IMF Ta Yi Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Nijeriya Da Kashi 2.1 A Bana

Kasa da sati biyu bayan da Bankin duniya ya yi hasashen karfafan tattalin arzikin Nijeriya, (GDP) wanda a cewarsa, zai karfafa da kashi 2.5, Hukumar bayar da lamuni ta Duniya (IMF), ita kuma a wannan ranar Litinin din ne ta bayyana cewa tattalin arzikin zai ja baya.

A mahangar hukumar bayar da lamunin, na wannan shekarar ta 2018, tattalin arzikin Nijeriya zai bunkasa ne da kashi 2.1 a wannan shekarar ta 2018. Mahangar hukumar kuma ya yi hasashen tattalin arzikin Nijeriyan zai ruburbusa kasa da kashi 1.9 ne a shekarar 2019.

Hukumar ta bayyana cewa, “Kasashen Afrika da suke a yankin kusa da sahara, tattalin arzikinsu zai bunkasa daga kashi 2.7, na shekarar 2017, zuwa kashi 3.3 a shekarar 2018, da kuma kashi 3.5 a shekarar 2019.

Hakanan kuma hukumar lamunin ta duniya, ta lashe amanta a kan hasashen da ta yi na tattalin arzikin duniya a shekarun 2018 da kuma 2019, zuwa kashi 3.9.

A dukkanin shekarun biyu, yana a saman kashi 0.2 koma bayan hasashen watan Oktoban da ya shige, da kashi, 0.2 sama da abin da aka kiyasta na tattalin arzikin duniya a shekarar da ta gabata.

A ta bakin babban daraktan binciken hukumar ta lamuni, Maurice Obstfeld, “shugabannin siyasa da masu mulki ya kamata su yi hattara, kan cewa dan dagowar da tattalin arziki yake yi a dan wannan lokacin ba lallai ne ya dawwama ba.

“Ya kamata kowace gwamnati ta tambayi kanta wadannan tambayoyi guda uku a yau din nan. Ta ya zamu tayar da komadar tattalin arzikinmu na tsawon lokaci? Tambaya ta biyu, ta ya zamu iya tallafansa a ciki da waje a lokacin da ya kasance karfafan da yake yi zai iya komawa baya a kowane lokaci?

“Tambaya ta uku, ta ya zamu tabbatar da cewan, mun mallaki dukkanin makaman da za su kare mana shi, muna kuma tafiya ne a kan tsarin tunkarar ko-ta-kwana.

 

Exit mobile version