Connect with us

NAZARI

Illolin Shaye-Shaye Da Hanyar Kawar Da Shi

Published

on

sshinco@yahoo.com

mameerah@gmail.com

Shaye-shaye dai yana nufin amfani da wani abu da zai gusar wa mutum da hankali ko ya saka shi maye: ta hanyar sha, shinshinawa, ci, busawa ko kuma allura. A zamanin baya, sai dai muji labarin irin wanan dabi’ar a kasashen ketare, wasa-wasa har ya shigo cikin kasar mu da al’ummar mu. Babban abun takaici halaya ce da aka fi dangantawa ga maza, sai ga shi ya zama ruwan dare har mata sun fi maza iyawa.

da yawa mutane basu san me ke kawo wanan dabi’ar ta shaye-shaye ba, ko kuma suna kan hanyar fadawa shaye-shayen ba tare da sun sani ba. Kadan daga cikin abinda ke kawo shaye-shaye ya hada da;-

 1. Shan magani bada izinin likita ba; da yawa muna da wanan dabi’ar, da mun ji rashin lafiya sai muje Kemis mu siyo magani mu fara sha ba tare da likita ya gwada mu ba ya tabbatar mana da abinda zamu sha din ko ya dace da jinin mu.

 2. Rashin amfani da magani a kan ka’idar da aka dora mu; misali an ce kayi sati daya kana sha, sai kayi kwana ukku, ko kuma ka zarce adadin kwanakin, Ko kuma an ce kasha cokali daya sai ka sha rabin kwalba.

 3. Matsalar bawa yara rashin kulawa; wasu iyayen basu damu da jan ‘ya’yan su a jiki ba, har su san damuwarsu, irin wanan yana kawo matsalar da a Turanci ake Kira ‘depression’. Kuma ana iya samun wanan matsalar a tsakanin ma’aurata da suke samun matsala,daga haka shaye-shaye zai iya biyo baya.

 4. Mu’amala da abokai masu shaye- shaye shi ma yana janyo matsalar a al’umma.

 5. Wasu iyaye mata suna da sakacin shan magani barkatai idan suna da ciki, wanda hakan na iya taba jinjiri kafin ma ya zo duniyar an koyar da shi. Ko Kuma mata masu ajiye magani barkatai a ko Ina suka ga dama,har yaro ya dauka ya Sha.

6.Wani lokaci likitoci kansu suna janyo wanan matsalar ta hanyar hada mutum da abinda jininsa ba zai iya dauka ba.

Wadanan sune hanyoyi sanannu da ke iya hadddasa matsalar shaye-shaye a cikin al’umma.

ILLAR DA SHAYE-SHAYE GA MUTANE

Idan mutum ya riski kansa a yanayin shaye-shaye, hakika rayuwarsa tana canjawa gaba daya. abin zai taba lafiyarsa, mu’amalar sa da mutane, aikin sa kai har hankalinsa zai iya rasawa baki daya. Ko a wayi gari mutum ya rasa ransa,toh meye ribar hakan?

A cikin al’umma duk wata barna, ta’adanci, rashin ta- Ido za kaga sun faru sai ka tarar da Mai aikata wanan abun

yanada dabi’ar shaye-shaye. Misali ‘yan fashi, masu yi wa mata fyade da barayi.

Shaye shaye yana kawo mutuwar aure, rasa aikin yi,talauci rashin zama lafiya da mutane,tabarbarewar tarbiyar yara da fadace-fadace. Ashe wannan zai nuna nana cewar matsalar shaye- shaye ba karamar matsala bace ga rayuwar mutum,da al’umma Baki Daya.

Abun tambaya yanzu yaya za a yi a magance wanan matsalar ta shaye shaye?

YADDA ZA A MAGANCE SHAYE-SHAYE

na yi bayani a kan abinda ke kawo shaye-shaye, da Kuma illolinsa ga mutum da al’umma baki Daya. Yanzu Kuma zan yi bayani a Kan hanyar Kare Kai daga fara shaye- shaye, da Kuma hanyar kawar da shi baki daya.

Yawancin mutane suna fara shaye- shaye saboda wata damuwa ko kaddara da ta hau kansu suka kasa jurewa, ko Kuma zama da masu irin wanan dabi’ar. Wadanan hanyoyin za su taimaka wurin Hana faruwar matsalar shaye shaye:

 1. Yana da kyau mutum ya fuskanci matsalarsa yayi kokarin magance ta maimakon ya fada shaye shaye.

2, Iyaye Yana da kyau su dinga Jan yaran su a jiki domin su San damuwarsu,Kuma su san irin abokanin da suke mu’amala da su.

 1. Maza ya kamata su daina tsangwamar matan su,su dinga Jan su a jiki,da Kuma sanin irin kawayen da suke Hulda da.

 2. Haka zalika maza su nisanci mu’amala da masu irin wanan dabi’ar Kuma su kasance masu karban kaddara a duk yanda ta zo musu,kada hakan ya zama dalilin fara shaye-shayensu.

 3. Mu guji Shan magani ba tare da izinin likita ba,Kuma mu kiyaye ka’idojin shan maganin.

 4. Mata su guji amfani da magani barkatai a lokacin da suke da juna biyu ko kuma, ajiye magani barkatai saboda kada Yara su dinga dauka suna Sha.

 5. Likitoci su San aikin su da kyau, su kiyayi baiwa mutum maganin da yafi karfin jinin sa ko zai iya janyo Masa matsala.

Hanyoyin da ya kamata kuma abi dan kawar da matsalar shaye- shaye sun hada da:

 1. Janyo masu matsalar a jiki, Ana lurar da su illar hakan, a guji tsangwamar su da kyara.

 2. Ya kamata gwamnati ta Kara daukar mataki a Kan masu Kemis da ke siyarwa mutane magani ba tare da takarda ba daga likita,wato prescription.

 3. A nemawa matasa sana’oi da za su dinga dauke hankalin su, Kuma su hanasa su zaman kashe wando.

 4. A bude wuraren da za a dinga Kai masu wanan lalurar ana killace su, da taimaka musu har a rabasu da lalurar,wato rehabilitation centers a Turance.

 5. Ya kamata hukumar fasa kwarin kwayoyi ta Kara kaimi wurin Kama masu sayar da magani a bayan fage.

 6. Gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu, su kara kaimi wurin ilmantarwa da fadakarwa, ta hanyoyi da sako zai Isa zuwa ga mutane a birni da kauyuka.

Idan aka bi wanan hanyoyin Ina ga za a samu saukin lamarin shaye- shaye a al’umma, koma a kawar da ita baki daya.

Masu yi Allah ya ganar dasu su daina, muda bama yi Allah ya tsare mu da zuri’ar mu baki daya, amin ya rabbi!
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: