Imo: Zanga-zangar PDP Ba Za Ta Canja Komai Ba – BCO

Kungiyar ‘Buhari Campaign Organisation’ (BCO) a jiya Lahadi ne take shaida cewar shirye-shiryen yin gangamin babban zanga-zanga da jam’iyyar PDP ke shirin yi, ba zai taba canza matakin da matsayar da Kotun Koli ta yanke kan zaben gwamnan jihar Imo da ta tsige tsohon Gwamna Emeka Ihedioha na jam’iyyar PDP gami da ayyana Hope Uzodinma na jam’iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar ta Imo.

Kungiyar ta misalta yunkurin jerin gwanon a matsayin “Rashin mutunta doka da oda”, sun kara da cewa, “Nijeriya tana tafiya ne gaba daya a kan doka da oda wanda aka sanya ikon ga sashin Shari’a a matsayin masu yanke hukunci na karshe,”

Ko’odinetan BCO na kasa, Alhaji Danladi Pasali a cikin watan kwafin sanarwar manema labaru da ya rabar wa manema labaru, “Abun fata ne ga kowani bangare a Nijeriya da ya amshi hukuncin kotun koli a kowani gaba,” A cewar kungiyar.

Daga bisani ya shawarci jam’iyyar PDP da su amshi hukuncin da zuciya guda, kana Pasali, ya bukaci ‘yan Nijeriya su kasance masu kwantar da hankalinsu, kana su bijire wa shiga zanga-zangar da PDP ke shirin hadawa.

 

Exit mobile version