Illar Zargi A Tsakanin Ma’aurata

Zargi

Tsokacin yau zai yi duba ne game da Zargi tsakanin ma’aurata, wasu ma’auratan na kasancewa cikin Zargin juna ko kuma daya daga ciki ya zamo yana yawaita zargin dayan wanda in aka yi buncike aka duba sai a gano abinda ake yawan zargin nan sam ba haka bane. Toh shi dai zargi yana haifar da abubuwa da dama wanda suke hana zaman lafiya tsakanin ma’aurata wanda shi daman aure in akwai zargi cikinsa baya karko bare ya dore, dan baya yuwuwa.

Mafi yawan masu zargi na yin duba ne da abinda zuciyarsu ta raya kawai, ba wai dan sun tabbatar da abinda suke zargi ba ne. Wani lokacin kuma akan samu akasin faruwar wani abu daban wanda ba shi da alaka da zargin da ake ganin afkuwar al’amarin sai zargi ya bayyana nan take ba tare da an tabbatar da gaskiyar lamarin ba. Zargi na kawo dana sani sosai musamman lokacin da ba a bukatar hakan ya kasance. Wani lokacin kuma ta gefe guda ake samun wadanda suke saka wannan zargin cikin zuciyar daya daga cikin ma’auratan, dan ganin an rusa rayuwar zamantakewar aurensu.

Wani lokacin kuma Zargin ya kan yi dai-dai ga wanda ake zargin ta yadda rayuwarsa take canjawa ba tare da shi ma ya sani ba.  Akwai abubuwa daban-daban da Zargi ke haifarwa da kuma dalilin da ke jawo zargin. Yana da kyau ma’aurata su kasance masu zama da juna da zuciya daya ba tare da kokwanton dayan cikinsu ba, bada yarda ga juna na magance yawan zargi, bawa juna kulawa ta yadda kowanne zai rinka marmarin juna shima na magance wannan matsala ta zargi, sai kuma batun hakuri a rinka kai zuciya nesa ta yadda ko da zuciya ta raya za a yi sauri a kawar da abinda take kokarin sakawa. Rashin sauraron jita-jita daga wajen wasu mutane daban na magance wannan matsala dan muddin wani zai kawo suka daga gefe dole ne a fara zargi, akwai abubuwa da dama wanda suke magance yawan Zargin. Aishat Musa Yankara ta bayyana nata ra’ayin game da abinda ya ke jawo zargi tsakanin ma’aurata ta kuma bawa ma’auratan shawara dan magance wannan matsala ga kuma bayanin nata kamar haka:

Aisha Musa Yankara:

To a zahirin gaskiya babu abinda zance ga Maza masu zargi ban da Allah ya shirye su, dalili kuwa shi ne mafi akasarin namijin da kika ga yana zargin matarshi wajan aikata wani abu wanda bai kamataba hakika shima cikin biyu dole a samu daya ko dai ke Matar kin aikata abinda ya kawo wannan silar zargin ko kuma Shi mijin yana aikata abinda yake zargin kina aikatawa, wanda hakan babbar illace a rayuwar aure kai ba ma aure ba a yanayin zamantakewa babbar matsala ne. Shi zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya, Allah ya sa mu dace ya yi mana Jagora a dukkan al’amuranmu ameen. Abinda ke kawo yawon zargi ga Maza shi ne rashin fahimtar juna, da kuma rashin sanin darajar juna, da kuma rashin yarda da juna rashin sanin halayyar juna, tun kafin aure duk da dai mutum kan iya canja hali sai dai idan har an san wadannan abubuwan da na lissafa tsakanin ma’aurata za a samu maslaha ta yadda ko da wata nagana ta zargi ta shigo tsakaninsu za su tsaya su fahimci juna har su magance abin ba tare da wani ko wata sun jiba. Babbar matsalar da zargi ke jawowa shi ne jashe aure daga lokacin da miji ya fara zargin matarshi hakika babu su babu zaman lafiya, shi mijin ba zai taba yarda da macen ba ya yin da ita macen ba za ta rika kallonshi da kima ba saboda wannan furucin daya furta mata hakika ko mace na aikata abinda mijinta ke zarginta dashi Idan har zai rika furta mata kalmar ina zarginki ba za ta kara ganin kimarshi ba a idonta sannan kai maigida idan babu rami me ya kawo rami ni kam? Allah yasa mu dace ya shiryi masu yi ya kuma kare mana imaninmu da zuciyoyinmu amin.

Shawarata ga maza a matsayinka na magidanci ya kamata a ce ka san wacece matarka menene za ta aikata menene ba za ta aikata ba, Koda a ce maka aka yi wance na ka za, kai a matsayinka  na makusanci a gareta akwai hanyoyi da dama wadanda za ka yi bincike domin tabbatar da abinda aka fada maka ba wai ka dinga yarda da maganar wasu makauta ko yara ba, wannan sam bai dace ba hasalima kanka za ka jawa zargi saboda babu yadda za a yi daga zama waje daya da mutum ya kawo maka maganar matarka ba tare da ka bincikeshi dalilin da yasa ya sakawa matarka ido ba, sai dai kuma Idan kaine ka saka su gadinta saboda rashin yardar da ka yi mata mu gyara muna da diya muna da iyaye muna da mata dukkansu matane Ya ya za ka ji a rayuwanka Idan har aka aikatawa yarinyarka kwatankwacin abinda ka aikatawa yar wani mu sowa dan uwan mu abinda muke  so ma kanmu Allah ya yi mana jagora yasa masu wannan hali na zargi su dena Amin.

Exit mobile version