IMF Ta Bukaci Nijeriya Ta Samar Da Cikakken Tsarin Tattali Arziki

Asusun bayar da lamuni na duniya IMF ya gardadi Nijeriya akan cewar tana bukatar cikakken tsari don tattalin arzikin ta ya bunkasa a cikin wattani masu zuwa.

Gargadin yana kunshe ne a cikin sanarwara da Babban jami’ain asusun a Nijeriya Mista Amine Mati ya fitar, inda kuma ya kara gargadin kasar akan cewarb tattalin arzikin ta yana da mahimmanci sosai.

Mati wanda ya snar da hakan a madadin gidauniyar a cikin sanarwar bayan ya jagoranci ma’aikatan asusun da suka ziyarci Nijeriya daga ranar 27 na watan Yuni zuwa 8 ga watan Yuli, 2018 don tattaunawa akan tattalin arzikin kasar na kwanana baya da kuma yin nazari akan wanzar ta tsare-tsare, ya yi nuni da cewar, hauhauwan farashin kasar zai kara hawa a a tsakiyar shekara.

Ya ci gaba da cewa, hauhawan farashin mai da kuma yin aiki na gajeren zango ya samar da sauki daga waje da kuma nauyi, inda yace, farfado da tattalin arzikin kasa har yanzu akwai kalubalen da kasar ke fuskanta.

Acewar sa, asusun ajiya na kasar a daidai yake, inda ya kai kimanin dala biliyan cording to him, 47 duk da rashin samun samun karin kudin shiga na waje a cikin watan Afirilu ya kuma yi nuni da cewar hauhawan farashi ya sauka a kasar a ciukin sheakaru biyu da suka kuma tattalin arzikin kasar yana kara fadada zuwa kashi biyu a cikin farkon shekarar 2018 indan aka kwatanta da shekarar data abata.

Sai dai ya yi nuni da cewar gudanar da ayyuka a sashen da ba na mai ba  da kuma na aikin noma ya yi rauni inda hakan ya sanya abinda ake iya saye yakan yi wuya kuma bankuna basa bayar da bashi ya kuma yi nuni da cewar akwai bukatar da kara yawan harajin da ake karba da kuma tabbatar da ana bin ka’idar kasafin kudi musamman ganin kakar zabe ta matso.

Ya yi nuni da cewa, tsare-tsaren da aka samar sun habaka kasuwanci musamman da baiwa zuba jari mahimmanci da rungumar dokar kamafni ta (CAMA), inda hakan zai taimakwa yan kasuwa na kasar masu zaman kansu.

Wanzar da tsarin farfado da wutar lanatrki da kuma sanya ido akan masu amfani da wutar da samar masu da mita ta zamani ya taimaka sosai.

Acewar sa, kara fitar da mai zuwa waje asusun kasar zai kara samun karin kudi da kuma kara daukaka matsayin asusun ajiya na kasar dake waje, inda ya kara da cewar, tawagar ma’aikatan sun kuma tattauna da jamia’n babban bankin kasa CBN tare da ganawa da wakilan wasu bankuna da yan kasuwa masu zaman kansu da kungiyoyi da kuma abokan hudda na kasa da kasa.

Exit mobile version