Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mesut Ozil, ya ce yana fatan kungiyar ta Arsenal ta kammala kakar wasan bana da lashe kofi sannan ya ce har yanzu kungiyar Arsenal tana cikin zuciyarsa kuma ba zai taba cire tarihin daya kafa a kungiyar ba har karshen rayuwarsa.
Suma dai magoya bayan kungiyar ba zasu taba mantawa da irin kokarin da dan wasa Ozil ya yiwa kungiyar ba tun bayan komawarsa Arsenal a lokacin Arsene Wenger daga Real Madrid akan kudi fam miliyan 42 a shekarar 2013.
A watan Janairun daya gabata ne dai kungiyar Fenerbahce ta kaddamar da Ozil a gaban ‘yan jarida bayan an dauki lokuta ana tattaunawa tsakanin kungiyoyin guda biyu kafin a amince da kulla yarjejeniyar komawar Ozil kasar Turkiyya da buga wasa, kasar da yadade yana fatan komawa domin buga wasa.
”Arsenal tana cikin zuciya ta kuma ba zan taba mantawa da irin abubuwan farin cikin da suka faru ba a lokacin da nake kungiyar hakan yasa nayi musu fatan alheri a wasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United a kwanakin baya kuma har yanzu ina bibiyar wasannin kungiyar tare da yi musu fatan alheri” in ji Ozil
Ozil ya koma Arsenal daga Real Madrid a kan kudi fam miliyan 42 a shekarar 2013 inda ya taimaka mata wajen lashe kofunan FA sau uku sannan ya zura kwallaye da dama bugu da kari a zaman da yayi a Arsenal ya taimaka wajen zura kwallaye da dama.
Ozil ya bayyana shaukinsa na tafiya Fenerbahce a wani shirin tambaya da amsa da ya gudanar a shafukan sada zumunta a kwanakin baya inda ya shaida wa mabiyansa cewa Fenerbahce kamar yadda Real Madrid da ke Spain take ita ce kungiya mafi girma a kasar kuma zai taimaka wajen ganin kungiyar ta samu nasarori.
An haifi Ozil a kasar Jamus amma iyayensa ‘yan asalin kasar Turkiyya ne, kuma a baya shugaban Fenerbahce Ali Koc ya ce babban burinsu shi ne su dauki Ozil sannan a shekarar 2019 kungiyar ta Turkiyya wadda sau 19 tana lashe kofin Super Lig ta ce ba za ta dauki Ozil ba saboda ba ta da kudi.
Ozil ya buga wasa a wasanni 10 tun bayan da aka nada Arteta a matsayin kociyan Arsenal a watan Disamba na shekarar 2019, sai dai bai sake buga wasa ba tun da aka koma wasanni bayan dokar kullen farko sanadin barkewar annobar korona a watan Yuni.
Ozil dai ya sha suka daga bangarori da dama na kungiyar Arsenal kuma kungiyoyi da dama a kasar Ingila da Amurka da China da kuma hadaddiyar daular larabawa sun nemeshi amma a haka ya amince da komawa kasar Turkiyya da buga wasa.