Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Ina Dalilin Da Ya Sa Cutar COVID-19 Ke Yaduwa Cikin Sauri A Amurka?

Published

on

Tun da aka samu mutumin farko da ya kamu da cutar mashako ta COVID-19 a kasar Amurka a ranar 21 ga watan Janairu, kawo yanzu, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar ya zarce miliyan 1, har ma yawan mamatan kasar ya zarce dubu 50. Ke nan saurin yaduwar cutar a Amurka ya fi duk wata kasa ta daban a duniya. Ina dalilin da ya sa haka?
Dalilin farko shi ne, tun farkon bullar cutar, shugaban Amurka ya yi biris da gargadin da aka yiwa gwamnatinsa. Rahotannin kafofin watsa labaran Amurka sun ce, a ranar 18 ga watan Janairu, wato rana ta uku bayan da aka bada rahoton mutumin farko wanda ya kamu da cutar a kasar, ministan lafiya da samar da hidimomin al’umma na Amurka, ya yiwa fadar White House bayani kan yiwuwar yaduwar cutar, amma Donald Trump ya yi biris da shi.
Duk da cewa White House ta kafa rukuni na musamman domin tinkarar annobar COVID-19 daga baya, amma abun da ta fi maida hankali shi ne, dawowa da mutanen Amurka gida daga kasashen waje, wato ba ta maida hankali sosai ba kan batun gwajin kwayar cutar.
Dalili na biyu shi ne, gwamnatin Amurka ba ta shirya sosai ba wajen tinkarar yaduwar cutar. Zuwa ranar 19 ga watan Maris, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ya zarce dubu 10 a Amurka, amma jihohi daban-daban a kasar ba su yi hadin-gwiwa ba, har ma ta kai suna fuskantar babban matsin lamba a fannin samar da jinya.
Dalili na uku kuwa shi ne, maimakon daukar managartan matakan dakile yaduwar cutar a kasar, gwamnatin Amurka tana yunkurin dorawa sauran kasashe laifi. Saurin yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 ta riga ta shaida irin gazawar gwamnatin Trump a fannin aiki. Rahotanni daga kafar yada labarai ta CNN sun ce, tun daga watan Janairun bana, Trump ya yabawa kasar Sin akalla sau 37, har ma ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa, kasar Sin ta dade tana himmatuwa wajen shawo kan annobar COVID-19, abun da ya cancanci yabo. Amma yanzu cutar na dada kamari a Amurka, har ma Trump ya zargi kasar Sin da boye ainihin yanayin annobar, kuma yana neman kasar Sin ta bada diyya.
Ina ake kwana game da annobar COVID-19 a Amurka? Sai dai mu zuba ido mu ga matakan da gwamnatin Trump za ta dauka a nan gaba.

(Mai Fassara: Murtala Zhang)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: