Illolin Bara Da Roko A Cikin Al’ummah

Daga Usman Umar Assakafiy (Gombe)

Da sunan Allah…
Roko kalma ce ta Hausa da za mu iya fassara ta da nema ko neman tallafi wanda shi ne mutum ya nemi tallafawar wani mutum da kudi ne ko abinci ko kayan masarufi ko kayan sawa (sutura) da sauransu. Harkar bara ta kasance da tsohon tarihi kowace al’umma ko addini ko wasu gungu na masana suna da iya abun da za su iya hasashe game da harkar bara ko barace-barace.
Idan muka ƙara nazari a irin karnin takwas na miladiyya za mu riski harkar bara ba ta zamto baƙuwa ba, musamman a yankin gabas ta tsakiya lokacin bayyanar addinin musulunci wanda rubutattun kundi na tarihi ta hakaito mana wannan al’adar duk dama sashin addinin musulunci tun farkon bayyanarsa ya aibanta harkar barace-barace ya kuma kwadaitar a kan dogaro da kai, da falalolin bayar da tallafi ga wanda yake bukatarta.
Kasantuwar ba manufata bace a wannan nazarin na bayyana matsayin barace-barace a gurin ma’abota wata fahimta ba, manufata ita ce in bayyana yadda nake kallon harkar bara da kuma yadda take rusa al’ummah da kuma yadda na hangi yadda na hangi yadda za’a magance matsalar.
Matsayin Bara A Gurin Jama’ar Nijeriya
Harkar bara tana iya zamowa laruri ga wasu ɗaidaikun mutane daga jama’armu ta yadda wani bala’i ko wata annoba za ta faruwa da wani mutum ta yadda ba shi da wata hanyar tsira da mutumcinsa koma bayan ya yi bara ta hanyar rokon mutane, a abun da ya rasa.
Amma a wannan al’ummar tamu,sai harkar ta nemi gindin zama ta zauna saboda wanda ya cancanci barace-barace ya yi wanda ma bai cancanta ba shi ma ya yi wanda hakan yakansa wanda yake ganin zai iya taimakawa mai son taimakon mutane ya fasa saboda shigar ƴan cuwa-cuwa a lamarin.
Harkar ta zama ruwan dare a wannan al’umma ta yadda za ka samu yara ƙkanana ana kaisu almajirancin barace-barace da sunan karatun addini sai rayuwarsu gaba ɗdaya ta canja daga abun daya kawo su ta yadda za su manta manufar turo su wannan karatu ɗin sai su ɓbuge da barace-barace idan ma ba’ayi sa’a ba sai su iya afkawa harkar da za ta iya zamowa barazana ga al’umma saboda ganin yadda al’ummarsa bata damu da rayuwarsa ba.
Wasu kuma suna turo yaransu zuwa karatu ta hanyar barace-barace saboda ragewa kai wahalhalun na yawan iyalai, wato kamar mutum ya haifi yara masu yawa da yasan cewa shi ba zai iya ɗdaukar nauyin su ba, hakan sai ta sa ya sa su bara dan nemawa kansu abun da za suci ko kuma ya turasu wata karkara ko wani gari da sunan karatun addini ba tare da ya waiwaye su dan sanin halin da suke ciki ba.
Ana samun wasu ma da ransu da lafiyarsu sai suje a rubuta musu katin asibiti na magani na ƙkarya ko kuma su nemo katin ta hanyar da bata halasta ba suna yawo da wannan katin don neman tallafi na kudin da zai sayi magani, ko kuma ma ka ga wani yana amfani da wata cuta da Allah ya ɗora masa yana yawon barace-barace da sunan neman magani wanin kan ma da kansa kullum yake zuwa ana wanke masa ciwo saboda ya zamo kamar ɗdanye ta yadda idan wani ya gani zaiji tausayin halin da yake ciki ya ba shi wani abu.
Wani lafiyansa ƙkalau amma sai yana yawo yana ƙkarya kala dabam-daban dan abashi kudi, wanda idan kuma kayi nazarin wannan mutumin sai ka ga ba wani irin aiki na ƙkarfi da ba zai iya ba.
