Yusuf Shuaibu" />

Illolin Da Ke Tattare Da Fadawar Matasa Rikece-rikicen Siyasa

Cikin wannan mako, rikici ya barke lokacin da jam’iyyar APC take gudanar da gangamin siyasa a jihar Legas, inda aka bayyana cewa rayuka da dama sun salwanta. Idan za a iya tunawa a baya mun yi kira ga matasa a kan illolin da ke tattare da fadawa hannun ‘yan siyasar da basu da manufa mai kyau, suna amfani ne da matasa kuma da zarar sun cimma burinsu sai su juya musu baya. Wajibi ne matasa su yi tunani.
A cikin watan Fabrairun shekarar 2019 za a yi babb an zabe, ‘yan siyasa sun fara daukan damara ta inda kota hadin yaya sai sun samu nasara, sun fara yin al’adar da suka saba wajen daukar hayar matasa maza da mata tare da basu makamai da kuma kayayyakin maye domin gudanar da rikici da rashin jituwa wajen kokarin sai sun kai ga karagar mulki. A wasu lokuta, ‘yan kunyoyin asiri sukan bayyanar da kansu wajen tada hankali gun zabe. Wannan lamari yana ci gaba da kamari duk da irin yadda ake musu wa’azi game da yin rikici da kuma kalamun da su dace ba wajen neman mukaman siyasa. Kafin hanzu, suna amfani da irin wannan mutane a siyasa a boye ne, sannan su barshi a tsakanin su. A wancen lokaci, ana yin hayar ‘yan barandar siyasa ne daga tashar mota da kan haya inda ake shaye-shaye da kuma sauran wurare da ake saida kwaya. Amma lamarin ya canza a halin yanzu. A yau, suna kewaye ne da maigidansu a matsayin matemakinsa ba tare da kayyade matsayinsu ba. Suna amfani da ‘yan barandar siyasa domin yin farmaki, kashe-kashe, rikici da kuma wajen karya doka da oda lokacin zabe ko kuma bayan zabe. Irin wadannan ‘yan siyasan suna baiwa wannan matasa tukwici na wajin gadi. A cikin kwanan nan ne hukumar kidaddiga ta Nijeriya, ta bayyana cewa rashin aikin yi ya tashi daga miliyan 1.9 zuwa 9.9 a cikin kwatan shekarar 2015. Amma a cikin shekarar 2017 kuma, kididdigan ya nuna cewa, matasan da basu da aikin yi a Nijeriya sun kai kashe 13.41 cikin dari. Ciyar da kansu ma ya zama musu tashin hankali, yawan matasan da basu da aikin yi yana nuna alamar cewa babu aminci a cikin jihohi, saboda haka ake samun rikice-rikice. Wasu daga cikinsu, shi ya sa suka addabi al’umma.
Kafin samun ‘yancin kai da kuma bayan samun ‘yanci kai lokacin zuwan dimokradiyya cikin wannan kasa, a baya, rikici baya cikin siyasar Nijeriya musamman wajen satar akwatin zabe. Tsarin yana nuna cewa an samo shi ne daga wani waje. Me ya sa lamarin ya kazanta, inda ta kai ‘yan siyasa wadanda suka zabi tada rikici cikin al’umma ita ce mafita, suna amfani da kudinsu wajen samar da makamai ga wannan mummunar hali, a halin yanzu yana da tukar wahala su gya abin da suka yi, domin basa iya dawo da wadannan makamai ko da sun lashe zabe suna kan karagar mulki. Wadannan matasa basu san abin da suke yi ba ta inda suke wasa da rayukansu, sannan kuma suna ci gaba da amfani da wannan makamai wajen aikata rikice-rikice, fashi da makami da kuma kashe-kashe.
A akwanan nan ne aka cafke ‘yan fashi da makami wadanda suke yin kisan gilla, an nuna cewa da yawa daga cikin su ‘yan barandar siyasa ne wadanda ‘yan siyasa suka basu makamai, inda suka yi amfani da su bayan sun cimma burinsu sai suka yi watsi da su. Duk da haka a hayin yanzu wadannan matasa su kadai za su fuskanci hukuncin abin da suka aikata. Ana saka wannan laifin ga ‘yan siyasa, amma suma iyaye suna da nasu laifin wajen rashin binciken abin da ‘ya’yansu ke aikatawa. Gaskiyar magana ita ce, ‘yan siyasa suna amfani da yara maza wajen yin kashe-kashe ko kuma raunata wasu, yayin da su kuma ‘yan mata suke yin lalata da su. Wannan jaridar tana kira ga iyaye da malaman makaranta da shuwagabanin addini harma da su kansu matasan su tsaida wannan mummunar lamari tare da tambayan kawunanmu cewa indan muka yi wani aiki mene rabar da zamu samu. Kamar iyaye, su kasance masu jan kunnen ‘ya’yansu a kana bin da suke aikatawa.
A tsarin siyasar Nijeriya, mutane nawa ne suke da dangantaka da ‘yan siyasa wadanda suke yi musu barandar siyasa. A wannan lokaci, wadannan ‘yan siyasa suke kai ‘ya’yansu makarantun kasar waje, yayin da ‘yan uwansu da kuma yaran danginsu suna aiki wurare masu kyau, amma sun saka ‘yan barandar siyasarsu suna lalata rayukan mutane. A ra’ayinmu, muna kira ga hukumar fadakarwa ta tashi tsaye wajen gudanar da nauyin da ya rataya a wuyansu wajen ilmantar da matasa da kuma iyaye irin illolin da ke tattare da fadawa rikici wajen gudanar da ayyukan siyasa. Rundunar ‘yan sanda da duk sauran jami’an tsaro su yi kokari wajen ganin cewa matasa basu fada hannun baragurbin ‘yan siyasa ba. Har yanzu dai a cikin ra’ayinmu, wasu mutane suna amfani da matasa wadanda su kuma matasan sun kasa gane irin illar da ke tattare da haka, inda suke amfani da karfin iko wajen jan ra’ayinsu.Cikin wannan mako, rikici ya barke lokacin da jam’iyyar APC take gudanar da gangamin siyasa a jihar Legas, inda aka bayyana cewa rayuka da dama sun salwanta. Idan za a iya tunawa a baya mun yi kira ga matasa a kan illolin da ke tattare da fadawa hannun ‘yan siyasar da basu da manufa mai kyau, suna amfani ne da matasa kuma da zarar sun cimma burinsu sai su juya musu baya. Wajibi ne matasa su yi tunani.
A cikin watan Fabrairun shekarar 2019 za a yi babb an zabe, ‘yan siyasa sun fara daukan damara ta inda kota hadin yaya sai sun samu nasara, sun fara yin al’adar da suka saba wajen daukar hayar matasa maza da mata tare da basu makamai da kuma kayayyakin maye domin gudanar da rikici da rashin jituwa wajen kokarin sai sun kai ga karagar mulki. A wasu lokuta, ‘yan kunyoyin asiri sukan bayyanar da kansu wajen tada hankali gun zabe. Wannan lamari yana ci gaba da kamari duk da irin yadda ake musu wa’azi game da yin rikici da kuma kalamun da su dace ba wajen neman mukaman siyasa. Kafin hanzu, suna amfani da irin wannan mutane a siyasa a boye ne, sannan su barshi a tsakanin su. A wancen lokaci, ana yin hayar ‘yan barandar siyasa ne daga tashar mota da kan haya inda ake shaye-shaye da kuma sauran wurare da ake saida kwaya. Amma lamarin ya canza a halin yanzu. A yau, suna kewaye ne da maigidansu a matsayin matemakinsa ba tare da kayyade matsayinsu ba. Suna amfani da ‘yan barandar siyasa domin yin farmaki, kashe-kashe, rikici da kuma wajen karya doka da oda lokacin zabe ko kuma bayan zabe. Irin wadannan ‘yan siyasan suna baiwa wannan matasa tukwici na wajin gadi. A cikin kwanan nan ne hukumar kidaddiga ta Nijeriya, ta bayyana cewa rashin aikin yi ya tashi daga miliyan 1.9 zuwa 9.9 a cikin kwatan shekarar 2015. Amma a cikin shekarar 2017 kuma, kididdigan ya nuna cewa, matasan da basu da aikin yi a Nijeriya sun kai kashe 13.41 cikin dari. Ciyar da kansu ma ya zama musu tashin hankali, yawan matasan da basu da aikin yi yana nuna alamar cewa babu aminci a cikin jihohi, saboda haka ake samun rikice-rikice. Wasu daga cikinsu, shi ya sa suka addabi al’umma.
