Daga Sagir Abubakar, Katsina
Ƙungiyar mata yan jarida reshen jihar Katsina ta shirya wani taron wayar da kan jama’a dangane da illar fyaɗe a shiyyar Daura.
An shirya gangamin ne domin faɗakar da jama’a haɗarin dake tattare da yiwa mata fyaɗe.
Da take jawabi wakiliyar ɓangaren lafiya na ƙungiyar Haj. Binta Husaini Dustinma ta danganata fyaɗe da cewar abune da ake yi dagaryan kuwa da wata manufa.
A wasu ɓangaren wakiliyar Hukumar Yan Sanda da kuma na ma’aikatar shari’a Mrs Martha Papka da Aisha Abba sunyi jawabi kan tanadin da hukumar tayi kan abinda ya shafi fyaɗe.
Kamar yadda sukace kundin tsarin mulkin ƙasar nan yayi tanadin hukunci ga waɗanda aka samu da aikata laifin.
Da take tsokaci shugabar ƙungiyar Haj. Hauwa Elladan ta bayyana godiya ga gwamnatin Aminu Bello Masari dangane da goyon baya da tallafin da yake baiwa ƙungiyar.