Umar A Hunkuyi" />

Ilimi Garkuwar Dan’adam

Babban Sakataren hukumar bayar da Ilimi ta UBEC, Dakta Hamid Boboyi, a ranar Laraba, ya misalta rashin samun ingantaccen Ilimi a matsayin cuta ma fi girma da ke karya tattalin arzikin kasa, a sashen na ilimin kasar nan. Ya nuna cewa, matsalar tana lalatawa tare da jefa ci gaba da kuma tattalin arzikin kasa a cikin hadari.

Ya fadi hakan ne a wajen wani taron karawa juna sani mai taken, Transparency and Accountability for States Unibersal Basic Education Boards (SUBEB) , a shiyyar kudancin kasarnan, wanda wata cibiya mai suna, ‘Anti-Corruption Academy of Nigeria (ACAN),’ ta shirya a Abuja.

Ya koka da yadda matsalar cin hanci da rashawa suka hana yaran kasar nan samun ilimi mai inganci, inda ya yi nuni da cewa, magance matsalar ta cin hanci da rashawa a fannin na ilimin yaran, hakki ne da ya rataya a kan hukumomin, UBEC da kuma SUBEB.

Shugaban na UBEC, wanda ya nanata cewa, bai halasta masu ruwa da tsaki a wannan sashen su gaza sauke nauyin da aka dora musu ba, ya yi nuni da cewa, matukar dai ana la’akari da kokarin mutane ne ta hanyar magudi, cuwa-cuwa, nuna son kai da cin hanci, tabbas akwai babbar matsala a cikin al’umma.

A cewan sa, cin hanci da karban rashawa a sashen ilimi ya fi cutar da al’umma da yin hakan a sauran sassa, a karkara ne ko a cikin birane, domin kuwa, makaranta ce ke haifar da Shugabannin gobe, cin hanci da rashawa a sashen yana hana samun wadatattun makarantu masu yawa da kuma inganci.

Ya bayyana cewa, a dokar hukumar bayar da ilimin firamare ta UBE, ta shekarar 2004, an yi tanadin bai wa hukumar kashi 2 ne na kudaden daunin da ke shigowa gwamnatin tarayya na CRF, da kuma kamar hakan a Jihohi da kananan Hukumomi da ma sauran wasu cibiyoyin, domin habaka ilimin na Firamare a cikin kasar nan, ya bayyana cewa, domin tabbatar da ana amfani da kudaden bisa ka’ida, hukumar sa ta dauki wasu matakai na duba yadda ake kashe kudaden.

Domin tabbatar da hakan, doka ta 9 (b) ta UBE, ta yi tanadin cewa, ba za mu bai wa kowa karin kudade ba, har sai mun tabbatar da ya kashe wadanda muka ba shi a baya a kan ka’idan da dokar ta tanada, kan haka ne, suka gabatar da duba ayyukan da suka yi a kowane Kwata da sauaran su, domin mu tabbatar da abin da ake yi da kudaden a Jihohi har da Abuja.

Ya ce, “Ilimin Firamare shi ne ginshikin rayuwar yaranmu a gobe. Tilas ne mu tabbatar da mun baiwa yaran namu kyakyawan tushe mai aminci, domin su gina mana ingantacciyan kasa mai aminci.

Mukaddashin Shugaban hukumar ICPC, Dakta Musa Usman Abubakar, ya ce, a kokarin da hukumar ta ICPC, ke yi na ganin an samar da ingantaccen ilimi ne ta shirya yin wani bincike da nazari kan hukumonin, UBEC da SUBEB, a dukkanin kasar nan, a hakan ne ta gano cuwa-cuwa mai yawa a sashen, hakan ne kuma ya kai ta ga shirya taron karawa juna sani a kowace Kwata.

Dakta Abubakar, ya tunatar da mahalarta taron kan babban aikin da aka dora masu, da su nu na dattako wajen sarrafa kudaden da aka ba su domin su gudanar da manyan ayyuka a makarantun na gwamnati, ya kara da cewa, ya wajaba su kasance masu sa ido da kuma nu na halin gaskiya da rikon amana. Buhari: Ba Zan Manta Da ‘Yan

Exit mobile version