Iyami Jalo Turaki" />

Illar Gasa A Tsakanin Mata

Mata da yawa kan shiga matsala saboda dora wa kai abin da wata ta yi nima sai  na yi, wanda haka ba daidai ba ne. Ko su tursasa miji sai ya yi mu su abu alhali karfinsa bai kai ba wanda dalilin haka har a yi ta samun tangarda a zamantakewa wani lokaci har mutuwar aure ya ke jawowa. Mata su sani cewa a rayuwa komai da lokacinsa, idan Allah Ya kawo lokaci sai ku ga komai ya zo da sauki. A dalilin sakawa zuciya wance ta canda kayan daki ni ma sai na canda ya jawowa wasu zaman gidan yari, barin gidajensu saboda ma su bin su bashi, to ina amfanin wannan canji?

 

Mu rinka kallon abin da mu ke da shi sai mu duba mu gani mun fi wasu, kalilan din da ki ke da shi ki ke rainawa wata nemansa ta ke yi, saboda haka har kullum a rayuwa kar mace ta kalli ta samanta domin shi ke wahalar da yawan mata. Ko ki ce mijin wance ya canda mata mota ni ma nawa mijin dole sai ya canda min, daga haka a je a afkawa matsala. Kada mu tursasa miji yin abin da aikinsa  bai kai ba don kawai wata kawa ko makwabciya ta yi shi. Idan kiga wata tayi wani abu da shine daidai karfinta ya kuma burge ki har ya baki sha’awar mallakarsa, to ki yi mata murna da fatan alheri a kan abin sannan kiyi wa kanki addu’ar ke ma Allah Ya baki kamarsa ko wanda ya fito shi amma ba ki sa rai lallai dole sai kin same shi ba ko miji sai ya yi miki ba.

 

Mafi aksari mata wasu ko atamfa ta gani wurin wata sai ta ce itama sai ta samu kamar ta, ko an sayawa yara kaya ko kayan wasa sai mace ta ce ita ma dole ta samarwa yaranta kamar su, anan mu sa ni yatsun hannu fa ba daya ba ne, sannan dole akwai mai wadata akwai wanda ba shi da shi mu daina tursasa zuciyar mu sai mun mallaki abin da mu ka san ba mu da halin samunsa ko miji bai da halin samar da abin. Akwai takaici ne a samu mace da ta ke uwa a gidan maza ko kotu saboda ta shiga matsala akan kudi ta dalilin wance tayi nima sai nayi.

 

Matsalolin Da Ke  Biyo Baya :

 1. Ya na haifar da zubewar mutunci a idon mutanen da ku ke tare.

2n Ya na ragewa mace daraja a wurin miji.

 1. Ya na haifar da lalacewar tarbiyyar yara ta yadda uwa ba ta da lokacin kula da yaranta.
 2. Ya na jawo rashin nutsuwa da kwanciyar hankali.
 3. Ita kanta ya na jawo mata fadawa wani hali kamar sata, zina don kawai ta samu abin da ta ke so ko ta wani hali.
 4. Ya na haifar da mutuwar aure.
 5. Ya na hana mace samun wani miji ta aura.

Da sauransu.

 

Mafita:

 1. Mata su daina kai kansu in da Allah bai kai su ba.
 2. Su zama ma su wadatar zuci da godiyar Allah.
 3. Har kullum su rinka duba na kasansu
 4. Kar su kalli yadda rayuwar wata ya ke balle su kwadaitu a kai.
 5. A kullum su ringa duba kan su da rayuwarsu wadata a kan hakan sai su samu kwanciyar hankali.

 

Shawara

Mata su tsaya su kula da kansu da abin da Allah ya hore mu su sai su zama abin koyi cikin al’umma, domin abin da duk mace ta yi haka yaranta za su tashi da shi.

Exit mobile version