Daga, Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
An bayyana ilimi a matsayin ƙashin bayan ci-gaba da bunƙasar kowace irin al’umma a doron ƙasa don haka muhimmancinsa ya fi gaban a nanata.
“Duk al’ummar da ba ta bayar da muhimmanci tare da kulawar musamman a sha’anin ilimi to za ta ci-gaba da kasancewa a sahun baya.”
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Farfesa Bello Bada na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo a wajen liyafar musamman ta taya murna ga Dakta Aminu Mode wanda ya samu ci-gaban zama Shehin Malami a fannin Adabin Turanci.
A jawabinsa a matsayin babban baƙo na musamman Alhaji Dakta Ummarun Kwabo (Jarman Sakkwato) wanda Kwamishinan Ma’ikatar Gandun Daji da Lafiyar Dabbobi, Muhammad Tukur Alƙali ya wakilta ya bayyana cewar tun a lokacin Jahiliya Harshen Turanci ya na da matuƙar tasiri ballantana a yanzu da ya zama babban Harshen da duniya bakiɗaya ke amfani.
“Zama Farfesa da Aminu Mode ya yi ba ƙaramar baiwa ba ce wadda ta samu a dalilin sadaukar da kai da jajircewa wajen neman ilimi da yaɗa shi.”
Aminu Mode haifaffen Ƙaramar Hukumar Sakkwato ta Arewa yana ɗaya daga cikin sababban Shehunan Malamai da Hukumar Gudanarwar Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo ta aminta da zamansu a ƙololuwar matsayin na ilimi a makwanni biyu da suka gabata.
Farfesa Mode wanda ya yi digirin farko a 1988, digiri na biyu a 1999 da kuma digiri na uku a 2005 ya riƙe mabambantan muƙamai da dama a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo wadda ya kama aikin koyarwa da ita a 1995.
Daga ciki akwai muƙaman da ya riƙa akwai Mataimakin Shugaban Tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci, Shugaban kula da ɗab’i na jami’ar, mataimakin sakataren ƙungiyar Malamman Jami’a (ASUU) a yanzu haka kuma Farfesa Mode shine Shugaban Sashen Turanci na jami’ar.
Farfesa Mode ya duba ɗalibai sama da 500 a Kundayen kammala digiri na farko, da na biyu da na uku ya kuma wallafa littaffai da dama.
Ɗaya daga cikin ɗaliban Shehin Malamin a Sashen Turanci, Shehu Garba a zantawarsa da LEADERSHIP A Yau ya bayyana cewar Farfesa Aminu Mode ya cancanta da matsayin da ya samu.