Bazance duka ba amma mafiya yawan mabaratan nan ƴ’yan shaye-shaye ne wadanda zuciyarsu ta mutu suka bi wannan hanyar da suke tsammanin mafita ce.
Yadda Harkar Barace-Barace Take Ruguza Al’ummah
Harkar bara ko barace-barace tana karya zuciyar matasa wanda hakan shi zai kai ga rugujewarta ta fuskoki da dama daga ciki:
(1) BARA TANA HANA DOGARO DA KAI:
Muddin mutum ya fara bara ya kuma fara samun abun da yake so takan sa mutum ya dogara da barace-barace dan biyawa kansa bukatun yau da kullum wanda hakan zai janyo asarar mutumin da ya dace ya dogara da kansa dan taimakon al’umma wanda rasa shi kuma zai sa al’umma ta shiga wani yanayi.
(2) BARA TANA DAƘTOSHE BASIRA:
Zaka iya samun mutum mai hazakaƙa wajen ilimin ƙkirkira ko aiki ƙkarfin wanda idan mutum ya tsaya ya yi amfani da wannan basirar tasa zaici gaba kuma al’umma za tayi alfahari da shi, idan kuma har ya lalata basirar tasa tare da yin tsammanin samun wani ba ga wanda zai zo ya taimake shi, wannan ya yi illah.
(3) ROKO YANA HANA YIN SANA’A:
kaidace ta zaman takewar mutane cewa duk wanda ya dogara da barace-barace da rokon abun hannun mutane to, wannan mutumin ba zai iya nitsuwa ya kama wata sana’a ba, saboda zai ci gaba da rayuwa ne cikin zaton zai samu biyan bukata muddin wancan da wancan suna bashi.
(4) BARA TANA GADAR DA TALAUCI:
Talauci shi ne shiga halin fatara na abun rayuwa da kowani ɗdan adam yake bukata domin ya rayu shi wanda yake bara daman da wahala ya iya tara abun da yake samu musamman ma irin nau’in barace-barace da muke gani ana yi a arewacin Nijeriya, sai ka ga mutum kullum a tsiyace bayan kuma Allah ya bashi ƙkarfi wani kuma Allah ya bashi fasahar yadda zai iya tsara mutum ya bashi kudi, to ɗdan uwana mai karatu meye tsammaninka da wannan mutumin ya yi amfani da ɗdaya daga cikin ni’imomin da aka masa wajen neman abinci? Ni kam bana tsammanin zai wanzu cikin talauci da fatara.
(5) ROKO TANA HAIFAR DA TA’ADDANCI:
A dabi’ar rayuwar mutum koma waye yana son kyautatawa a rayuwa ko wanda baya roko ko barace-barace, dan haka nake ganin muddin mutum mai lafiya da basira ya dogara da barace-barace kuma ya zamto baya samun abun da yake so, zai iya jin rashin tausayin wannan al’ummar da yake rayuwa a cikin ta, daga nan zai iya ƙkokari na kowani irin yunkuri wajen neman abinci ta kowace mummunar hanƴa wanda wannan hanyar ko da ta’addanci ne.
Allah Ya Sauke.
YADDA ZAMU MAGANCE HARKAR BARACE-BARACE DA ROkO
Akwai hanyoyin da dama da na iya riska duk da nasan jama’a zasu iya risko sama da abubuwan da na hanga waɗanda sune:
(1) Wayar da al’umma akan hadarin dogara da wani ko wasu mutane.
(2) Ka/ki yi kokarin nunawa mai bara ko roko muhimmanci dogaro da kai.
(3) Taimakawa wadanda suke bukatar taimako ta zahiri, ba wanda zai ƙroke ka baka san shi ba ya yi ta maka kukan larura.
(4) Biyan hakkinsu daga zarar sun gama aiki a bisa yadda kuka tsara ko kuma tsarin da aka saba biyansu.
(5) Nazari akan nauyin iyalai da mutum zai iya ɗdaukar nauyin su, wannan zai taimaka wajen rage barace-barace a cikin al’ummah.
(6) Hukumomi da malaman Addini su yi nazari wajen sauya tsarin makarantun islamiyya ta yanayin da ba sai anyi baran abinci ba.
Idan har mun tsaya mun nazarci wadannan abubuwan al’ummarmu za ta fuskanci gobe mai kyau, saɓanin hakan kuma Allah ya Sauke mana,ya tausayawa al’ummarmu.

Exit mobile version