Abubakar Abba" />

Ina Alfahari Da Matasa ‘Yan ‘NYSC’, inji Shugaba Buhari

Kasa Muhammadu Buhari ya kara jaddada aniyar sa na cecar imanin sa yana nan daram akan masu yiwa kasa hidima kuma har yau bai cnaza ba.

Ya fadi hakan ne a kasarsa ta hauhuwa kmDaura dake cikin jihar Katsina a lokacin da ya karbi bakuncin masu yiwa kasa hidima da suke gudanar da aikinsu a garin suka kai masa gaisuwar barka da Sallah.

Buhari a yanzu haka yana gudanar da bikinsa na sallah ne a Daura kuma tun lokacin da ya dare karagar mulkin kasar shekaru uku da suka shige yake zuwa garin yin sallah kara da babba.

Ya kara jaddda da goyon bayansa akan shirin da aka kirkiro dashi a 1973, inda yace yafi a san komai gale da kasar maimakon a boyewa mutane wani abu, akoda yaushe ina son inga yan yiwa kasa hidima domin mafi ayyuka na na soja nayi su ne a Kudu.

Yaci gaba da cewar, a lokacin yana aikin soja mafi yawzncin mutane basu san wurare ba, amma ga su masu yiwa kasar hidima da aka turo daga Kudu zuwa yankin sahara akwai wahalhalu da dama amma hakan zai yi mahimmanci ga Nijeriya, kuma nida kaina nayi magana da Janar  Gowon don in gode masa akan kirkiro da shirin ganin irin dimbin mahimmancin da yake dashi ga kasar nan.

Ya kuma nuna jin dadinsa akan yadda kasar nan take tafiya akan turba wajen wadata kasar da abinci  ya kuma godewa Allah akan amfanin gina da aka samu a bana ina kuma fatan sauran damina fa zasu zo a nan gaba albarkar ta rubanyya, musamman don a daina shigo da abinci cikin kasar baki daya.

Acewar sa, dukkan nasarorin da aka samu an same sune saboda shirye-shiryen da gwamnatin sa ta samar na ciyar da aikin noma gaba a kasar.

Da yake tsokaci akan dubban alummar yankin da suka fito suna cewa sai Baba a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa gifa bayan an tashi daga sallar Idi a  massalacin Daura   Buhari ya godewa masu da kuma kara neman goyon bayansu don ciyarbda ksar gaba.

A nashi jawabin shugababan tawagar masu yiwa kasar hidima , Jibrin Ishak, ya godewa shugaban kasar akan inganta walwalar masu yiwa kasar hidima da kuma yiwa shugaban alkawarin sake komawa akan kujerarsa a zaben 2019.

Exit mobile version