Connect with us

NAZARI

Illolin Rashin Adalcin Da Ake Aikatawa

Published

on

Adalci wani abu ne dake bayyana da ayi ma kowa yadda ya dace, gwargwadon yadda ya dace a yi, ba tare da nuna wani bambanci ba na  domin wani daga can yake, ko don ba da nan yake ba, ko kuma don harshensu daya, domin ita  mace ce , sai a yi mata abin da ma ya wuce  a ba ta, shi kuma namiji ai ta yi ma shi na mujiya kawai. Ko mun fito daga gari daya ne, mazabar kansilanmu daya, Karamar Hukuma daya, jiha daya, ko kuma ai daga sashe kaza da kaza muke, bari na dan daga ma shi, addinmu daya, duk idan ana maganar adalci tsantsar shi, bai kamata  a kalli daya daga cikin wadannan abubuwan ba. Idan kuma aka ce sai an yi hakan to sam bai dace ba, ba kuma haka ya kamata a rika tafiyar da al’amura ba, saboda komai nada nasa tsarin da za a tafiyar da shi, ba hakanan ba, a yi ta yin abubuwa kara zube, idan za a yi ma wasu bangare a bude idanu domin a kalle su sosai, idan kuma za a yi ma wancan bangaren sai kawai a rufe idanu domin bama a son a san ko su wanene su.

Idan aka kalli gida a matsayin wurin da za a fara duba adalci yadda yake farawa, saboda can ne ake fara komai na rayuwa, can ne mai gida zai fara al’amarin yadda ake adalci, tun yana ango a matsayinsa miji, ita kuma matar tana amarya, haka abin zai fara har dai ta kai ga an fara samun karuwa ta haihuwa, tun ana uku sannu a hankali har watarana a kai ga kasancewa ‘ya’ya sun samu. Sai dai kuma maganar yadda za a tafiyar da shi gidan. Daga nan ne kuma sai a fara maganar yadda za a yi hidimar ‘ya’ya wadanda suke maza da mata ne, anan bai kamata shi maigida ya rika yin rashin adalci ba, a tsakanin ‘ya’yansa, musamman ma ko a cikin maza, ya nuna bambanci ke nan  wanda rashin adalci ne. Idan ya ci gaba da nuna wannan halayyar hakanan gidan kuwa zai kasance a samu rarrabuwar kai tsakanin ‘ya’yan na sa, wanda idan ba sa’a aka yi ba, gidan zai iya zama wani wuri ne na shuka kiyayya tsakanin ‘ya’yan na shi. Wannan ya nuna ke nan tamkar gida ya baci ke nan, idan Isa ya ce a ba shi wani abu sai a ce ma sa wani abu nan da nan za a yi ma shi, amma kuma idan Sallau ya nemi da a ba shi  wani abu ko kuma a yi ma sa yadda aka yi ma Isa, sai a fara fada ma shi maganganun da basu kamata a fada ma shi ba. To wannan tun a gida ma ke nan  an fara takin saka a dalilin yadda mahaifi yake yi, irin hakan sai su ‘ya’yannan su kai ga nasu ‘ya’yan har ma a kai ga yin jikoki, abin har ya kai ga yin gaba, wadda za ta dade ana yi. Sai maganar aure idan ba sa’a ka yi ba nan ma din a kan taba rashin adalcin wanda shi ma kan kasance, sanadiyar yarinya ta tafi uwa duniya karuwanci, dalili kuwa, wasu iyaye inda su kan yi nasu rashin adalcin shi ne, lokacin aure wasu sukan duba Naira ce ba maganar hali ba, koda kuwa, shi ya mai son yarinyar tasu da aure ne yake. Ba maganar nagari suke ba, su babbar nagarinsu ita ce Naira, farin cikinsu ke nan, koda kuwa ace shi yafi kowa munanan ayyukan ashsha, su ba wannan ya dame su  ba, da zarar dai za su yi ido hudu da Naira. Daga karshen idan ita yarinyar ba mai daukar irin halin bace, sai ta shiga uwa duniya, wanda kuma su iyayen  nata suna da kamisho, akan dukkan abubuwan data aikata, saboda ai basu zaba mata miji nagari ba, sun tafka mata rashin adalcin ne.

Idan aka kammala da gida sai kuma makaranta saboda nan ma wani wuri ne da wasu marasa tsoron Allah ke nuna rashin adalci, idan ka dauki Malaman makaranta, sune ke amfani da ita wannan kalma, saboda su yi yadda suka ga dama da dalibai, badan komai ba sai saboda sun san cewar su a matsayin wata matakala ce wadda daliban ke bi, su samu tudun dafawa. Don haka sai yadda suka ga dama za su yi, wasu daliban ba wai saboda ba su da kokari bane ake kada su jarabawa, ana yi masu rashin adalci ne musamman ma ganin cewar, su daliban da akan yi ma haka, ba su da wata hanya da za su yi maganin sa al’amarin, sai dai ko  su yi Allah ya isa, ko kuma suce ai ba komai. To irin wadannan daliban da ake danne ma hakki a dalilin rashin adalci, idan ba sa’a aka yi ba, ya kasance su tun suna ‘yan yara ba wai an yi masu kyakkyawar tarbiyya, a gaba irin sune ke haduwa
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: