Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi a ranar 1 ga wata ta kafar bidiyo a wajen babban taron MDD na tunawa da cika shekaru 25 da shirya babban taron mata na kasa da kasa a Beijing.
A cikin jawabinsa, shugaban na kasar Sin ya jaddada muhimmancin tabbatar da kiyaye hakkokin mata, inda ya ce, ya zama tilas kare hakkokin mata ya zama muradun kasa. A yayin da ake samun farfadowa bayan annoba, ya kamata a samar wa mata sabon zarafin shiga harkokin siyasa, a daga matsayin mata na shiga ayyukan tafiyar da harkokin kasa da harkokin tattalin arziki, al’adu da zaman al’ummar kasa. Sanin kowa ne na cewa, mata ne suka kirkiro al’adun bil Adama, suna kuma kara azama kan ci gaban zaman al’ummar kasa. Ya zuwa yanzu, suna kokarin cimma nasarorin da za su wuce zaton mutane a sana’o’i daban daban a mabambantan sassan duniyarmu. A matsayinta na babbar kasa da ke sauke nauyin dake wuyanta, kasar Sin ta tabbatar da daidaiton jinsi a matsayin wata muhimmiyar manufarta. Kawo yanzu, Sin ta kafa wani ingantaccen tsarin kare hakkokin mata, ciki har da zartas da dokoki sama da 100, da kawar da gibin jinsin dake kasancewa a fannin bada ilimi. Kasar Sin tana rubanya kokarinta na ganin kowace mace ta samu damar cimma burinta. Sa’an nan kuma daga dukkanin mutanen da suka samu ayyukan yi a kasar Sin, sama da kaso 40 bisa dari mata ne. A fannin yanar gizo kuwa, yawan mata da suka habaka cinikinsu ya zarce rabin yawan mutanen da suka habaka ciniki.
Yayin da kasar Sin take kokarin kawar da bambancin ra’ayi da wariyar jinsi da ake nuna wa mata da cin zalin da ake yi musu, da zummar ganin daidaiton jinsi ya zama ka’idar kowa da kuma da’ar kowa a zaman al’umma, a jihar Kaduna ta tarayyar Nijeriya, kuma an samu wani labari mai kyau a kwanakin baya.
Sakamakon dokar kulle da aka aiwatar a kasar ta Nijeriya a watanni da dama da suka wuce domin dakile kandagarkin annobar COVID-19, an samu karuwar yawan fyade da aka yi wa mata. Don haka wasu kungiyoyin mata suka yi kira da a kara daukar tsauraran matakai kan wadanda suka aikata laifin, ciki had da yi musu hukuncin kisa. An zartas da wata doka a kwanan baya a jihar Kaduna, inda dokar ta ce, za a yi wa maza da mata wadanda suka aikata laifin fyade aikin tiyata kan sassan jikinsu da suka shafi haihuwa tare da yanke musu hukuncin daurin rai da rai. Dukkan wadanda suka yi fyade kan kananan yara ’yan kasa da shekaru 14 da haihuwa, za a yanke musu hukuncin kisa. Zaman wakafi na lokaci mafi tsawo da aka yanke wa wadanda suka aikata laifin fyade shi ne shekaru 21 bisa dokar da ake bi a halin yanzu a Kaduna, yayin da aka yanke wa wadanda suka yi wa kananan yara fyade hukuncin daurin rai da rai. Gwamnan jihar ta Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai ya jaddada cewa, zartas da wannan doka zai taimaka wajen kara kare mata da kananan yara daga miyagun laifuffuka.
Ci gaban da aka samu wajen kiyaye hakkokin mata a kasashen Sin da Nijeriya sun faranta rayukan mutane sosai. Yayin da masu iya magana suke ambato rawar mata, su kan ce, in ba ku ba gida. In ana fatan samun kyakkyawar makomar dan Adam, to, ana bukatar hazakar mata da kuma karfinsu. Akwai sauran rina a kaba a kafa wata duniya, inda ba a nuna bambancin ra’ayi da wariyar jinsi ga mata. Sai mu ci gaba da hada kai wajen gaggauta samun daidaiton jinsi da kara azama kan ci gaban sha’anin mata na duniya. (Tasallah Yuan)