Khalid Idris Doya" />

Ilimi Kyauta: Gurguwar Shawarar Kwamishinan Ilimin Bauchi

Kasa da ‘yan watanni da rantsar da sabon kwamishinan ma’aikatar ilimi na jihar Bauchi, Dakta Aliyu Tilde, ya yanke shawarar daukar wata gurguwar shawara ta dakatar da amsar kudaden makaranta daga hannun iyayen dalibai ko dalibai ba tare da samar da makwafin kudaden ba.

Kudaden da makarantu ke amsa a karshen zangon karatu da su ne su ke samun damar gudanar da harkokin gudanar da ilimi a makarantunsu. Ba tare da yin wani tanadi na a zo a gani ba, sabon kwamishinan ilimi ya dakatar da amsar kudaden, wanda daga dukkan alamu hakan zai iya kawo wa harkar koyo da koyarwa tankarda a jihar.

A bisa haka ne wannan nazarin zai bayyana halin da makarantun su ka samu kansu a yau da kuma barazanar da ke akwai.

Irin matakin da Kwamishinan ya dauka ko da kuwa ya na da wani sabon tsari mai nagarta, kamatuwa ya yi ya fara samar da mafita ko hanyoyin magance bukatun da su ka zama tilas gabanin daukar irin wannan matakin.

Bincikenmu ya gano cewar, satin da a ka bude makarantu (a ka dawo daga hutu) na shiga wannan sabon zango na karatu da a ke ciki, wato satin farko da fara ayyukan koyo da koyarwa ilimi, sai sabon kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Aliyu Usman Tilde, ya aika wa dukkan shugabannin makarantu na sakandare (Principals) da Daraktocin ilimi a fadin jihar Bauchi sakon cewar, kada a sake karbar ko kwabo a wajen yara, domin harkar ilimi a makarantun gwamnati a daukacin jihar Bauchi.

Wannan umarni na sabon kwamishinan ilimi na jihar Bauchi ya na kunshe ne a cikin wata takardar umarni ta ranar 23 ga September, 2019, wacce a ka aika wa dukkan ko-odinetocin ilimi na shiyyoyin jihar Bauchi tare da sa hannun Malama Hannatu Iliya, a madadin kwamishina.

Sakon ya na cewa, “Ina sanar da ku cewar, an dakatar da karbar kudade da a ka saba karba a hannu dalibai har illa Masha-Allahu, wadannan kudade da ake magana a kai sun hada har da kudaden jarraba na WAEC da NECO, dadai sauransu,” kamar yadda sanarwar ta zayyana.

Sanarwar ta ce idan kuma an kardi wadansu kudaden makamantan wadanda a ka hanna karba, kafin isowar wannan sako, ya zama wajibi a mayarwa yara kudaden da aka karba daga hannun su ba tare da bata wani lokaci ba. Sanarwar ta ci gaba da cewar, bada jimawa ba, Ma’aikatar ilimi ta jiha zata sanar ire-iren kudaden da makarantu zasu rika karba daga hannun dalibai, kuma da zarar anyi sabon tsari na karban kudade, za a sanarwa dukkan makarantun jihar sabon tsarin.

Wannan sanarwa an yi shi ne domin ya shiga kunnuwan wadanda a ke nufin ya shiga, wato shugabbannin makarantu na gwamnatin jihar, da zumma jagoranci da kuma aiki da sanarwar.

Idan za a iya tunawa dai, kafin zuwan sabon kwamishinan na ilimi, wato Aliyu Usman Tilde, a na karban kudade kimanin naira dari bakwai da hamsin zuwa naira dari takwas (N750 zuwa N800) a daukacin makarantu a jihar Bauchi, a kowani zangon karatu, wato bayan watanni uku-uku (termly). Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi ta jihar, wanda har yanzu shine akan gado, a karkashin jagorancin su ne aka amince da karban wadannan kudade daga dalibai a makarantu, aka kuma aikawa daraktoci da shugabannin makarantu, akan takarda mai lamba kamar haka, MOE/S/EDU.217/B.11 ta ranar goma sha daya ga watan tara na shekara ta dubu biyu da goma sha takwas (11th September, 2018) mai taken ‘UNIFIED SCHOOL CHARGES FOR CONBENTIONAL SCHOOLS’. An kuma fayyace kudaden kamar haka: PTA – N200, Edams (kudaden jarabawa) N150, Games (wasanni) N150, Health (lafiya) N150, G&C N50, Omo, Bleach, Brooms, MSS/FCS N50, wadanda a jimlace suka tasar ma naira dldari bakwai da hamsin (N750). Wadannan kudade, idan an yi la’akari ba suna sayen dukkan kayayyaki da aka zayyana bane, saboda canje-canjen farasi lokacin zuwa lokaci.

Kuma akwai ma wadansu batutuwa da ba a ambata ba, wadanda makarantu ne suke yi da kansu, kamar a wasu lokuta, makarantu ne ke daukar biyan albashi na masu gadi, ko kuma sukan kara yawan masu gadi idan basu wadace su ba, suke kuma biyan kudaden albashi na masu gadi da suka kara.

Akwai kuma batun aike – aike zuwa Ma’aikatar Ilimi ta jiha, ko zuwa da mota ga masu hali, dadai sauran bukatu makamantan wadannan, wadanda duka suna bukatar kashe kudade na zirga-zirga. Kada ka yi maganar allin rubutu akan allo dake cikin ajujuwan karatu, ko babban biro da ake kira ‘marker’ dadai makamantan kayan aiyuka bargaje, dukka makarantun jihar suna dogoro wajen gudanar da mafiya yawan ababen da muka zayyano ne ta hanyar amfani da wadannan kudadan da suke amsa daga hannun dalibai a duk karshen zangon karatu.

Sai ga shi kwatsam an bijiro da wani umarni mai hana karban ire-iren wadannan kudade daga iyayen dalibai a makarantu. Ma’aikatar Ilimi ta kuma yi bayani na cewar, akwai wani sabon tsari na karbar kudude ko akasin haka da zata bijiro da shi. Amma kafin wannan bijirowa, yaya makarantu zasu aiwatar da lamura da suka jibanci kashe kudi ko kudade? Idan zasu karbi aron kudade ko rance daga ina zasu karba, ko kuma za’a jira yin koyo da koyarwa har sai lokacin da ma’aikatar ilimi ta bijiro da sabon tsari da take tutiyar bijirowa? Abin la’akari shine jinkiri na kwana daya, na rashin samun kayayyaki da zasu kasance tagomashi na koyo da koyarwa wani babban nakasu a cikin lamuran bunkasa ilimin dalibai a makarantun mu.

Akwai kuma batun samar da littafai na tsara koyo da koyarwa, wanda ake cewa ‘lesson plan’ da makarantu suke bayarwa, Akwai batun samar da magunguna a makarantu saboda yara, musamman a makarantun kwana, hadi da wani tsari na koyar da dalibai, da ake lakabi da ‘works dairy’. Samar da kayan wanke-wanke kamar Omo na wanke makewayi, da wuraren wanke-wanke, hadi da wuraren dafa abincin dalibai a makarantun kwana. Abubuwa dai suna da tarin yawa wadanda makarantu suke yi na yau da kullum, wadanda kuma ba a gudanar dasu sai da kudade, meye sa kwamishina bai fara tanadar da wadannan gabanin daukar irin wannan matakin nasa ba?.

A binciken da na gudanar a cikin makarantu da dama da suke Bauchi, mun iya gano a wannan zangon karatu da ake ciki, babu kayan aiki, domin ba a yi tanadin sa wa makarantu ba, kuma an ce kada a karbi kudade daga dalibai, don haka babu kayan aiki da za a yi aiki kenan tun lokacin da aka fara zangon na karatu zuwa yau a mafiya yawa daga cikin makarantun. A takaice dai, lamari da ake ganin an kawo tawaya wa koyo da koyarwa, kuma ba a san kowace rana ce Ma’aikatar Ilimi ta jihar zata yanke shawarar abinda za a ba kan wannan lamari. Don haka da zarar dalibi ko dalibai sun rasa kwana daya, biyu ko uku, koma abinda ya fi haka, ilmantarwa ya samu nakasu kenan, kuma za a samu kwanaki ko watanni kafin a cike wannan gibi. Masana dai na ganin tunanin Kwamishinan a matsayin wata tunanin da ba a shawara wajen yanke ta, domin kuwa matakin farko ya dace a tabbatar da samar wa makarantu ababen bukatarsu ne Kafin a kai ga katse amsar kudaden gudanarwa.

Abin jimami da takaici shine kowane mahaluki ya san farashin kowane abu karuwa yake yi, babu rangwame a cikin farashi, kamar yadda hada-hadar kasuwanci na yau da kullum suke bayyanawa. Adai halin da ake ciki yanzu babu magunguna a wasu makarantun, musamman makarantun kwana na dalibai da za a tonyesu da shi idan matsalar rashin lafiya ta taso, kuma babu kudaden sayen su a wajen shugabannin makarantu na jiha.

Idan za a yi la’akari da dokar kasa wacce ke nuni da cewar, makarantun firamare da karamar sakandare su bayar da ilimi kyauta, mafi yawancin makarantu, musamman makarantu masu zaman kansu a halin yanzu suna ta karban kudaden dalibai da ya kai naira dubu daya zuwa dubu biyu da dari biyar (N1, 000 – N2, 500), hadi da makarantun al’umma, suna ta karbar ire-iren wadannan kudade, kuma babu abinda sabon kwamishina yayi dangane da hakan, ba wani hani daga babban sakarare ko ma’aikatar ilimi, suna tacin karnukan su babu babbaka. Kuma babu mamaki ma shi kwamishina bai soke karbar ire-iren wadannan kudade a makarantu masu zaman kansu a yankin Tilden Fulani ba, hadi da tasa makarantar.

Ga alama dai sabon kwamishina bai yi shawara da kowa ba kafin ya yanzu wannan hukunci na rashin karban kudade daga dalibai a makarantun mu. Idan kuwa yayi shawara, da su wanene yayi wannan shawara a matsayinsa na sabon kwamishina?, domin abin lura shine, kafin zuwansa, babban sakatare a ma’aikatar ilimi da mukarraban sa sune suka yanke shawarar karban wadannan kudade, don haka da ya tuntube su za su bashi shawarar da ta dace dangane da wacannan lamura na tafiyar da koyo da koyarwa a makarantun jihar Bauchi.

Ya kamata kwamishina ya koma baya, ya waiwaici jami’ai dake ma’aikatar sa dangane da wadannan lamura, ya tuntubi daraktoci na ma’aikatar, kuma ya nemi shawarar mai girma gwamna kafin daukar ire-iren wadannan matakai. Domin idan aka duba misali da wasu jihohi da suka rungumi aniyar bayar da ilimi kyauta daga firamare zuwa karamar sakandare, sun dauka kwararan matakai kafin su hana karbar kudade daga hannun dalibai. Misalin jihohi da suka sha damarar wannan niyya sune Kano da Kaduna.

Jihar Bauchi dai mun sani gwamnatin ta Ayyana dokar ta baci kan ilimi, Amma ba mu san yaushe ne aka ayyana free education ba, ma’ana bayar da ilimi kyau. Mu kaddara kwamishina na da sabon tsarinsa, ya dace ne ya fara dogoron nazari da bibiyar muhimman ababen can suka dace gabanin zuwa ga wannan matakin. Ko ma a ce, da kwamishina ya fara kokarin samar da ababen gudanarwa da kudaden gudanarwa a makarantun kafin datse amsar kudaden, amma kash.

Misali yanzu, kamar jihar Kano, ta bijiro da tsarin bayar da ilimi kyauta wa makarantun firamare da kananan sakandare tare da tanadin kudade da zata baiwa wadannan makarantu. Jihar ta Kano kafi ta aiwatar da wannan tsari na bayar da ilimi kyauta, saida gwamnatin jihar ta yi bibiyar dukkanin ire-iren matsaloli dake addabar gudanar da koyo da koyarwa a daukacin fadin jihar, ta yi la’akari da dukkun bukatu da suka jibanci koyo da koyarwa, da zummar daukar wadannan nauye-nauye, wadanda a jimlace saida kudade wadannan bukatu suka cimma zunzurun kudade wajen naira biliyan dari biyu da ashirin (N220 billion) a shekara na ire-iren wadannan bukatu na makarantu kafin ta fara aiwatar da shirin a fadin jahar ta Kano. Amma anan jihar Bauchi, wane shiri aka yi dangane da aiwatar da shirin bayar da ilimi kyauta? Amsa babu. Illa dai a baki ko bisa takardun umarci, an ce a daina karban kudade daga daliban makarantu, ba tare da wani sahihin tanadi na aiwatar da tsarin ba. Ai karfe shi kadai baya yin amo, sai an hada da dan-uwansa.

Idan aka yi la’akari da jihar Kaduna, suma nasu tsarin shiryayye ne. Gwamna Nasir E-Rufa’i ne ya bayar da umarni wa daraktoci da sakatarorin shiyya-shiyya na ilimi na daukacin jihar da su gabatar da dukkan ire-iren bukatun su na aiwatar da tsarin bayar da ilimi kyauta a makarantun firamare da kananan sakandare a daukacin fadin jihar ta Kaduna, na kayayyaki da suke bukata, wato ‘Estimates’ na dukkan abubuwa da suke saye. Bayan an gabatar wa gwamnan tanade-tanade na ire-iren wadannan bukatu, ya ga kudaden basu tasar ma naira biliyan guda ba, sai ya cika suka zama naira biliyan guda (N1 billion). Kuma a watan da aka bayar da kudaden wa makarantu, a watan ne aka bada umarni na cewar, kada a sake karban kudade daga hannun daliban makarantu. Yanzu haka ake ta tafiyar da shirin, wadannan misalai sun isa su nuna gaza mazari a Bauchi.

Kuma kafin yanke irin wannan hukunci, akan yi la’akari ne da wasu abubuwa kamar, yawan kudade da suke shigowa jiha na haraji cikin gida, yawan kudade da jiha take samu daga asusun rabo na wata-wata na tarayya, ire-iren nauye-nauye dake kan jiha, dama yadda zata gudanar da tsarin ya dore kamar yadda ake bukatan sa, dadai sauran nazarce-nazarce da suka jibanci kashe-kashen kudade a jiha.

Misali, a karamar hukumar Toro, inda sabon kwamishina ya fito, mu dauka akalla, akwai ‘senior sec. school’ guda goma sha biyar (15) a yankin karamar hukumar, kuma kowace makaranta tana da yara ko dalibai guda dari uku (300). Dangane da haka ne, za a yi la’akari da ire-iren kudade na shirye-shirye da za a bukata na kowane yaro ta fannonin: kudaden kungiyoyin iyaye da malamai a makarantu, kula da lafiya, G/C, MSS/FCS, Omo ko Sanulu, Tsintsiya, Kayayyakin wanke-wanke na makewayi da sauransu, dadai duk makamantan abubuwan bukatu da suka dace. Ire-iren wannan jimloli ne za a yi, wadanda gwamnati zata dauki nauyin su wajen gudanar ko bayar da ilimi kyauta a makarantu.

Alal misali, idan a karamar hukumar Toro, kowane dalibin makaranta zai biya kudi naira dubu daya da dari daya (N1, 100), sai ka hada kudi N1, 100 da yawan dalibai 300 a makaranta guda, tare da jimlace kowace makaranta na makarantu goma sha biyar, misali ka samun jimlar kudade kimanin naira N4, 950, 000 a kowane zangon karatu. Daga wadannan kudade ne makaranta zata saye littafan rubutu, littafan tsare-tsaren tafiyar da koyo da koyarwa, fararen takardu na rubutu, magunguna, tsintsiya, albashin masu gadi, dadai sauran bukatu da zasu kasance tagomashi wa koyo da koyarwa. Wannan misali ne kawai aka tufar domin fahimtar shirye-shirye na gudanar da tsari da ake son cimma, a jihar Bauchi, dama kowace jiha a kasar nan.

Bisa wadannan kididdiga na bukatun koyo da koyarwa, gwamnatin jiha a zangon gamuwa na ilimi, wato shekaru guda kenan (session), zata kashe kudade kimanin N227, 700, 000 wa makarantun sakandare na manyan yara, wato ‘sen. Sec. schools’ wa makarantu dari biyu da talatin (230). Wanann kiyashi banda kudaden ciyarwa na yara, da biyan masu gudanar da WAEC, littafai, kayan kimiyya, da horaswa na malamai. Wadannan kudade ma ya zame wajibi a samo su, domin lamuran ba zasu tafi babu wadannan tanade-tanade ba. Akwai kuma bukatar gudummawar iyayen yara bisa karantar da ‘ya’yansu. Dukkan wadannan sai anyi tanadin su, domin bawai haka kawai rambatse za’a gudanar da lamuran koyo da koyarwa ba.

A cikin wannan hidima, a yanzu haka idan ka ce a sake dawowa baya, a cigaba da biyan ire-iren wadancan kudade da aka hana karbar su a yanzu, yaya mutane zasu kalleka, ko zasu kallaci ma’aikatar ilimi, ko kuma gwamnatin jiha. Za a yi amai a lashe ne?, ko yaya sabon zai kasance, ko gwamnati zata gaggauta sakin kudade domin gudanar da aiyukan koyo da koyarwa.

Don haka, ya zama wajibi gwamnati ta samar da kudade wa makarantun ta na aiwatar da aiyukan koyo da koyarwa. Idan ma kuma aka ce, za a ci-gaba da biyan ire-iren wadancan kudade, babu shakka, akwai alamun sai ma an samu kari akan na baya, la’akari da yawan hauhawar farashi a kasuwanni. Kuma koma dai wane hali ake ciki, ya zama wajibi gwamnati ta himmatu da daukar matakan gaggawa domin ceto makarantun ta daga halin kaka-nikayi na rashin kudaden gudanarwa.

Domin, kusan a halin yanzu, idan ma lamuran tafiyar da makarantu yana garawa, la-budda ko yana tafiya ne a gurgunce, saboda babu kudaden tafiyar da lamura masu yawa a makarantu, kuma daukar matakai na yanzu-yanzu ne zai ceto makarantun daga gurguncewa warwas, la’akari da cewar, jihar Bauchi tana daga cikin jahohi masu koma-baya a lamuran ilimi a kasar nan.

Wani shugaban wata makarantar sakandari a Bauchi da ya bukaci mu sakaye sunansa ya bayyana cewar dakatar da amsar kudaden gudanarwa daga wajen iyayen dalibai, ya janyo musu tarnaki da matsaloli wajen gudanar da harkokin koyo da koyarwa. Matakin da ya misalta a matsayin barazana ga bayar da Ilimi mai nagarta, da neman matakin gaggawa don shawo kan matsalolin da ilimi ke fuskanta.

Kalubalen da ke gaban sabon Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi Malam Tilde lallai suna da gayar yawa.

Exit mobile version