Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTAUNAWA

Ilimi Na Buƙatar Bindiddigi –Kwamared Sabo

by Tayo Adelaja
October 29, 2017
in TATTAUNAWA
11 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

KWAMARED SABO MUHAMMAD Shi ne tsohon Kakakin Gwamnan Bauchi kuma sabon mai baiwa gwamnan jihar Bauchi shawara na musamman a fannin ilimi, a wannan hirar da ya yi da LEADERSHIP A YAU LAHADI ya shaida muhimmacin da ke cikin tashi tsaye ga dukkanin shuwagabanni domin zagayawa cibiyoyin ilimi gami da zaƙulomatsalolin da ilimi ke fuskanta. Ya bayyana cewar sha’anin ilimi na buƙatar bindiddigi da kuma sanya ido sosai. KHALID IDIR DOYA ne ya tattauna da shi, sun kuma taɓo batutuwa sosai musamman ƙalubalen da ilimi ke fuskanta a jihar ta Bauchi. ga hirar kamar haka:

Da wa LEADERSHIP A Yau, Lahadi take tare?

samndaads

Sunana Kwamared Sabo Muhammad mai baiwa gwamnan jihar Bauchi shawara a ɓangaren ilimi.

Kasancewar ba ka jima a wannan muƙamin ba; ka bayyana mana halin da ka zo ka tarar da sha’anin ilimi a jihar?

Uwa-uba ma shi ne babu ofishohin shiyya da za su ke duba halin da sha’anin ilimi ke ciki a faɗin jihar Bauchi, wannan dalilin ne ya sanya jarabarwar ƙarshe na sakandari a alif 2015 ‘yan jihar Bauchi da suka samu kiredit biyar (credit 5) da suka haɗa da Ingilishi da kuma darasin lissafi adadin waɗanda suka ci ba su haura kashi uku da ɗigo shida a cikin biya 3.5 ba; wannan sakaci da sha’anin ilimin da kuma halin ko’in kula da gwamnatocin baya suka nuna a kan sha’anin ilimi ya sa shi gwamnan jihar mai ci yanzu ya yi azama ya tashi ka’in da kuma na’in wajen ganin ya samu nasarar shawo kan dukkanin matsalolin da fannin ilimi ke fuskanta. A bisa himmarsa ne ma har ka ga an fara samun sakamako mai kyau, domin a shekara ta 2016 kashi 17.6 suka ci jarabawarsu na WAEC da NECO, abun nasara a wannan shekarar ta 2017 adadin ɗaliban jihar Bauchi da suka samu maki da kuma darurusan da zai basu zarafin shiga kowace irin jami’a a Nijeriya ya haura zuwa kashi 20.8 ka ga wannan yana nuna maka abubuwan da gwamnatin ke yi ana samun nasara sosai.

Wacce hanyoyi aka bi wajen samun irin waɗannan nasararon da ka bayyana a fannin ilimi?

An samu wannan nasarar ne kuwa bayan da gwamnan ya kafa wata kwamiti a watan Julai 2015 da nufin yin dubiya kan sha’anin ilimi tun daga farko har zuwa ƙarshe domin kwamitin ya kawo shawarorin yanda za a shawo kan matsalar ilimi. A bisa himmantar da wannan kwamitin da gwamnan ya yi, kai tsaye ma ya miƙa ragamar kwamitin a hanun mataimakinsa Injiniya Nuhu Gidado domin a samu sakamako mai kyau, an kuma samu domi ga sakamakon mun fara gani. A rahoton kwamitin nan sun bayyana cewar an yi wa sha’anin ilimi riƙon sakenen kashi wannan ya haifar da lalacewar ilimi fiye da kima.

Wani irin riƙon sakenan kashi kuma ke nan a sashin ilimi, kana nufin ba a karatu ne a gwamnatin baya?

