Ina Da Muradin Daidaita Matsalolin Da Ke Jibge A Bauchi –Farfesa Sani Malami

FARFESA SANI ABUBAKAR MALAMI Daya ne daga cikin ‘yan takarar gwamnan Jihar Bauchi a zaben 2019. A hirarsa da LEADERSHIP ya shaida dalilan da suka sabbaba ya fito neman wannan kujerar. Farfesa Malami wanda tsohon Kwamishinan Lafiya ne a jihar, ya kuma kasance malamin makaranta inda ya kwarance sosai kan harkar lafiya, ya bayyana cewar yana da tsararren tsari wanda hakan zai kai ga kawo karshen matsalolin da suka yi wa jihar Bauchi katutu da zarar aka ba shi zarafi. Wakilinmu na Bauchi KHALID IDRIS DOYA ne ya tattauna da shi:
Ka gabatar mana da kanka?
Sunana Farfesa Sani Abubakar Malami, ni Likita ne, Malamin Jami’a ne kuma ina dan taba siyasa.

Kana daga cikin ‘yan takarar kujerar gwamna a Jihar Bauchi a zaben 2019, mene ne ya sanya ka fito neman wannan kujerar?
A tunani na lokaci ya yi da ya kamata na tsaya na saurara wa irin shawarwarin da jama’a suke bani na tsawon lokaci, daga cikin su akwai iyaye, akwai shugabanninmu, akwai yayu, akwai kanne akwai abokan mu’amala wadanda sun san abun da ya kamata; sun zo kashi da yawa suka sameni akan cewa ya kamata a gwada neman wannan kujerar; domin a fahimtarsu ina da wasu alamu da zan iya taka rawa wajen ci gaban Jihar Bauchi, a fahimtarsu lokaci ya yi da zan nemi kujerar gwamna domin samar da mafita wa jama’an Jihar Bauchi. A dunkule dai ba nine na yanke shawara kawai cewa zan fito neman wannan kujerar ba, a’a, jama’a ne suka nemi na fito takarar gwamnan Jihar Bauchi.

Idan Allah ya baka nasara a wannan gwagwarmar maya da kake yi, wasu fannoni ne za ka fi maida hankalinka a kai?
A cikin gwagwarmayar da aka fara dangane da neman takarar gwamnan na, matakin da muka fara dauka shine ziyarce-ziyarce da na ke kaiwa birni da kauye don tuntuba, musamman ga iyayen kasa, malamai, da kuma magabantanmu, a dukkanin fadin Jihar Bauchi babu shiyyar da ban taka ba, babu wata karamar hukuma daga cikin 20 da suke Jihar Bauchi da ban taka na je neman shawarorin manya ba. Daga cikin shawarwarin da na samu sun kara bani haske na irin dumbin matsalolin da suke fuskantar Jihar Bauchi.

Na farko shine rashin abun yi, ba kawai ga matasa ba, kowa da kowa, kama daga mata, maza, yara kai har ma dattawa ‘yan fansho ya kamata a ce suna da dan abun da za su rufa wa kansu asiri, to gaskiya akwai matsalar abun yi sosai a Jihar Bauchi don haka da bukatar a farfado da tattalin arzikin Jihar Bauchi domin jama’a su samu abun yi. Na biyu, ni dai malamin makaranta ne, ilimin nan ita ce ginshikin ci gaban al’umma, an yi watsi da batun ilimi, a halin da muke ciki a jihar Bauchi zan iya cewa Jihar Bauchi tana na baya-baya a dangane da matakin ilimi a Nijeriya baki daya, kama daga matakin Firamare, Sakandari da ma manyan makarantu ne ko Jami’o’i, don haka a cikin tunani na, idan Allah ya bamu nasara za mu sanya ido mu tabbatar an samu gyara a cikin harkar ilimi a Jihar Bauchi. Na uku, sha’anin lafiya, na yi aiki a matsayin kwamishinan lafiya na tsawon shekaru hudu na san matsalolin da suke fuskantar wannan sashin a Jihar Bauchi, don haka za mu yi iya bakin kokarinmu gwargwadon abun da Allah ya bamu daman yi. Wato mutumin da baya da lafiya, ba ma maganar yunwa yake yi ba, ba maganar ilimi yake yi ba, ba maganar dakin da zai yi yake yi ba ko rashin dakin kwana ko titinua, a’a shi lafiyar nan ita ce komai a gareshi, saboda haka dole a fuskanci hidimar kiwon lafiya don shine komai, maras lafiya in ka kawo masa abinci ba zai iya ci ba, duk wanda bai da lafiya ko kawo masa riga mai kyau ba bukanta ta ya keyi ba, komai girman ofis ka ba shi ba zai iya sarrafa aikin ba, don haka kiwon lafiya abu ne mai muhimmanci kwarai da gaske, don haka za mu sanya ido sosai kan sha’anin lafiya a jihar nan.
Bayan nan kuma za mu duba bangaren habbaka tattalin arzikin Jihar Bauchi, domin a wannan fannin an yi wasa da bangaren tattalin arziki, Jihar Bauchi tana da arziki na mutune masu nagarta wanda in aka yi amfani da basira na zamani wannan yawan namu zai iya samar mana da arziki sosai nan gaba, za mu yi amfani da yawanmu don mu cimma nasarori a Jihar nan. Kuma musamman a Jihar Bauchi muna da arziki da Allah ya mana na kasa mai albarka, na koguna masu albarka, Allah ya mana arzikin abubuwan da ya boye a karkashin kasa na ma’adanai da sauransu, wadanda har yanzu ko kashi daya daga cikin dari nasu ba mu fara amfana da su ba. Bugu da kari, ya kamata a ce duk da irin arzikin da Allah ya yi mana na koramu da tafkoki don noman rani a ce muna zuwa makwaftarmu muna sayo Tumatur ko albasa? Har ma kai a ce mu ‘yan Jihar Bauchi muna zuwa wasu jahohi sayen kwai? Ka ga ai rashi ingantaccen shugabanci shi ya jawo wannan. Ba na ce dole a zo a kafa manyan kamfanonin da za su rika gina motoci ko jiragen sama ba ne. Amma akwai irin wadannan kananan matakai na tattalin arziki da kamata a ce mun rungume su, rashi yin hakan shine ya sa muke fuskantar babban barazana a kowace bangaren rayuwarmu, don haka idan Allah ya bamu nasara za mu sanya ido wajen farfado don ingantan sana’ar noma bil-hakki da gaskiya a Jihar Bauchi, kuma za mu yi amfani da irin dumbin arzikin da Allah ya yi mana ne a wannan Jihar wajen ganin mun kyautata wannan bangaren.
Sannan, a Jihar Bauchi tana fama da matsalar rashin tarbiyyar, musamman a cikin matasan da suka fandare suke shaye-shaye, wadanda basu tausaya wa iyayensu, suna ta’addanci da rashin kunya. Za mu sanya ido kwarai da gaske wajen ganin mun ladabta su, da rarrashi da komai, mu ga cewa mun tattaro hankulansu mu fadakar da su kan illolin ababen da suke bi domin ganin an samar musu da kyakkawar tarbiyya.

A wace jam’iyya ce kake wannan gwagwarmayar kawo yanzu?
Muna kan wannan gwagwarmayar ne a karkakashin jam’iyyar ‘Green Party of Nigeria’, ita wannan jam’iyyar ita ce ta yi kama da tsari na zamani, ita GPN ita ce ta sha banban da dukkanin jam’iyyun da muke da su a Nijeriya kasantuwarta jam’iyya ce mai tushe a kasashen waje da suka shahara a fannin siyasa. Green Party akwai ta a Jamani, Ustaroliya, Kanada, da sauran manya-manyan kasashe, daga cikin kasashen ma Green Party din nan sun kai kusa shekaru 100 suna gwagwarmayan daidaita ala’amura. Jama’iyar tana da manufofin da suke bani sha’awa gaya.
Ita wannan jam’iyyar tana daga cikin manufarta na samar wa matasa aiyukan yi, manufar jam’iyyar na son ganin an rage aiyukan ta’addanci, an habbaka sashen ilimi, an bunkasa masana’antu, manufofin ta na ganin an bar barnata dajunnan mu, wato bishiyoyi da gonakai da sauransu ana amfani da su sola wato hasken rana, manufar Green Party na samar da ci gaba mai ma’ana a ga jama’a, wadannan manufofin sun bani sha’awa kuma na ga sun dace da muradina. Alhamdullahi, ba ni kadai ne na shiga cikin jam’iyyar ba. Dalili kuwa shine saboda farkon damar da na samu a siyasa na same ta ne karkashin tsohon gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda da jama’arsa. Dalilin haka ya sa har gobe muna tare da jama’an da suke amana da shi a wannan jam’iyyar, da wadannan jama’an muka gana muka yi ta shawarwari sai gaba dayanmu muka amince muka shiga cikin jam’iyyar GPN. Don haka zan iya cewa hankalina ya kwanta domin ina tafe tare da mutanen da nake da aminci da su.

Farfesa ba ku gamsu da salon mulkin APC ba ne kuke son amsar mulki daga hanunta?
Babu shakka gwamnatin jam’iyyar APC a Jihar Bauchi ta baiwa kowa kunya, gwamnati ce da ta zo da sunan kawo sauyin da zai kawo ci gaba wa al’umma kan al’amuran yau da kullum. A yau, jam’iyyar APC ta zarce shekaru uku a bisa ragamar mulki ta doshi na hudu, babu abun da APC ta tabuka wa jama’an jihar Bauchi, illa dai kamar motace take tafiya i’zuwa wani gari mai nisa sai aka sanya mata ribas, to irin halin da muka samu kanmu kenan a Jihar Bauchi. Duk wani abun da muka fi karfinsa shekaru 4 zuwa 10 a Jihar Bauchi yanzu ya fi karfinmu, ba ma sai na tsaya ina cewa da kaza da kaza ba, kowani dan Jihar Bauchi yana matukar kuka da Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi ba wani abune a boye ba. Don haka duk wani dan halal ya san ya kamata a shiga a yi jahadi, a yi yaki domin ganin cewa an ceto ita Jihar Bauchi daga irin wannan lalacin da shugabanci mara kan gado da muka samu kanmu a ciki.

Yaya kake kallon nasarar Green Party ganin cewar sabuwar jam’iyya ce a Nijeriya?
Gaskiya ina da yakinin za mu sami babban nasara, jam’iyyar GPN jam’iyya ce ta matasa da mata, kuma har ma dattijai a Jihar mu suna ta rubibin shiganta a halin yanzu, ba don komai ba sai rashin samun mafaka, don kuwa an gan sakun hannun da PDP da ta yaudari jama’a, ita kuma APC ta zo ta fi PDP ma kasawa don haka jama’a sun gama yanke hukunci cewa yanzu GPN kadai suke marmaari, don haka ina mai tabbatar muku GPN za ta shimfida gwamnati domin ceto jama’a.

Ya za ka kwatanta gwamnatin PDP da ka yi aiki a ciki da ta APC mai mulki a halin yanzu a jihar Bauchi?
Kuna kalubalantana da in banbance haske da duhu ne? Bari in baku misali, zan baku misali ne kadan a bangaren daya kawai, wato bangaren da na yi aiki a gwamnatin da ta shude, a lokacin da na rike matsayin kwamishinan kiwon lafiya. A karkashin ma’aikata ta kawai gwamnati ta samar babban asibiti wato ‘teaching hospital’, da babban asibitin kwarraru wato ‘specialist hospital’ mai gadajen kwantar da majinyata sama da 400, mun gina manyan asibitoci wato ‘general hospitals’ guda 13 a garuruwan Katagum, Misau, Ningi, Toro da sauransu, a karkashina mun gina kananan asibitin jinya fiye da 200, a karkashina gwamnati ta dauki nauyin karatun dalibai a kasar Egypt wadanda yanzu duk sun zama Daktoci, 25 mata ne da kuma kusan maza 50, a karkashina mun dauki nauyin sama da dalibai dubu daya da suka karanci fannonin harhadar kiwon lafiya dan-daban, a karkashin ofishina mun gina kwalejin jinya da ingomazoma na biyu a cikin tarihin Jihar Bauchi, mun gina asibiti na musamman don mata da yara wato ‘women and children hospital’, a karkashin ofishina mun samar da sababbin kwasa-kwasai biyar a kwalejin jinya da ke Ningi a cikin shekaru hudu da na yi a matsayin kwamshinan lafiya. Abubuwa da dama mun cimma a karkashin gwamnatinmu a lokacin da na ke kwamishina, ta yaya kuke son na kwatanta gwamnatin da bata iya ko gina asibiti guda daya da waccan? Kai sai da muka shekara takwas muna bada tallafi wa duk mace da ta shi ga nakuda wato ‘free delibery kits’, da dai sauransu. A karkashina kawai kun ji kadan daga cikin ababen da muka gudanar, don haka babu ma hadi, gaskiya kenan.

