In Kuka Zabe Ni Shugaban Kasa, Ba Zan Ba Ku Kunya Ba –Yahaya Bello 

Cin Zarafi

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello,ya yi alkawarin cewa, ba zai taba ba ‘yan Nijeriya kunya ba matukar suka zabe shi ya zama shugaban kasa a shekara ta 2023.

Bello ya bayyana hakan ne a wani shiri da gidan talabijin na ‘Channels Television’ ke gabatarwa mai suna ‘Siyasarmu A Yau’.

“’Yan Nijeriya da suka hada matasa da mata da wasu dattawa ne suka bukaci in fito takarar shugaban kasa a 2023.

“Na yi imani da cewa, a wannan lokacin ‘yan Nijeriya za su tabbatar da cewa, sun zabi wanda ya cancanta, wanza zai iya tafiyar da al’umma da bumkasa tattalin arzikin kasa da kuna sanar da tsaro.

“Na tabbatar da cewa, mutane sun lura da wasu abubuwa ne ya sa suka bukaci in fito takarar shugaban kasaI, musamman ganin yadda muke kokarin hada kan al’ummar kasa domin samar da ci gaba da bunkasa rayuwarsu.

“Al’umma kasar nan za su kara fahimtarmu sosai matukar suka ba mu goyon baya nab a mu damar tafiyar da ragamar mulkin kasar nan a zabe mai zuwa in Allah ya kai mu.

“Saboda haka ina nukatar dukkaninmu mu kasance masu hakuri. Mu hada kai domin kawo ci gaba. Ina tabbatar muku da cewa, b azan taba cin amanarku ba, matukar kuka ba ni wannan dama,” in ji Bello.

Exit mobile version