Connect with us

HANTSI

Illolin Ruwan Sanyi Guda Takwas

Published

on

Ruwan sanyi yana da dadin sha a baki musamman idan kishi ya kama mutum. Sai dai likitoci sun bayyana cewa yana da illoli ga jikin Dan Adam. Shafin Hantsi Leka Gidan Kowa ya yi muku nazarin illolin kamar haka:

  1. Tsaida Bugun Zuciya: Bugun zuciya shike gyara dumin jiki da daidaita numfashi to rowan sanyi yana sa bugun zuciya ya rika raguwa har takai ga tsayawa. Ko kunsan yawancin’ yan Fim na kasar Indiya  da ‘yan Ball da Boding da Wrestling tsayawar bugun zuciya ke ajalinsu kuma bincike ya nuna yawancin shan ruwa mai sanyi yayin da suke aikine yake jawo masu.

 

  1. Lalata Tsarin Kayan Ciki: Shan ruwan mai sanyi yana tattare hanta guri daya sai ya sanya abinci yaki narkewa da wuri hakan kan ke jawo tsalar hanji (Ulcer) kenan ko kuma tashin zuciya. Yawan zubda yawu ko tashin zuciya ko saurin kullewar ciki.

 

  1. Dauke Karfin Jiki: Duk da cewa shan rowan sanyi kan sa mutum ya ji dadi amma a hankali yana dauke masa karfin jiki sakamakon cewa yayin da ruwa mai sanyi ya shiga jikinsa dole sai na’urorin jikin sunyi kokarin su na ganin sun maida wannan rowan ya daidaita da dumin jikin hakan yana sa suyi rauni sakamakon kokarin da suke yi yana wuce haddi. Ko kun lura duk sanda kuka sha ruwan sanyi sai kunji duk jikin ku  sanyin ya ratsa Kaman farkon zazzabi a hankali kuma sai ku ji ya daina?

 

 

  1. Ciwon Makogwaro Da Dakushewar Murya: Yawan amfani da rowan sanyi yana lalata jijiyoyin makogwaro har su kai ga basa amfaninsu mai kyau a mai shay a kai shekaru 40 sai ya fara fama da ciwon makogwaro da dakushewar murya ta fashe kwatankwacin mashayin taba.

 

  1. Ciwon Hanta Da Koda: Dukkan su suna bukatar wadataccen ruwa a jikinsu don haka yayinda bawa ya zama yana amfani da ruwa mai sanyi zai zamo su kuma suna cutuwa ta yanda aikinsu zai fara kasa in haka ta samu mutum ya shiga mastala.

 

 

  1. Busar Da Ruwan Jiki: Akwai na’urori a jikin dan Adam da aikinsu shine sadar da ruwa ko ina na jikinsa zai samu damar motsawa cikin nishadi. To wadannan na’urori sukan yi sanyi sakamakon ruwan sanyi sais u zama jiki ba kwari.

 

  1. Matsalar Ma’aurata: Wannan abune tabbatacce har ga likitocin zamani cewa shan ruwan sanyi yana raunata mazantakar namiji yana kuma busar da mace in mahaifarta nada rauni yana iya hana haihuwa. Yana tsinka maniyyin namiji ya zama yana saurin biyan bukata ko kuma na rage masu kuzari. Yana dauke ni’imar jiki su zamo basa gamsuwa da juna.

 

  1. Basir Da Ciwon Kai Na Gefe (Migraine): Shan ruwan sanyi yanda na ce muku yana tattare hanji hakan yana kawo mutum ya kasa bayan gida sai ya hadu da basir.

Sannan yana kawo ciwon barin kai wanda ake cewa migraine. Shi kuma migraine yana kasha jijiyoyin jikin ido a daina gani sosai in yayi nisa har hauka yana sawa.

 

Allah ya bada ikon kiyayewa amin summa amin.             

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: