Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home DAGA BIRNIN SIN

Illa Za Ta Koma Kan Masu Yin Adawa Da Sin

by Sulaiman Ibrahim
March 20, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Illa Za Ta Koma Kan Masu Yin Adawa Da Sin
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga CRI Hausa

Yayin taron watsa labaran da aka shirya a jiya Alhamis a jihar Xinjiang, Gulbostan Rozi, wadda ta zo daga yankin Kashgar na jihar, ta bayyana cikin fushi cewa, “Kamar yadda karin maganar ‘yan kabilar Uygur ya bayyana, idan ka jefa dutse sama, kila ne dutse zai fado a kanka, wato dai mayaudari Adrian Zenz ka kula da kanka, kada dutse ya fado a kanka.”
To, ko wane ne Adrian Zenz? Wasu rukunonin masu adawa da kasar Sin suna kiran wannan ‘dan asalin kasar Jamus mai shekaru 47 da haihuwa da “kwararren mai nazarin harkokin Xinjiang”, amma hakika shi mai baza jita-jita ne kawai kan jihar.
A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, ya kan wallafa wasu rahotanni na adawa da kasar Sin a fadin duniya, inda har ya samu goyon bayan rukunonin masu adawa da kasar Sin, kuma kasancewarsa mamban asusun tunawa da wadanda suka shan wahalhalun kwaminis, wanda Amurkawa masu sassaucin ra’ayi suka kafa, ana iya cewa, yana yin aiki ne na adawa da kasar Sin.
Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, tun daga shekarar 2018, gaba daya Adrian Zenz ya rubuta rahotanni sama da goma, wadanda ke shafawa jihar Xinjiang ta kasar Sin bakin fenti. Ga wasu jimlolin da ya rubuta, “aikin tilastawa” da “tiyatar hana haihuwa da aka tilastawa mata” da “kare al’adu” da “kisan kare dangi”, dukkansu suna tsorata masu karantawa, amma abu mai ban mamaki shi ne, wannan masanin batun Xinjiang bai taba zuwa jihar ba ko sau daya.
Yanzu haka mazauna jihar Xinjiang na fadin gaskiyar ainihin yanayin da suke ciki, inda jami’ai, da wakilan bangaren addini, da fararen hula na jihar, suka karyata rahotanin karya da Adrian Zenz ya rubuta, yayin taron watsa labarai da aka shirya.
Migit Timit, mai noman auduga a jihar Xinjiang, ya bayyana cewa, “Muna noman auduga a gonakinmu, kuma mun samu kudin shiga daga aikin, shin ina dalilin da ya sa za a kira aikinmu aikin tilastawa?”
Rahotannin sun nuna cewa, wasu kamfanoni da mazauna na jihar Xinjiang, sun riga sun kai Adrian Zenz kara a kotu, domin kiyaye kima da moriyarsu. Ko shakka babu, za a hukunta Adrian Zenz bisa doka, da rukunonin dake adawa da kasar Sin, wadanda ke goyon bayansa. (Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

SendShareTweetShare
Previous Post

Yang Jiechi Da Wang Yi Sun Bayyana Matsayin Kasar Sin A Yayin Taron Tattaunawa Tsakaninsu Da Na Amurka

Next Post

Shin Tattaunawa Tsakanin Manyan Jami’an Sin da Amurka Za Ta Kyautata Dangantakar Kasashen Biyu?

RelatedPosts

Bai Kamata A Fake Da Batun Tinkarar Sauyin Yanayi Don Neman Cimma Muradun Siyasa Ba

Bai Kamata A Fake Da Batun Tinkarar Sauyin Yanayi Don Neman Cimma Muradun Siyasa Ba

by Sulaiman Ibrahim
3 hours ago
0

Daga CRI Hausa Kwanan nan ne a wajen taron kolin...

Jami’in MDD A Sin: Na Ganewa Idona Yadda Kasar Sin Ta Kawo Sauyi Ga Nahiyar Afirka

Jami’in MDD A Sin: Na Ganewa Idona Yadda Kasar Sin Ta Kawo Sauyi Ga Nahiyar Afirka

by Sulaiman Ibrahim
3 hours ago
0

Daga CRI Hausa Yau Lahadi, babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya...

Sanawar Amurka Kan Yankin Hong Kong Za Ta Taimakawa Masu Barna Wajen Kara Aikata Laifuka

Sanawar Amurka Kan Yankin Hong Kong Za Ta Taimakawa Masu Barna Wajen Kara Aikata Laifuka

by Sulaiman Ibrahim
4 hours ago
0

Daga CRI Hausa Kwanan nan ne Amurka ta fitar da...

Next Post
Shin Tattaunawa Tsakanin Manyan Jami’an Sin da Amurka Za Ta Kyautata Dangantakar Kasashen Biyu?

Shin Tattaunawa Tsakanin Manyan Jami’an Sin da Amurka Za Ta Kyautata Dangantakar Kasashen Biyu?

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version