Ta Yi Kira Da A Gaggauta Kubuto Da Leah

Published

on

Shugaban Cocin, Christ Apostolic Church, na duniya, Fasto Abraham Akinosun, ya yi kira ga shugaba Buhari, da ya yi duk mai yiwuwa na ganin an sako yarinyar nan, Leah Sharibu.

Leah Sharibu, daya ce daga cikin yaran makaranta ‘yan mata 100 da kungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram ta sace a makarantar Sakandaren gwamnati ta, ‘Gobernment Girls Technical and Science College, da ke garin Dapchi, a watan Fabrairu.

Cikin sanarwar da ya fitar ta bakin mai magana da yawun Cocin, Fasto Ade Alawode, a ranar Juma’a, Akinosun, ya bayyana hakan ne a wajen wani babban taron Fasto-Fasto na Cocin da aka yi a shalkwatar Cocin da ke, Ikeji Arakeji, ta Jihar Osun.

Malamin na Cocin ya ce, wa’adin da kungiyar ta deba wa gwamnatin tarayya na gaske ne, don haka ya wajaba gwamnatin ta yi duk sadaukarwan da ya hau kanta na ganin an ceto ran yarinyar.

Ya yi nu ni da cewa, Nijeriya ba za ta iya daukan nauyin wani yakin basasan ba, ya kara da cewa, ba wata sadaukarwar da ta gagara a yi domin ceton ran yarinyar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: