Connect with us

LABARAI

Ilmantar Da ‘Ya’yan Fulani Makiyaya  Zai Magance Rikici Da Manoma – Ardo Mato

Published

on

 


Kasancewar wutar rikici tsakanin Fulani Makiyaya da Manoma sai kara ruruwa take yi a jihar Filato, an nemi al’ummar Fulani makiyaya da su fi maida hankali wajen ba ‘ya’yansu ilimin addini da kuma na zamani fiye da duk wadansu ayyuka dake gabansu.
Daya daga cikin Shugabannin Fulani Makiyaya, Ardo Mato Hassan daga yankin gundumar Mayongo cikin karamar Hukumar Bassa dake jihar ne, ya yi wannan kira a lokacin da yake ganawa da wakilimmu a kan rikicin tsakanin Fulani makiyaya da manoma a jihar a makonnan, ya ce, ilmantar da ‘ya’yan filani makiyaya , shi ne kawai hanya mafita bisa irin halin da Fulani makiyaya suka sami kansu a jihar Filato da wadansu jihohi da ke a tsakiyar Najeriya.  Ya ce, ba’a yawan hare hare da ‘yan ta’ adda suke kaiwa Filani suna ta kashe’su da dabbobin su abin damuwa ne kwarai. Ya ce, yankinsa ba’a dade ba, mahara suka kai wa rugar daya daga cikin su mai suna Isa inda suka nemi kashe shi, da basu samu nasarar kashe shi ba, sai suka juya akan shanunsa suka kashe shanu 60 daga cikin  rugarsa ya kara nuna damuwarsa .
Hardo Hassan ya nuna matukar damuwar sa akan rashin samun kyakkyawan tsaro daga jami’an tsaro dake aiki a jihar, ya ce duk da gudunmawar da suke nema daga jami’an tsaro bai  hana a kawo masu harin ba, ya ’yi kira da babbar murya ga gwamnatin Tarayya da ta hanzarta aiwatar da shirin nan na kebe wa Fulani makiyaya Gandun Dajin kiwo don karfafa masu gwiwa wajen ba ‘ya’yansu ilimi mai inganci kuma ya ce, hakan zai taimaka ainun wajen rage yawan tashe tashen hankula da ake samu yanzu a tsakanin Fulani makiyaya da manoma a wadansu jihohin kasar nan.

Ya nuna matukar damuwarsa a kan ganin yadda rikicin yaki ci yaki cinyewa a jihar Filato, saboda haka yace, duk da irin kokarin da gwamanan jihar da shugabanbnin al’ummomi, da na addini ke yi a jihar don kawo karshen rikicin an kasa gano bakin zaren har yanzu.
Ya yi kira ga al’ummar jihar dasu cire babbancin kabilanci da na addini su hada kai da filani makiyaya dake zaune a yankunansu don a samu zaman lafiya mai dorewa a jihar da kuma kasar baki daya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: