Ilimin Kwamfuta: ATAP Da NUJ Za Su Ba ’Yan Jarida 50 Horo

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa reshen jihar Bauchi ta fara ba da horo kan ilimin na’ura mai kwakwalwa da yanda ake iya sarrafa ta ta hanyoyin da suka shafi ɗan jarida da kuma aikin na jarida a wannan zamanin. Wannan horon dai haɗin guiwa ne a tsakanin ƙungiyar ‘yan jaridan da kuma kwalejin kimiyya da fasaha na gwamnatin jihar Bauchi wato (Abubakar Tatari Ali Polytechnic, Bauchi).

Da yake yi wa LEADERSHIP A Yau ƙarin bayani kan shirin, Kwamared Ibrahim Muhammad Malam Goje wanda shi ne shugaban ‘yan jarida na jihar ya bayyana cewar wannan horon sun himmatu ba da shi ne domin cika alkawuran da suka ɗauka a yayin da suke yaƙin neman zaɓe a wajen mambobin ‘yan jaridan “wannan dai wani ci gaba ne ta fuskacin horas da ‘yan jarida na jihar Bauchi wanda ita NUJ ta ƙuduri aniyar yi kamar yanda muka shelanta a lokacin yaƙin neman zaɓe. Kuma shi wannan horaswar na tsawon kwanaki uku ne kamar yanda aka fara a yau talata 31/10/2017 za kuma a kammala a ranar Alhamis 2/10/2017”.

Malam Goje ya ci gaba da cewa abun da wannan tirenin ɗin ya ƙunsa dai shi ne ba da horo na musamman kan ilimin amfani da na’ura mai kwakwalwa wato (computer). Ta bakinsa “abun da wannan horaswar ya ƙunsa dai shi ne mutane hamsin daga cikin ‘yan jaridarmu ne za mu ba su horon nan, kamar yanda muka yi a karo na farko. Horon nan a kan fannonin da suka shafi aikin jarida kai tsaye ne. na farko akwai abun da ya shafi mu’amala kai tsaye da na’ura mai kwakwalwa ta hanyar shiga yanar gizo, na biyu kuma akwai horo na sarrafa na’ura mai kwakwalwar wajen yin rubuce-rubuce sai kuma na uku wajen yin amfani da kwamfuta wajen sarrafa hotuna da sauran fannonin da ake ba da horon domin inganta aikin namu”. A cewarsa

Ya ci gaba da cewa babban abun da suke son cimmawa a irin wannan horo da suke baiwa mambobinsu na ‘yan jarida shi ne domin su laluɓo hanyoyin shawo kan matsalolin da suke jibge a aikin na jarida “irin matsalolin da ake samu ka ga wasu ‘yan jarida suna gudanar da aikin ba tare da ilimin da ya dace ba; muna son ganin an kawo ƙarshen rashin gudanar da aikin nan ba tare da ilimin da ya kamatan ba. za ka samu ɗan jarida a wannan ƙarnin na 21 amma bai iya sarrafa kwamfuta ba, wannan abun kunya ne kuma naƙasu ne mai girma ga shi kansa ɗan jaridan. Muna son su mambobinmu suna da ilimi kan ita na’ura mai kwakwalwa ta yanda za su iya sarrafa ta cikin ƙanƙanin lokaci wannan shi ne abun da muke son mu cimma domin yin aikin da kwamfuta na kawo sauƙi sosai wajen tafiyar da aikin jarida”. In ji Goje

Da yake bayani kan natijar da horon farko ya jawo kuwa, ya bayyana cewar an samu ci gaba sosai ga waɗanda aka basu horon nan a karin farko yana mai cewa natijar ba ma ya misaltuwa “hatta shuwagabanin cibiyoyin ‘yan jaridu sun yi ta kiranmu suna bayyana mana cewar a sakamakon wannan horon sun fara ganin canji a wajen wasu daga cikin ma’aikatansu wannan ka ga ci gaba ne. sannan su kuma waɗanda aka basu horon nan da dama sun yi ta samun yanda za su yi domin shawo kan matsalolin da suke ciki. wasu da dama da aka basu horon nan sun iya fahimtar a da suna shan wahala sosai wajen gudanar da aikinsu a sakamakon basu amfani da ita kwamfuta amma yanzu da suka samu ilimi kan kwamfutar sun koma suna amfani da ita wanda mun ga ci gaba sosai ta fuskancin wannan horon”. Ta bakinsa wannan horaswar dai shi ne karo na biyu, inda aka yi wa ‘yan jarida hamsin horo a karin farko yanzu ga wasu hamsin ɗin suna samun horo kan wannan Ilimin zamanin, baya ga na  za kuma a sake zaƙulo wasu ‘yan jaridar domin horas da su.

Sakatare NUJ na Bauchi Yakubu Lame ya bayyana cewar sun himmatu wajen inganta walwala da kuma jin daɗin mambobinsu a bisa haka ne suke samar da shirye-shirye domin inganta aikin jarida da kuma dawo da martabar aikin a idon duniya yana mai shaida cewar za su ci gaba da fitar da tsare-tsare masu fa’ida domin a samu cimma nasarar da aka sanya a gaba.

Exit mobile version