Da babu sakaci ai kwazon ɗalibai da zai ke tafiya yanda ya dace ba kashi uku ba. Misalin da zan ba ka a dukkanin kusan kwasa-kwasai da jami’ar jihar Bauchi ta ke koyarwa ba su da sahalewa daga hukumomin da suke da haƙƙin bayar da wannan sahalewar kamar BTE da NUC da sauransu. Illa dai an basu na wucin gadi, wasu kwasa-kwasan ma basu nemi samun sahalewar ko da ta wucin gadin ne ma. Ɗaya ke nan, na biyu, kwalejin gwamnatin jihar Bauchi Abubakar Tatari Ali ta shafe sama da shekaru 23 tana gudanar da wasu kwasa-kwasai ba tare da sahalewarsu ba; da kuma samar musu da damar yin wasu kwasa-kwasai ɗari bisa ɗari. Sannan akwai makaratundun da suke da buƙatar malamai, sannan su malaman da ake buƙata ana neman a ɗauko su ne daga sauran ma’aikatu na jiha, tun da akwai takunkumin ɗaukan aiki, an tura takardun nan wa gwamnatin baya ba sau ɗaya ba, ba kuma sau biyu ba, babu abun da suka yi. Irin waɗannan sune suka taru suka haifar da cewar akwai ƙarancin jami’in da suke sanya ido kan sha’anin ilimi kama daga matakin sakandari ko manyan makarantu ko kuma ma firamare.

Wannan dalilin ne ya sanya aka kafa kwamiti, kwamitin da ya ba da shawarori ana kuma ci gaba da gudanar da shawarorin nan yanda suka dace. Ya zuwa yanzu za mu iya cewa kwalliya ta na biyan kuɗi sabulu, domin yanzu haka ci gaban ilimi na samun nasara sosai.

Tun bayan lokacin da gwamnan jihar nan ya yi maka sauyin wajen aiki daga Kakakinsa zuwa mai ba shi shawara a fannin ilimi mun ga kana ta zagaye cibiyoyin ilimi ya zuwa yanzu wani sakamako ka iya samowa?

Dalilina na biyu kuma, ba ka yin shirye-shirye sai kana da bayanai a hanunka , bayanai kuma daga ainihin inda matsala take ko abun ya shafa wannan dalilin ne ya sa na samu goyon baya daga shi mai girma gwamnan Bauchi na ke wannan zagayen.

Natijar zagayen da muke yi kuma gaskiya bai misaltuwa. Misalin da zan ba ka akwai AD Rufa’i Collage Legal and Islamic Studies da ke Misau, rabon da wani mai ba da shawara ko kwamishina daga cikin gwamnatin jihar Bauchi ya shiga makarantar kafin ranar da muka je shekara 21 kenan, alhali makarantar tana da shekaru 39 da kafuwa, amma rabon da wani babban jami’i da ya kai kwamishina ko mai ba da shawara ya shiga domin duba sha’anin ilimi shekaru 21 ta yaya za a ƙarfafi masu hidimar koyarwar nan da wannan matakin? Ka ga za su ke yin abun da ransu ya ke so ne kawai. Abu na biyu kuma shi ne mun je kwalejin ilimi na Aminu Saleh rabon da wani gwamna ko na soja ko na siyasa rabon da wani gwamna ya shiga cikin kwalejin shekara 20 sai gwamna M.A Abubakar, ka ga duk irin waɗannan abubuwan su ne suke nuna maka sakaci da riƙon sakenan kashi da gwamnatocin baya suka yi, domin da suna da muhimmanta ilimi ba za su kai irin waɗannan lokutan ba tare da suna duba wacce marhala ilimi ke ciki ba. amma a wannan lokacin malamai da masu gudanarwa na makarantu sun fara sanya wa ransu cewar yanzu akwai iyuwa da ƙarfin guiwar cewar ba mu zo da wasa ba, suna kuma sanya wa ransu cewar matsalar ɓangaren ilimi ya kusa zama tarihi a jihar Bauchi.

Abu na huɗu kuma kan nasarorin da fitar ya iya kawowa shi ne ya tabbatar mana da cewar lallai akwai nasarori da aka samu wanda ku ‘yan jarida ba ku sani ba, duniya ma bata sani ba; haka kuma akwai matsaloli a jibge wanda ku kanku ‘yan jarida ba ku sani ba a makarantunmu, sannan ita kanta gwamnati ba ta sani ba, wannan fitar nawa ya sa ni na iya samosu kuma sannu a hankali ina ta gabatar wa gwamna nasarori da kuma matsalolin da suke jibge domin a samar da hanyoyin magancewa nan take.

Duk inda na je na samu matsala nan take ina yi musu alƙawura guda uku nan take, na farko dai ina yi musu alwashin cewar a shekarar da za mu shiga za mu yi ‘Educational Summit’ wanda za mu tattara dukkanin masu ruwa da tsaki a sha’anin ilimi domin mu zo mu tattauna mu ga yanda ilimin yake da kuma yanda za a kawo gyara da shawarorin da za su kawo karshen matsalar. Ta wannan hanyar ne za mu iya fitar da wata kundi mai ƙunshe da matsalolin da ilimi ke ciki a jiha, matsayar ilimi a jihar, matakan da za ɗauka domin a dawo da martabar ilimi a jihar, kana da kuma matakin da ya kamata gwamnati ta ɗauko domin ganin an samu nasarar cimma muradin da ke akwai.

Abu na biyu, na fahimci cewar akwai matsalar sadarwa a tsakanin cibiyoyin ilimi da ma’aikatar ilimi na jihar da kuma ita kanta gwamnatin jihar Bauchi, a bisa haka ne a wannan maganar da ma da na ke da kai na rigaya na rubuta takarda na neman izini ta hanun shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin jihar domin a bamu zarafin rana guda mu kawo ziyara domin a tattauna kan sha’anin ilimi da shi gwamna. Tattaunawar zai ƙunsi gwamnan jihar, shuwagabanin makarantun ilimi da manyan jami’an da suke aiki a fannonin ilimi a jihar Bauchi. irin wannan zaman ba a taɓa yinsa ba, abu ne kuma mai sauƙi wanda bai ma buƙatar kuɗi amma natijarsa ba a magana domin zai ba da zarafi gwamna ya gansu su ganshi kowa ya tashi ya bayyana matsalolin wurinsa da kuma nasarorin da aka samu. Irin wannan zaman kamar yanda muka tsara za a ke yinsa ne a dukkkanin bayan wata uku aƙalla sau ɗaya, ko kuma sau ɗaya a wata shida. Wannan zai kawo ci gaba sosai ta fuskacin inganta ilimi a tsakanin janibobin da suke aiki kan sha’anin ilimi a jihar.

Sannan abu na uku, na ɗauko shi ne daga cikin rahoton da Injiniya Nuhu Giɗaɗo ya fitar, zuwa ƙarshen shekarar nan indan muka samu amincewa da izinin Allah za mu yi gagarumin taro ƙarshen shekara domin mu karrama malamai da suka yi kwazo a shekara ‘Best Annual Teachers Award’ wanda tun da aka zo gwamnatin demokraɗiyya a jihar Bauchi ba a taɓa yin hakan ba, kuma hakan zai ba da gwarin guiwa da kuma fitar da haziƙan malamai domin inganta musu aiki da kuma ajiye tarihin kwarazan malamai.

A wannan fitar nawa da ne ke yi ina ba da aikin a zaƙulo min irin waɗannan malmai hazikai da suke da ƙoƙari, da kuma ma’aikatan da suke sadaukar da lokacinsu da kansu wa sha’anin ilimi. Gaskiya zagayen da na ke yi an samu nasarori sosai.

Ka bayyana min kaɗan daga cikin matsalolin da ka iya cin karo da su mana?

Matsaloli suna da yawa, amma misalin da zan ba ranar da na je makarantar mata na garin Azare, ziyarar bazata na kai a lokacin da muke tattaunawa da shuwagabanin makarantar sun nuna min wani baba mai gadi mai suna Malam Ali Inuwa, wannan mai gadin tun tantancewar da aka yi na watan ɗaya aka dakatar masa da albashinsa ya daina shiga masa, kuma ya yi ƙoƙarin bi a Bauchi, amma babu safe babu rana mutumin nan bai taɓa fashin aiki ko na rana ɗaya ba. cewa ma ya  ke yi yana da haƙƙi koda kuwa na addini ne ya lura da waɗannan ɗaliba. Mai gadin nan ba yaro bane ya kai kusan shekaru 60 a rayuwarsa. Irin waɗannan idan ba ka fita da kanka ba, ba za iya fahimtar ƙananan matsalolin da suke jibge ba. amma ka ga daga dawowar mu har na fara bibiyar ina ne matsalar albashin wannan bawan Allah ta maƙale. Na je ma’aikatar da ke biyan albashi na ce a yi min cikakken bayanin dalilin tsaida albashin wannan mai gadin tun da ma’aikaci ne wanda aka ɗauka tun 2000 kuma yana aiki sosai, kuma a wajen tantancewar nan dukkanin takardun da suka jibinci aikinsa yana da su. An kuma tsaida masa albashi babu wani dalili a bisa haka ne ni kuma na kama bibiyar shawo kan matsalarsa. Gaskiya mataloli suna da yawa.

Sabo bayan nan kuma me ka iya sake nazartowa ganin cewar akwai matsalar wasu makarantun sun fi wasu makarantun wani abu yaya wannan batun?

Eh to a zagayen da muka yi mun iya fahimtar akwai makaratun da malamai suka musu yawa, wasu makarantun kuma suna da ƙaracin malamai kamar yanda aka fi yawan ji. Ba wai ba a da malamai bane, rashin daidaita tsarin ne, misali yanzu akwai makaranta a cikin garin Bauchi da take da malamai kusan 67 sannan akwai makarantar da suke da malamai kacal guda 5 idan ka haɗa da shi shugaban ƙasa, kuma suna da ɗalibai tun daga matakin aji ɗaya har shida. Malam sai ka tambayi kanka ta yaya ake koyar da waɗanan ɗaliban kuma wani irin sakamako ake son ɗalibin nan su samu?. Sannan idan ka je Azare akwai makaranta na jeka ka dawo dake Maɗangala tana ɗauke da malamai kusan 40 sannan a wannan garin na Azaren akwai kuma wata makaranta wacce ake ƙira Tatari Ali Goɓernment Day Secondary tana da malamai kacal 8 har da shi shugaban makarantar. Sannan akwai makarantar da muka je a Giyaɗe akwai malamai ɗaiɗai har 4 zallan malaman lissafi ne, amma kusan a garin Azare babu malaman lissafi da yawa, ka duba jimawar makarantar mata na Azare amma malamin lissafi ɗaya ne tak.

Fatana a ci gaba da gudanar da al’amuran ilimi yanda ya dace, ya zama akwai wani sanya ido mai zafi da zai ke zaburantar da malamai kan aikinsu, don haka za mu ci gaba da sanya ido da kuma zagaye domin binciken mene ne ke wakana a sha’anin ilimi. Yanzu ƙarfe takwas za ka ga malamai suna rige-rigen shiga cikin aji domin suna fargabar kwamared Sabo zai iya kawo zityarar bazata, domin tun da na zo wannan kujerar daga ni har babban sakatare a wannan ma’aikatar ta ilimi babu wanda ya zauna, haka da sauran dataktocin da muke da su. Na sanya mun ɗauki alkawari wa kawukanmu a ƙalla a kowace sati kowannenmu zai shiga makarantu a faɗin jihar Bauchi a ƙalla sau biyu domin yin dubiya kan mene ne malamai ke gudanarwa.

Ƙalubale na gaba da ke fuskantarmu shi ne mu faɗakar da iyaye su gane cewar suma suna da gagarumin fa’ida wajen inganta ilimi, nan gaba za mu zauna da ƙungiyar iyaye domin ganin yanda za a yi. Domin na zauna da ƙungiyoyi da dama domin ganin ilimi ya ɗaukaka a jihar nan, tun daga kan ƙungiyar malamai, ƙungiyar, ƙungiyar malaman jami’o’I na Gaɗau, da kuma ƙungiyar malamai na kwalejin jinya da gingozoma, na zauna da NUT domin ganin kowa ya kawo ta sa gudunmawra domin mu haɗu mu inganta sha’anin ilimi a jihar Bauchi.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Jami’ar Bamenda Ta Karrama Haziƙan Ɗalibanta A Bauchi

Next Post

Aisha Muhammadu Buhari: Zinariya Ba A Samun Ki A Bola

RelatedPosts

Har Yanzu Babu Sabuwar Kwalta Ko Kwalbati A Garin Giwa – Kwamred Alkurkawee

Har Yanzu Babu Sabuwar Kwalta Ko Kwalbati A Garin Giwa – Kwamred Alkurkawee

by Sulaiman Ibrahim
8 hours ago
0

Daga Idris Umar Game da more romon dimukradiyya da wasu...

Zaman Lafiya

Marasa Son Tabbatuwar Zaman Lafiya A Nijeriya Ke Sukar Furucin Gwamna Bala Kan Fulani, Inji Ladan Salihu

by Muhammad
4 days ago
0

DAKTA LADAN SALIHU Shi ne shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar...

Cigaba

Mun Samar Da Daftarin Cigaba Na Shekara 10 Ne Domin Kafa Harsashin Inganta Rayuwar Gombawa –Gwamna Inuwa

by Muhammad
1 week ago
0

ALHAJI MUHAMMAD INUWA YAHAYA Shine gwamnan jihar Gombe, a wani hira ...

Next Post

Aisha Muhammadu Buhari: Zinariya Ba A Samun Ki A Bola

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version