Kafin samun ‘yancin kai da kuma bayan samun ‘yanci kai lokacin zuwan dimokradiyya cikin wannan kasa, a baya, rikici baya cikin siyasar Nijeriya musamman wajen satar akwatin zabe. Tsarin yana nuna cewa an samo shi ne daga wani waje. Me ya sa lamarin ya kazanta, inda ta kai ‘yan siyasa wadanda suka zabi tada rikici cikin al’umma ita ce mafita, suna amfani da kudinsu wajen samar da makamai ga wannan mummunar hali, a halin yanzu yana da tukar wahala su gya abin da suka yi, domin basa iya dawo da wadannan makamai ko da sun lashe zabe suna kan karagar mulki. Wadannan matasa basu san abin da suke yi ba ta inda suke wasa da rayukansu, sannan kuma suna ci gaba da amfani da wannan makamai wajen aikata rikice-rikice, fashi da makami da kuma kashe-kashe.
A akwanan nan ne aka cafke ‘yan fashi da makami wadanda suke yin kisan gilla, an nuna cewa da yawa daga cikin su ‘yan barandar siyasa ne wadanda ‘yan siyasa suka basu makamai, inda suka yi amfani da su bayan sun cimma burinsu sai suka yi watsi da su. Duk da haka a hayin yanzu wadannan matasa su kadai za su fuskanci hukuncin abin da suka aikata. Ana saka wannan laifin ga ‘yan siyasa, amma suma iyaye suna da nasu laifin wajen rashin binciken abin da ‘ya’yansu ke aikatawa. Gaskiyar magana ita ce, ‘yan siyasa suna amfani da yara maza wajen yin kashe-kashe ko kuma raunata wasu, yayin da su kuma ‘yan mata suke yin lalata da su. Wannan jaridar tana kira ga iyaye da malaman makaranta da shuwagabanin addini harma da su kansu matasan su tsaida wannan mummunar lamari tare da tambayan kawunanmu cewa indan muka yi wani aiki mene rabar da zamu samu. Kamar iyaye, su kasance masu jan kunnen ‘ya’yansu a kana bin da suke aikatawa.
A tsarin siyasar Nijeriya, mutane nawa ne suke da dangantaka da ‘yan siyasa wadanda suke yi musu barandar siyasa. A wannan lokaci, wadannan ‘yan siyasa suke kai ‘ya’yansu makarantun kasar waje, yayin da ‘yan uwansu da kuma yaran danginsu suna aiki wurare masu kyau, amma sun saka ‘yan barandar siyasarsu suna lalata rayukan mutane. A ra’ayinmu, muna kira ga hukumar fadakarwa ta tashi tsaye wajen gudanar da nauyin da ya rataya a wuyansu wajen ilmantar da matasa da kuma iyaye irin illolin da ke tattare da fadawa rikici wajen gudanar da ayyukan siyasa. Rundunar ‘yan sanda da duk sauran jami’an tsaro su yi kokari wajen ganin cewa matasa basu fada hannun baragurbin ‘yan siyasa ba. Har yanzu dai a cikin ra’ayinmu, wasu mutane suna amfani da matasa wadanda su kuma matasan sun kasa gane irin illar da ke tattare da haka, inda suke amfani da karfin iko wajen jan ra’ayinsu.

Exit mobile version