Baqeer Muhammad" />

Illolin Mugun Sabo Da Wayar Hannu

Allah kadai ya san adadin masu amfani da manyan wayoyin hannu (Smartphones) a duniya, a kasar Amurka an kiyasta kashi 61 cikin dari na manyan mutane suna amfanin da manyan wayoyi, ba abun mamaki bane manyan wayoyin suna da matukar ba da sha’awa musamman wajen amfani da su, sun zame mana tamkar kananun kwamfuta na hannu, sanadiyar su mun kasance ba ma bukatar agogo mai kararrawa, ba ma bukatar karamin littafin rubuta adireshi da ma kyamarar daukar hoto, duk manyan wayoyi za su yi mana wannan aikin cikin sauki.

Amma fa duk da haka suna da na su matsalolin wadanda ka iya cutar da mai amfani da su, za mu dan duba wasu matsaloli a takaicce.

1-      Mugun Sabo:

Lallai da gaske ana mugun sabo da manyan wayoyin hannu, bincike ya tabbatar da ‘yan mata da suke zuwa manyan makarantu su kan rike manyan wayoyi a hannun su na kusan awa 10 cur, su na shiga intanet, akalla a wannan lokacin za su aika daruruwan sakonni, haka na nufin lokacin da su ka bata rike da wayar hannu ya fi wanda suka bata da abokansu, bincike ya nuna kashi 80 cikin dari na mutane baba  iya yin awa daya ba tare da sun duba wayar su ba, akwai wata nau’in cutar da take shafan kwakwalwa ma mai suna “Nomophobia” wato tsoron kasancewa ba waya a hannun mutum.

 

2-      Daina Amfani Da Manyan Wayoyi Na Da Matukar wahala:

Kamar dai shan kwayoyi masu sa maye, haka daina amfani da wayar hannu yake da matukar wahala, an yi wani bincike inda aka bukaci daliban jami’a su 1000 daga kasashe daban-daban guda goma su daina amfani da wayar su na tsawon sa’a 24, an gano dukkan daliban sun shiga halin kaka ni kayi saboda rashin wayar, wasu ma duk sun rude kamar za su zauto saboda ba su yi amfani da wayar su ba.

 

3-      Ciwon Baya:

Yawan dukawa domin duba sakonni ko kallon waya ya na matukar wahalar da bayan masu amfani da wayoyin, a kasar Birtaniya an gano yawan matasa ma su ciwon baya ya matukar daduwa saboda yawan amfani da wayar hannu, kusan kashi 45 cikin dari na matasa masu shekaru 16-24 suna fama da ciwon baya saboda yawan wahalar da kashin bayan su da suke wajen amfani da wayar hannu.

 

4-       Sanya Bakin Ciki Da Damuwa:

Dadewa ana kallon fuskar waya yana jawo damuwa har ma da bakin ciki, saboda mafi yawan lokaci ana tsammanin samun sako daga abokai da dangi, in sakon bai shigo ba sai a shiga damuwa ko ma bakin ciki, duk lokacin da mutum ya bata wajen amfani da wayar ya na nufin ya yi hasarar yin wani abu mai matukar muhimmanci Kenan, misali atisaye, ko dafa dafe na abinci ma su kara lafiya da sauran abubuwa, wadanda duk suna da matukar muhimmanci ga lafiyar jikin mutum.

 

5-      Rashin Barci:

Kashi 63 cikin dari na matasa ‘yan tsakanin shekaru 18-29 su na yin barci ne da wayoyin su a hannun su, wani bincike da akayi a shekarar 2014 ne ya tabbatar da hakan, sannan kusan kashi 30 na ‘yan tsakanin shekaru 30 da 60 su ma su na yin barci da wayar su a hannun su, masana sun tabbatar da ko sinadarin kafain (Caffeine) da ya ke matukar hana barci bai kai hasken wayoyin hannu hana barci ba, mafi yawan mutane ba sa yin amfani da sinadarin kafein amma suna kallon hasken fuskokin wayar su, an ce hasken fuskar waya ya fi kafein hana barci ninki biyu.

 

6-      Kwayoyin Cuta (Bacteria):

Yawan rike wayoyin hannu yana matukar kawo kwayoyin cuta, wani bincike da jami’ar Arizona ta kasar Amurka ta yi yana da matukar ta da hankali, in da suka gano yawan kwayoyin cutar da suke manne a jikin wayar hannu sun ninka wanda su ke a bayi (Toilet) sau goma, ku san ko yaushe ana wanke bayi amma fa wayar hannu ba a wani tsaftace ta, duk tsaftar bayin ka zai yi matukar wahala ka bari fuskar ka ta shafi inda ba shi da tsaftar, amma ko da yaushe wayar ka ta na shaffan fuskar ka, don haka yakamata a dinga tsaftace wayar hannu akai-akai.

 

7-      Tana Jawo Dabi’un Da Suka Saba Da Al’ada (Social Effect):

Yawan amfani da waya ya kan maida mutum saniyar ware a cikin ‘yan uwa da abokan arziki, sai ta hana mutum ziyartar ‘yan uwan sa ko abokan sa wanda hakan ba karamar illa ba ce gare shi, sannan tana matukar kawo rashin jituwa a tsakanin abokan zama, ta na sanya halin ko in kula sosan gaske, ga sanya mugun son kai, ta na rage taimakon al’umma wato (Prosocial Behabiour) inji masu bincike na jami’ar Maryland ta kasar Amurka.

 

8-      Rage Karfin Ido:

Yawan kallon hasken fuskar waya ya na jawo raguwar karfin ido sosai, ya na iya bata kwayar ido ma, hasken fuskar waya shi ne ake ce ma “Blue light” yawan kallon wannan hasken ya na jawo wata irin cutar ido da ta  ke hana mutum ganin abunda yake gab da mutum, duk da har yanzu ba’a san yawan adadin dadewa ana amfani da hasken wayar zai kawo makanta ba.

 

9-      Toshewar Ji:

Yin waya kawai ba zai kawo rashin ji ba, amma fa in mutum yana yawan amfani da lasifikar saw a a kunne (headphone) wajen jin kide-kide da manyan wayoyi to tabbas zai iya fadawa matsalar rashin ji, musamman in ana kure sautin karar kide-kiden akwai wasu kwayoyin gashi da suke kai ma dodon kunne sauti, sauti mai kara sosai yana kashe su, yawan sauraron kida da kara zai haifar da rashin ji na dindindin.

 

10-  Tiririn Sabis Din Wayoyi (Radiation):

Tiririn da sabis din manyan wayoyi yake fitar wa yana da matukar illa ga lafiyar jikin dan adam, hukumar kula da lafiya ta majalisar dinkin duniya (World Health Organisation) sun ce tiririn da manyan wayoyi ke fitar w aba karamin cutar da mutane su ke yi ba, kuma suna gab da kaddamar da wani bincike na raba gardama kan illar tiririn da manyan wayoyi ke fitar wa.

 

Exit mobile version