Ina Fatan Neman Da Chelsea Take Yimin Ba Gaskiya Bane

Haaland

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund, Erling Braut Haaland, ya magantu akan rade radin da ake yadawa cewa zai bar kungiyar tasa domin komawa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kasar Ingila

Sai dai daman Dortmund tun farko ta bayyana cewa ba za ta sayar da dan wasan nata  ba a bana, duk da cewa manyan kungiyoyi a duniya suna ci gaba da bibiyar matashin dan wasan dan kasar Norway.

Tuni mai koyar da ‘yan wasan Chelsea, Thomas Tuchel ya bayyana cewa yana son salon buga wasa dan wasa Haaland, wanda ya ci kwallo 20 a wasanni 16 a Champions League a Red Bull Salzburg da kuma Borussia Dortmund sannan shima shima kocin Manchester City, Pep Guardiola na bibiyar dan wasan.

Guardiola dan kasar Sifaniya, na neman mai cin kwallayen, bayan da Sergio Aguero ya koma Barcelona, wanda yarjejeniyarsa ta kare a kungiyar a bana sannan ana kuma alakanta Manchester City da cewar tana son yin zawarcin dan wasan Ingila, Harry Kane, wanda ake cewar zai bar Tottenham a bana.

Amma kungiyar Manchester City ta nisanta kanta da cewar za ta dauki dan kwallon Barcelona, Antoine Griezmann da na Bayern Munich, Robert Lewandowski wadanda duka aka danganta kungiyar da dauka.

“Nayi mamakin yawan kudin da akace wata kungiya ta zuba domin dauka ta tabbas kudin suna da yawa ace an sayi mutum daya da wannan kudin saboda haka ina fatan maganar ba gaskiya bane” in ji Haaland

Daman dai Dortmund ta ce ba za ta sayar da Haaland ba, kuma zai ci gaba da yi mata wasanni a kakar da za a fara cikin watan Agusta kuma kungiyar ta Jamus ta sayar da Jadon Sancho, mai shekara 21 ga Manchester United kan fam miliyan 73 a bana.

Dortmund ta ce Sancho kadai ta amince ta sayar a bana, amma sauran ‘yan wasanta za su ci gaba da buga mata wasa har zuwa kakar wasa mai zuwa kafin tayi tunanin sayar dasu ga kungiyar da take bukata.

 

Exit mobile version