Kawo yanzu me za ka shaida wa jama’an Jihar Bauchi ganin cewar zaben 2019 ya karato?
Kiran da zan yi ga jama’an Jihar Bauchi shine kowa dai ya yi hukunci wa kansa. A shekara ta 2015 aka yi sak, a dalilin sak aka dauko mana tarkace aka shigo mana da su madafan mulki. A cikin lokaci kalilan kowa ya gano cewa sun shigo ne a karkashin inuwar wani mutumin kirki, amma da suka zo sai suka fidda ainihin halayen su, a karamin lokaci suka baza kayansu sai suka kama yi mana abun kunya. dan aikin da suke ta ikirarin wai suna mana ya kasa kasau, barnar ya wuce dukkanin inda ake tsammani, duk sun bi mu da baki suna ta cewa ba a yi kaza ba, ba a yi kaza ba, su kuma kasa tsinana mana komai, shekaru uku kenan har da wattani amma sai labarai ka ke ji! Babu ci gaban da wannan gwamnati ta APC ta kawo a Jihar Bauchi, babu sabon makarantan firamare guda daya tak da ita gwamnatin Bauchi ta gina nata na kanata, babu sakandari daya tak da ta gina sai dai kwaskwarima, babu sabon asibiti guda daya da ta gina a duk fadin Jihar Bauchi, babu wani gada na kirki ko madasan ruwa da za a nuna a ce an gina a cikin shekaru uku, kai babu wani hanya sabo da aka kamala aikin sa wanda ita gwannati mai ci ita ta yi sufurin sa ta tsaga a cikin daji ko birni da za a ce sabo ne aka yi mana a Jihar Bauchi. Tambayar shi ne, shin yaushe ne gwamnati za ta fara aiki ne kam? Don haka ‘yan Jihar Bauchi su shirya katin zabensu kawai mu hadu mu magance wannan barna.

Gwamnati ta yi korafin cewar a farkon hawanta ta samu lalitarta babu komai, ba ka ganin ya dace ku dan kara daga mata kafa?
Gwamnatoci daman a yadda aka tsara mulkin kasar Nijeriya kowace sabuwar gwamnati sai ta yi wannan barazanar, barazana ce kawai don samun amincewar jama’a shi ya sa suka yi ta shelar cewa wai sun zo ba su sami ko sisi ba. Babu abun da aka wawushe daga cikin abun da na sani, inda akwai abun da aka wuwushe kuwa, kamar yadda na ke gani da izuwa yanzu ya tabbata a zahiri kuma da an hukunta masu laifin. Ya dai kamata talakawa su yi wa kawunansu hukunci, yanzu su waye a ke tuhumar su da almundahana da dukiyar jama’a? Tambayar da za a yi yanzu, shin a yanzu ne ake a wawushe wan ko ba haka? Talaka ne ya dace ya baiwa kansa amsa. Amma tabbas an yi ta wannan shelar, kuma a lokacin da suke ta wannan zancen mun zura ido ne mun don mun san cewa wata rana gaskiyar za ta yi halinta.

Me ne ne fatanka?
Fatana ita ce Allah ya bamu nasara mu samu damar kawo sauyi a fadin Jihar Bauchi, sannan ina son na shaida wa jama’an Bauchi kan cewar su sani cewa zaben da za mu yi na 2019 muhimmancinsa ya wuce dukkanin wani zabe da muka taba yi a jihar Bauchi, saboda zabe ne da muke fatan cikin yardar Allah zai zama kamar juyi ne na zamani, zai kasance juyi ne na zamani daga tsarin na rashin sanin ya kamata da rashin sanin inda aka dosa, mun fatan za a samu dama a zubo sabbin zababbu masu tsoron Allah, masu kaifin basira, masu gogewa ba wai bara gurbi ba, wadanda za su zo su fuskanci aikin gyaran Jihar Bauchi. Wadannan masu ceto Jihar Bauchi, wadanda muna fatan Allah Ya sa muna daga cikinsu, ba za su samu damar kawo muradin da suke da su ba, sai kowani dan Jihar Bauchi ya ta tashi domin ganin an kawo wannan sauyin, hakan zai iyu ne kawai idon kowa ya amince da korar da wannan gwamnati da ta kasa kasau, don jam’iyyar Green Party ita ce za ta zo ta shimfida mulkin adalci a Jihar domin ganin jama’an sun ci ribar demokradiyya.

Farfesa Muna godiya?
Ni ma na gode.

Exit mobile version